UNICEF da Abokan Hulɗa Sun Kaddamar da Shirin Wayar da Kai Kan Rijistar Haihuwa a Yankin Gwarzo
Published: 13th, November 2025 GMT
A wani sabon yunƙuri na inganta haƙƙin yara da walwalarsu, Hukumar kula da kananan yara ta MDD wato UNICEF tare da haɗin gwiwar Hukumar Wayarda kan jama’a da ta Ƙasa (NOA) da Hukumar kidayar Jama’a ta kasa (NPC), da Hukumar Kula da katin zama dan Ƙasa (NIMC), sun kaddamar da shirin wayar da kai na yini guda kan muhimmancin rijistar haihuwa ga sabbin jarirai a duk faɗin Yankin Gwarzo na Jihar Kano.
Wannan wani ɓangare ne na shirye-shiryen gwamnati da UNICEF ke tallafawa, domin ƙarfafa tsarin kare yara da kuma tabbatar da samun damar yin amfani da muhimman aikace-aikacen zamantakewa, musamman a yankunan karkara na jihar.
Wakilin NPC, Malam Abubakar Lawal, ya jaddada muhimmancin haddin kan al’umma wajen cimma nasarar cikakkiyar rijistar haihuwa. Ya yi kira ga sarakunan gargajiya, malamai da shugabannin al’umma da su jagoranci wayar da kan jama’a don tabbatar da cewa babu yaro ko ɗaya da bai samu rajista ba.
A nasa jawabin, Mai ba da shawara kan harkokin lafiya (SBC Health Consultant), Alhaji Usman Yahaya, ya bayyana rijistar haihuwa a matsayin matakin farko na shari’a da ke tabbatar da wanzuwar yaro, yana mai cewa wannan ne kofar shiga ga duk wasu haƙƙoƙin yara irin su lafiya, ilimi da kariya.
Ya nuna damuwa cewa har yanzu yara da dama a yankunan karkara ba su da takardar shaidar haihuwa ta hukuma, lamarin da ke iya hana su shiga cikin shirin gwamnati da tsare-tsaren ci gaban jama’a.
Masu halarta sun gudanar da tattaunawa, inda aka yi tambayoyi da tattaunawa da aikin ƙungiya domin samar da dabarun aiki a matakin ƙasa da za su taimaka wajen faɗaɗa rijistar haihuwa a duk faɗin Yankin Gwarzo.
Khadijah Aliyu/Kano
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwarzon Kano rijistar haihuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta
An cimma wannan nasara ne a wani samame da aka kai tsawon makonni biyu a wasu wuraren da ake zargin ana aikata laifuka a yankin mai arzikin mai, in ji sanarwar.
Rundunar Sojin ta yi alƙawarin ƙara ƙaimi kan tarwatsa duk wata haramtacciyar matata a yankin Neja Delta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA