Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump
Published: 10th, November 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta nemi ƴan Nijeriya da su ƙwantar da hankali duk da tutsun diflomasiyya da ya taso tsakanin Nijeriya da Amurka.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a Dutse, Jihar Jigawa, yayin ziyarar gaisuwa ga Gwamna Umar A. Namadi.
Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya“Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da dukkan abin da ya kamata wajen tabbatar da tsaron Nijeriya daga duk wata barazana da zata kawo ruɗani, da kuma gyara duk wani tarnaki a dangantakar mu da abokan hulɗarmu na ƙasa da ƙasa, don haka, ƴan Nijeriya su samu nutsuwa,” in ji Idris.
Ministan ya ziyarci jihar Jigawa ne domin halartar taron matasa na Arewa maso yamma na shekarar 2025 da kuma Gabatar da Nasarorin Shugaba Tinubu bayan shekaru biyu a ofis.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC
Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar.
Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan AnambraOyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar.
“Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko siyasa ba ne. Abin da muke buƙata yanzu shi ne haɗin kai don kare ƙasarmu,” in ji shi.
Ya shawarci ’yan adawa da su yi hattara da kalamansu, tare da kira ga manyan hafsoshin soji da su tabbatar da amincewar da aka ba su ta hanyar yin aiki tuƙuru wajen murƙushe ’yan ta’adda.
Oyintiloye, ya kuma roƙi gwamnatin Amurka da ta taimaka wa Najeriya da bayanan leƙen asiri da kayan yaƙi maimakon turo sojojinta, inda ya ce hakan na iya ƙara dagula lamarin.