Aminiya:
2025-11-14@17:00:53 GMT

Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa

Published: 14th, November 2025 GMT

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sake hana jam’iyyar PDP gudanar da babban taronta na ƙasa da ta ke shirin yi.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Peter Odo Lifu, ya yanke hukuncin ne a ranar Juma’a.

Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP

Ya ce taron da aka tsara yi a Ibadan a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba ba za a gudanar ba sai an bai wa tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, damar sayen fom ɗin takarar kujerar shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Alƙalin ya kuma umarci INEC da kada ta sanya baki ko ido a kan taron har sai an bai wa Lamido damar sayen fom.

Lifu, ya ce PDP dole ta bi dokokinta ta kuma bai wa duk ’ya’yan jam’iyyar waɗanda suka cancanta damar yin takara.

Ya ce ba daidai ba ne a hana Lamido sayen fom ɗin takara.

Lamido, ya garzaya kotu ne bayan hana shi sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar.

Alƙalin ya ƙara da cewa PDP ba ta fitar da sanarwar da doka ta tanada ba, kuma ba ta bayar da kwanaki 21 na sanarwa kafin gudanar da taron kamar yadda yake a tsarinta.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: taro

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A duk shekara bayan girbin damina, ana sa ran manoma su ci gaba da noma a lokacin rani domin tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arziki. Sai dai hakan na fuskantar kalubale da dama da ke hana yawancin manoma shiga noman rani.

 

Kamar yadda masana suka sha bayyanawa, akwai dalilai da dama dake hana manoma shiga noman rani a duk lokacin da aka ce damina ta tattara inata intat.

Shin ko wadanne kalubale ne ke hana manoma shiga noman rani bayan damuna ta wuce?

NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin PDP: Fiye Da Wakilai 3,000 Ne Za Su Raba Gardama A Babban Taron Jam’iyyar
  • Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA
  • Ramaphosa Ya Caccaki Trump Kan Kauracewa Taron G20 A Johannesburg
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani
  • Dalilin da ya kamata PDP ta jingine taron da za ta gudanar— Saraki
  • An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe
  • Iraki: Hukumar Zabe Ta Fara Sanar Da Sakamakon Farko Na Babban Zaben Da Aka Gudanar
  • Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna
  • PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu