Aminiya:
2025-11-09@22:10:51 GMT

Yarin Fika ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a Yobe

Published: 9th, November 2025 GMT

Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar.

Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar.

Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci

Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar.

Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen goyon bayan jam’iyyar APC.

Ya ce, “Ina son ku gane cewa a halin yanzu, PDP da sauran jam’iyyun adawa a Yobe kamar sun ƙare.”

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Yobe, Alhaji Mohammed Gadaka, ya bayyana zuwan Yarin Fika a matsayin babbar nasara ga jam’iyyar.

Ya ce, “Muna maraba da ku a cikin jam’iyyar, kuma za mu ba ku cikakkiyar damar da kowane mamba yake da ita. Za mu yi aiki tare da ku don ci gaban jam’iyyarmu.”

A nasa jawabin, Gwamna Buni ya nuna farin cikinsa da shigowar Yarin Fika da magoya bayansa.

Ya ce za su ci gaba da ƙoƙari wajen ci gaban jam’iyyar APC a Potiskum, da kuma dukkannin faɗin jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamna Buni Sauya Sheƙa Yarin Fika

এছাড়াও পড়ুন:

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji November 9, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15 November 9, 2025 Daga Birnin Sin Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba November 9, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yarin Fika ya sauya sheƙa PDP zuwa APC a Yobe
  • CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032
  • Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar
  • Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar Yayin Daukar Ma’aikata
  • Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
  • Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu
  • Minista Goronyo ya Duba Ci Gaban Aikin Titin Abuja Zuwa Kano
  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa