Aminiya:
2025-11-13@06:36:01 GMT

Majalisa ta amince da buƙatar Tinubu na karɓo rancen N1.15bn

Published: 13th, November 2025 GMT

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓo rancen Naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025.

Amincewar ta biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Manu Haruna, ya gabatar.

Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana Super Falconets ta lashe gasar WAFU ta ’yan ƙasa da shekaru 20

Ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2025 na Naira tiriliyan 59.

99 ya bar giɓin naira tiriliyan 1.15 wanda dole ne a cike ta hanyar nemo rancen a cikin gida.

Sanatoci sun amince cewa rancen ya zama dole domin ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan gwamnati da tabbatar da nasarar kasafin kuɗin 2025, musamman ɓangaren manyan ayyuka.

Sai dai sun jaddada muhimmancin yin gaskiya da bayyana bayani kan yadda za a yi amfani da kuɗin.

Wasu sanatocin sun shawarci Ma’aikatar Kuɗi da Ofishin Kula da Lamuni (DMO), da su riƙa bai wa Majalisar Dattawa rahoto lokaci-lokaci kan yadda ake kashe kuɗin da kuma yadda za a biya bashin.

Sun ce hakan zai taimaka wajen kauce wa almundahana da kuma tabbatar da ɗorewar tsarin lamuni na cikin gida.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yaba wa kwamitin kan yadda suka gudanar da aikinsu a kan lokaci.

Ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa Majalisar Dattawa za ta ci gaba da sanya idanu kan yadda za a yi amfani da rancen domin tabbatar da cewa an yi amfani da shi wajen ci gaban ƙasa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwamiti Majalisar Dattawa rance Majalisar Dattawa

এছাড়াও পড়ুন:

Wani mutum ya rasu a gidan karuwai bayan ziyartar ’yan mata

Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a tabbatar da abin da ya jawo mutuwarsa ba.

Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ta ce an miƙa batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.

Wasu majiyoyi daga cikin gidan karuwan sun bayyana cewa wani ma’aikacin otal ɗin da ke kula da wurin ya yi faɗa da mamacin kafin daga bisani ya yanke jiki ya faɗi ya mutu.

Matar tsohon Shugaban Ƙasa Shagari ta rasu EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jallo

Majiyar ta ƙara da cewa an garzaya da mutumin asibiti domin ba shi agajin gaggawa, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Rahotanni sun ce an kama wani mutum daga cikin gidan matan da ake zargi da hannu a lamarin, kuma rundunar ’yan sanda ta jihar ta ta fara bincike a kai.

SP Grace Iringe-Koko ta kuma tabbatar da cewa an kama mutum ɗaya da ake zargi, kuma sashen ’yan sanda na Azikiwe ya miƙa shari’ar zuwa SCID domin gudanar da bincike mai zurfi.

Sai dai bayan faruwar lamarin, an lura dukkan ’yan mata masu zaman kansu da ke yawo a cikin da wajen gidan karuwan sun yi layar zana.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dattawa Ta Amince da Karbo Rancen Naira Tiriliyan 1.15 Domin Cike Gibin Kasafin Kudi
  • An Bayyana Ranar Karshe Ta Biyan Kudin Aikin Hajji Mai Zuwa
  • Kungiyar Wamban Shinkafi Ta Amince Da Tinubu a 2027
  • Yadda muka daƙile yunƙurin tsige Akpabio daga shugabancin Majalisa – Orji Kalu
  • Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro
  • Babu wani gwamna da zai yi ƙorafin ƙarancin kuɗi a mulkin Tinubu — Sanwo Olu
  • Wani mutum ya rasu a gidan karuwai bayan ziyartar ’yan mata
  • FCT Ta Saka Ranar 1 Disamba Don Kammala Biyan Kudin Hajjin 2026 N7.7m
  • Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC