Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire
Published: 14th, November 2025 GMT
Kasar Cote De Voire ta sanar da tsaurara harkokin tsaro akan iyakokinta na Arewa domin fuskantar ‘yan hijira da suke kwararowa daga kasar Mali da take fama da rikicin masu dauke da makamai.
Majalisar tsaron kasar “Cote De Voire” ce ta bai wa sojojin kasar umarni da su tabbatar da tsaro a kan iyakoki, kamar yadda gwamanti ta bayyana.
A can cikin kasar Mali mai makwabtaka da “Cote De Voire” ana samun karuwar hare-haren masu dauke da makamai akan fararen hula da hakan yake kara yawan kwararan ‘yan hijira.
Mali wacce ba ta da iyaka ta ruwa tana fama da rikickin masu dauke da makamai dake da alaka da kungiyar alka’ida da su ka tsananta kai hare-hare daga watan Satumbar da ya gabata.Masu dauke da makaman dai sun datse kan iyakar kasar da hana shigar da man fetur da hakan ya haddasa kamfar man fetur. An rufe gidajen mai masu yawa da kuma makarantu saboda babu ababen hawa da za su yi jigilar dalibai.
Kungiyar mai suna: “Nusratul-Islami Wal Muslimin” tana kara nausawa daga yammacin kasar zuwa kudu, da hakan yake jefa tsoron cewa za su kwace madafan iko.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 14, 2025 Unrwa: Fiye Da Gidaje 282,000 “Isra’ila” Ta Rusa A Gaza November 14, 2025 Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya November 14, 2025 Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya November 14, 2025 Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza November 14, 2025 Kwamitin Tsaro ya tsawaita wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya November 14, 2025 Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin November 14, 2025 Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka November 14, 2025 Iran da China na bunkasa alakoki da hadin gwiwa a tsakaninsu November 14, 2025 Abdoulaye Diop: ‘Yan Tawaye Ba Za Su Iya Mamaye Dukkan Kasar Mali Ba November 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Masu Alaka
Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Fara Karbar Harajin Man Fetur
Hukumar kula da harkokin man fetur a Najeriya ta ce ta dakatar da shirin fara karbar harajin kashi 15 cikin 100 kan albarkatun man fetur ɗin da ake shigowa da su kasar daga ƙasashen waje.
Mai magana da yawun hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), George Ene-Ita, ya faɗa cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa ya kamata ‘yan Najeriya su daina fargaba.
A ranar 29 ga watan Oktoba ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da saka harajin kan man fetur da dizel, wanda zai kara farashin man da ake saukewa a defo-defo, kuma daya daga cikin manufarta shi ne karfafa matatun mai na cikin gida.
Gwamnatin Najeriya ta tsara fara aiki da harajin daga ranar 21 ga watan Nuwamban nan, kafin matakin da NMDPRA ta sanar.
Duk da manufar karfafa matatun mai na cikin gida da harajin zai yi, zai kuma iya jawo hauhawar farashin a gidajen mai kasancewar har yanzu Najeriya na shigo da fetur mai yawa daga kasashen waje.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da china Za su Yi Bikcin Cika Shekaru 55 Da Huldar Diplomasiya Tsakaninsu November 13, 2025 Faransa: An Fara Shari’ar Shugaban ‘Yan Tawayen DRC Bisa Laifuna Akan Bil’adama November 13, 2025 Almayadin Ta Sami Rahoton Hukumar Makamashin Ta Duniya ( IEA) Aka Cewa Iran Tana Aiki Da Dukkanin Ka’idoji November 13, 2025 Janar Ali Fadwi: Muna Aiki Tukuru Domin Sabunta Nisan Makamanmu Masu Linzami November 13, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Iran da Rasha sun Tattauna Gabanin Taron Gwamnonin IAEA November 13, 2025 Iraki: An Fara Sanar Da Sakamakon Farko Na Babban Zaben Da Aka Gudanar November 13, 2025 Kenya: An gano tarin zinari a karkashin kasa da darajarsa ta haura Dala biliyan 5 November 13, 2025 Gaza: Hamas Ta Nemi Kawo Karshen Kisan Kiyashi Da Lamunce Shigar Da Taimako November 13, 2025 MDD ta yi gargadi game da hadarin yunwa a wasu sassa na duniya November 13, 2025 Amurka Na Shirye-Shiryen Aikewa Da Sojoji Guda 1000 A Iyakar Isra’ila Da Yankin Gaza November 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci