Majalisar Dattawa Ta Amince da Karbo Rancen Naira Tiriliyan 1.15 Domin Cike Gibin Kasafin Kudi
Published: 12th, November 2025 GMT
Daga Bashir Meyere
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na neman rancen Naira Tiriliyan 1.15 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2025.
Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da lamuran bashi na cikin gida da na waje.
Yayin da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, wanda mataimakinsa Sanata Haruna Manu ya wakilta, ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 59.99 da Majalisar ta amince da shi, ya karu da Naira tiriliyan 5.25 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 54.74 da gwamnatin tarayya ta fara gabatarwa.
Ya ce an riga an amince da Naira tiriliyan 12.95 a cikin kasafin, wanda hakan ya bar gibin Naira tiriliyan 1.147, abin da ya haifar da bukatar wannan shirin neman rance.
Kwamitin ya bai wa Majalisar shawarar amincewa da rancen cikin gida na Naira tiriliyan 1.15 domin cike gibin da ya samo asali daga karin kudin kasafin.
Kwamitin ya kuma bukaci Ministar Kudi da Ofishin Kula da Lamuran Bashi su tabbatar da cewa an aiwatar da rancen cikin tsari, tare da bin ka’idojin gaskiya, da sharuɗɗan da suka dace.
Majalisar Dattawa ta kuma umurci kwamitinta mai kula da bashin cikin gida da na waje da ya rika sa ido kan yadda za a aiwatar da amfani da kudin da aka ciwo bashi.
Haka kuma, Ministar Kudi za ta rika mika rahoton kowane watanni uku kan halin da ake ciki, da amfani da kudaden, da yadda ake biyan basussuka, yayin da za a kai duk wani rahoton sabawa tsarin ga Majalisar Dattawa domin daukar matakin doka da ya dace.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Majalisar Dattawa Rance Majalisar Dattawa Naira tiriliyan 1
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Ka’idoji Ga Samar da Injinan Noma a Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa ka’idoji da jagorori da za su tsara samarwa da amfani da injinan noma a fadin Najeriya.
Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 45 na Ƙungiyar Injiniyoyin Noma ta Najeriya (NIAE), mai taken “Kafa Ka’idoji da Ƙarfafa Fasahohin da Aka Gwada Don Samar da Abinci da Ƙara Darajar Kayayyaki a Najeriya”, da aka gudanar a Ilorin.
Ya ba da shawarar kafuwar cibiyoyin injinan noma a kowanne yanki na ƙasa, domin horo, gyara, da tsara fasahohin aikin gona.
A cewarsa, bayan samun injina, mafi muhimmanci shi ne kafa tsarin daidaitawa, haɗa na’urori a gida, da tsarin kulawa, domin tabbatar da cewa kowanne injin da aka tura yana dacewa da aikin da aka tsara, tare da samun ƙwararrun masu gyara.
Ministan ya bayyana cewa, manoma na Najeriya suna bukatar fasahohi na gida, waɗanda aka haɓaka bisa fahimtar ƙasa, irin amfanin gona, da kuma girman noman da ake yi.
END/ALI MUHAMMAD RABIU