A shekaru fiye da 20 da suka gabata, birnin Wenzhou dake lardin Zhejiang na kasar Sin ya yi suna domin samar da takalma, kuma kayayyakin da ya samar sun samu karbuwa a duniya domin suna da araha. Amma ma’aikatan kamfanonin samar da takalma sun yi aiki har na tsawon awoyi 14 a kowace rana, inda yawan takalman da aka samar a shekara daya ya kai miliyan 100, amma ribar kowane takalma biyu ba ta wuce Yuan biyu kacal ba, kana ba su da inganci, har ma mutanen Turai suna wa takalman shagube da sunan takalman yini daya.

Batun ya sa kaimi ga Xi Jinping wanda ya yi aiki a gwamnatin lardin Zhejiang da ya tsai da kudurin canja burin kamfanonin daga samar da kaya cikin sauri zuwa kyautata ingancin kayan.

A halin yanzu, kamfanonin samar da takalma na birnin Wenzhou suna amfani da fasahohin zamani na 3D wajen samar da takalman musamman, ribar takalma biyu ta karu zuwa Yuan 200, wannan ya shaida cewa, inganci ya fi daraja a kan yawa. Wannan ne misali na raya tattalin arzikin Sin mai inganci. Kasar Sin ta gudanar da matakai uku wajen samun ci gaba mai inganci da canja zaman rayuwar jama’a. Na farko shi ne yin kirkire-kikrire, na biyu shi ne canja tsarin samar da kaya don kiyaye muhalli, na uku shi ne bude kofa ga kasashen waje da more fasahohi a tsakanin juna. (Zainab Zhang)

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Matakin Amurka Na Dakatar Da Ka’idar Fadada Jerin Wadanda Kasar Ta Takaita Fitar Wa Kayayyaki November 12, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing November 12, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu November 12, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: samar da takalma

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Shirya Faɗaɗa Gonakin Shinkafar Jangwa Don Ƙara Samar da Shinkafa

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na faɗaɗa gonakin shinkafar Jangwa daga hektar 3,300 zuwa hektar 5,000 a kakar noma mai zuwa, domin haɓaka samar da shinkafa da kuma ƙarfafa tattalin arziki a jihar.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin ziyarar duba girbin shinkafa a garin Jangwa, ƙaramar hukumar Awe.

Gwamnan ya ce faɗaɗa gonakin zai ƙara hektar 3,000 daga yawan da ake da shi yanzu, domin inganta ci gaban tattalin arziki ta hanyar aikin gona. Ya kuma nuna yadda jihar ta samu ci gaba a fannin noma, inda gonar ta faɗaɗa daga hektar 2,000 a bara zuwa hektar 3,300 a wannan shekarar.

Gwamna Sule ya sanar da haɗin gwiwar gwamnatin jihar da kamfanin Silvex International, babban kamfani mai sarrafa shinkafa, domin ƙara samar da shinkafa a jihar.

A cewar Gwamna Sule, haɗin gwiwar zai baiwa Silvex International damar sayen shinkafar kai tsaye daga gonakin jihar sannan a tattara ta a ƙarƙashin tambarin Nasarawa Agro-Commodity Company (NASACCO).

Shinkafar, wacce za a kaita Kasuwa da suna “NASACCO Gold”, ana sa ran zai ƙara shahara da darajar kayan shinkafar jihar a kasuwa.

Gwamnan ya yi godiya ga Silvex International bisa wannan haɗin gwiwa, wanda ya ce yana daga cikin matakan gwamnatinsa na jawo jarin masu zaman kansu zuwa fannin aikin gona a jihar.

Haka kuma, Gwamna Sule ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen ƙara samar da shinkafa a jihar, tare da shirin faɗaɗa gonar zuwa hektar 8,000 nan gaba.

Gwamnan ya yaba wa matasa da al’ummomin garuruwan Jangwa, Ayakeke, da Agwatashi bisa jajircewarsu wajen tabbatar da nasarar gonar.

A nasa jawabi, Babban Jami’in Gudanarwa na Silvex International kuma Shugaban Aikin NASACCO, Abubakar Garba Ibrahim, ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin babban ci gaba ga kamfanin.

Ya bayyana cewa haɗin gwiwar zai amfani jihar ta hanyoyi da dama, ciki har da haraji, ƙara darajar kayayyaki, da raba riba ta ƙarshe.

Aliyu Muraki, Lafia.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Matakin Amurka Na Dakatar Da Ka’idar Fadada Jerin Wadanda Kasar Ta Takaita Fitar Wa Kayayyaki
  • Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Shirya Faɗaɗa Gonakin Shinkafar Jangwa Don Ƙara Samar da Shinkafa
  • Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
  • CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15
  • ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato
  • Jakadun Kasashen Waje: Shirin Raya Kasa Na 15 Na Sin Na Dauke Da Kyakkyawan Sako
  • An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 
  • Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin
  • Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa