Aminiya:
2025-11-10@10:30:17 GMT

’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano

Published: 10th, November 2025 GMT

’Yan bindiga sun kai hari a Jihar Kano a daren Lahadi, inda suka yi garkuwa mata biyar ciki har da masu shayarwa.

Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen ’Yan Kwada da ke cikin yankin Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono da ke Shiyyar Kano ta Arewa.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa dandazon maharan sun yi dirar mikiya a garin ne ɗauke da muggan makamai, inda suka yi ta harbe-harbe tare da shiga gidaje suna yin awon gaba da mutane.

“Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi a iska suna karya ƙofofi. Sun tafi da mata biyar, ciki har da masu shayarwa,” in ji majiyar.

Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shi Mahaifiyar Minista Balarabe Lawal Abas ta rasu

Sai dai ya ce daga cikin matan da aka sace, biyu sun tsere sun dawo, yayin da ragowar ukun ke hannun ’yan bindigar.

Harin na daren Lahadi na zuwa ne bayan mako guda da sojoji suka hallaka ’yan bindigar kimanin 19 a yankin.

Mutanen Faruruwa da sauran kauyuka da ke kan iyakar Kano da Katsina na ci gaba da rayuwa cikin fargaba sakamakon hare-haren ’yan bindiga da ke faruwa lokaci zuwa lokaci.

A sakamakon tsananin rashin tsaro, an ruwaito cewa yawancin ƙauyuka sun zama kufai, inda mazauna suka tswre zuwa garin Faruruwa ko kuma zuwa birane don tsira da rayukansu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Faruruwa Garkuwa shayarwa

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano

Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale.

Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa

Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar.

“A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar da yaro ɗan shekara biyu, Danjuma Salman, wanda ya faɗa cikin wata rijiya da murfinta ya lalace,” in ji sanarwar.

Abdullahi, ya ce jami’an hukumar sun fito da yaron, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

An miƙa gawar yaron ga mahaifinsa, Salman Dayyabu, bayan an fito da shi daga rijiyar.

Daraktan Hukumar Kashe Gobara na jihar, Alhaji Sani Anas, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyayen yaron.

Ya kuma yi kira ga mazauna unguwanni da su riƙa rufe rijiyoyi da sauran wuraren ruwa yadda ya kamata domin guje wa irin wannan iftila’i.

Haka kuma ya shawarci iyaye da su riƙa kula da yaransu sosai, musamman a wuraren da ke da hatsari.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno
  • Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL
  • ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra
  • Minista Goronyo ya Duba Ci Gaban Aikin Titin Abuja Zuwa Kano
  • Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato
  • Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko
  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai