Aminiya:
2025-11-12@20:23:34 GMT

Troost-Ekong ya gargaɗi Super Eagles kan wasan da za ta fafata da Gabon

Published: 12th, November 2025 GMT

Kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Najeriya, William Troost-Ekong, ya gargaɗi ’yan wasan ƙasar da su guji tafka kura-kurai a wasan da za su buga da Gabon a ranar Alhamis.

Ekong ya yi wannan gargaɗi ne kafin fara atisayen ’yan wasan a safiyar Talata, a yayin da suke ci gaba da shirin fafatawar neman gurbin shiga Kofin Duniya na 2026.

Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro ’Yan sanda sun kama mutum 14 kan zargin ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Jigawa

Super Eagles za ta kece raini da Panthers of Gabon a wasan da ake sa ran zai kasance mai matuƙar muhimmanci wanda shi zai tabbatar da matsayin Najeriya na samun tikitin babbar gasar tamaula.

A nasa bangaren, mai horar da tawagar Najeriya, Eric Chelle, ya yaba da kishin da ’yan wasan ke nunawa wajen ganin sun kai ƙasar zuwa gasar Kofin Duniya.

A bayan nan ne aka ruwaito cewa, tawargar ta Super Eagles ta ƙaurace wa atisaye a ranar Talata a birnin Rabat a ƙasar Morocco, kwana biyu kafin wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 da za su yi da Gabon.

’Yan wasa da jami’ai sun yi zanga-zangar rashin biyan haƙƙoƙinsu, ciki har da kudin alawus da ladan buga wasanni da suke bi tun daga shekarar 2019.

Ƙungiyar, wadda ke da manyan ’yan wasa kamar Victor Osimhen, Alex Iwobi, da Ademola Lookman, na neman hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (NFF) ta warware wannan matsalar biyan kuɗin cikin gaggawa.

Wannan lamarin ya jefa shakku kan shirin Super Eagles, yayin da aka tsara za ta fuskanci Gabon ranar Alhamis a filin wasa na Moulay Hassan Stadium da ke Rabat.

Har yanzu NFF ba ta fitar da cikakken bayani ga jama’a ba, amma majiyoyi sun tabbatar cewa ana gudanar da tattaunawa cikin gaggawa don kawo mafita.

Rahotanni sun ce bashin da suke bi ya haɗa da ƙudin alawus na wasannin neman shiga AFCON 2025 da kuma karawar neman shiga Kofin Duniya 2026.

Najeriya ta gaza samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022 da aka yi a Qatar, kuma yanzu tana shan matsin lamba daga masu bibiyar tamaula a ƙasar, domin ta dawo da martabarta a duniya.

Sakamakon wasan da za ta kara da Gabon zai iya tantance makomar Super Eagles a neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico a 2026.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Najeriya Kofin Duniya

এছাড়াও পড়ুন:

UNICEF ta ce Isra’ila ta hana allurar rigakafin yara masu mahimmanci shiga Gaza

UNICEF ta yi gargadin cewa  Isra’ila na hana shigar da muhimman kayan aikin da ake buƙata don  allurar rigakafi a Gaza, wanda hakan ke kawo cikas ga ƙoƙarin isa ga yara a yankin da yaƙi ya daidaita.

Hukumar ta ce kayayyakin, ciki har da sirinji da ake amfani da su don allurar rigakafi na yau da kullun da kwalaben madarar jarirai, har yanzu suna nan a wuraren bincike, duk da ci gaba da tsagaita wuta da kuma ƙaruwar buƙatun jin kai.

UNICEF ta bayyana cewa a halin yanzu tana gudanar da Shirin allurar rigakafi ga yara ‘yan ƙasa da shekara uku, waɗanda da yawa daga cikinsu sun rasa allurar rigakafi na yau da kullun a cikin shekaru biyu da suka gabata na rikici.

Duk da haka, tana fuskantar matsala mai tsanani wajen samun damar yin amfani da sirinji miliyan 1.6 da firiji masu amfani da hasken rana da ake buƙata don adana allurar rigakafi da sauran kayyayaki na kiwon lafiya, inda har yanzu Isra’ila ta hana shiga da sub isa hujjar gudanar da bincike tun daga watan Agusta.

An fara zagayen farko na shirin allurar riga-kafi na UNICEF a ranar Lahadi, da nufin isa ga yara sama da 40,000 wadanda suka rasa kariya daga cututtuka kamar su shan inna, kyanda, da kuma ciwon huhu. A ranar farko da aka fara wannan shirin, an yi wa  kimanin yara 2,400 da allurar riga-kafi yayin da dama kuma suke cikin layin jira.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministocin harkokin wajen kasashen yamma sun yi Allah wadai da ta’asar RSF a El Fasher Darfur November 11, 2025 Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya November 11, 2025 Larijani : ‘babu wani sabon sako’ da muka aika wa Amurka November 11, 2025 Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita November 11, 2025 Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar November 11, 2025 Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar November 11, 2025 Hamas ta soki kudurin Isra’ila na yin dokar hukuncin kisa kan laifin ta’addanci November 11, 2025 Iran Za Ta Harba Taurarin Dan Adam Guda Uku Zuwa Sararin Samaniya November 11, 2025 Lebanon: An Saki Hannibal Kaddafi Bayan Zaman Kaso Na Shekaru 10 November 11, 2025 An Sake Bude Gidajen Mai Da Makarantu Da Aka Rufe A Kasar Mali November 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo
  • Gabon: An Daure Mata Da ‘Dan  Tsohon Shugaban Kasa Bongo Shekaru 20 A Gidan Yari
  • UNICEF ta ce Isra’ila ta hana allurar rigakafin yara masu mahimmanci shiga Gaza
  • Kofin Duniya 2026 Zai Zama Na Ƙarshe A Wuri Na – Ronaldo 
  • Trump Ya Yi Barazanar Maka BBC A Kotu Tare Da Neman Diyyar $1bn
  • Matan sojojin da suka mutu na neman agaji
  • EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jallo
  • An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
  • Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL