A yau Lahadi 9 ga wannan wata, an rufe taron koli na Wuzhen na ayyuka masu nasaba da yanar gizo na duniya na shekarar 2025 mai taken “kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa mai bude kofa da hadin gwiwa da tsaro don kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin harkoki masu nasaba da yanar gizo”, inda wakilai fiye da 1600 daga kasashe da yankuna fiye da 130 suka halarci taron da tattauna taswirar kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa.

 

Babban sakataren taron Ren Xianliang ya yi bayani a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, an zartas da rahoton aiki na taron yanar gizo na duniya na shekarar 2025 a gun taron koli a wannan karo, da amincewa da kafa kwamitin kula da kiyaye abubuwan al’adu ta yanar gizo, da kwamitin kula da harkokin ciniki ta yanar gizo, da gudanar da taron tattaunawa kan cika shekaru 10 da gabatar da ra’ayin kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin harkoki masu nasaba da yanar gizo, inda mahalartar taron tattaunawar suka nunar da cewa, an zurfafa ra’ayin a fadin duniya a shekaru 10 da suka gabata, kuma an samu jerin nasarori wajen sarrafa harkokin raya ayyuka masu nasaba da yanar gizo na duniya. (Zainab Zhang)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa November 9, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032 November 9, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji November 9, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: masu nasaba da yanar gizo yanar gizo na duniya

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna tsoron wanda zai yi tunani a gaba, saboda duk wanda ya kawo wani ilimi sai ka ji an ce Zindiki ne, sai a so a halaka shi ma idan ba a yi wasa ba. Toh abin da ya dinga faruwa kenan har Allah Ya kawo falasfawa na Greeks Socrate, wasu sun ce Annabi ne, suka zo suka canza ilimi shi kan shi wannan Socrate din kashe shi aka yi da aka ce ko ya ce bai yarda da wannan ilimi ba, ko ya sha dafi shi kuma ya ce Allah ba zai ba shi ilmi ba, don haka gwara ya sha dafi ya mutu ya yarda ya sha, ga shi su wanda suka kashe shi ba sunansu shi kuwa har yau sunansa a duniyar ilimi ba zai bace ba. Toh Allah kuma Ya kawo juyin juya hali daga karni na 1800 har ya zuwa 1900 ilimin ya soma yalwata da aka fara rubuta shi, wasu na cewa ba mahaukaci sai wanda ya ba da aron littafi, ba wanda ya fi shi hauka sai wanda ya dawo da shi, wannan a lokacin da ake rubuta littafi da hannu kenan amma yanzu ya kare, an ce Shehu ya zo gidan daya daga cikin shehunnanmu yana duba library sai ya ga wani littafi sai ya ce ka ga wannan littafi na neme shi ban samu ba, ba ni aro sai ya ce Shehu na ba ka aro dauki, sai Shehu ya ce masu hikima sun ce babu mahaukaci sai wanda ya ba da aron littafi, ba wanda ya fi hauka sai wanda ya dawo da littafi, ya ce ni dai ba zan zama mahaukaci ba, sai Shehu ya yi masa wasa.

To da aka soma rubutun, China kamar su suka soma, to da buga littafi ilimi ya soma ya]uwa zuwa ga jama’a, ilimi ya fito daga dakin bauta, ya fito daga masarautar sarakuna ya shiga gidan kowa, a da kuwa yana gidan sarakuna ne kawai, ilimi ya soma yaduwa har Allah ya kawo Rediy,o tana daga cikin abin da ya yada ilimi, ta yi hobbasa wajen wayar da kan komai, dan haka a kula da rediyo yana da matukar kyau saboda galibin mutane rediyon nan ita ce hanyar daukar maganarsu, Allah ya saka wa Shehu Ibrahim Inyass (RA) da alkhairi, ya sha wahala wajen sa karatun Kurani a ciki, har Allah ya kawo talabijin, har “cable” din nan ta zo, yanzu fa za ka iya ganin duniya a cikin abu, karshen wayewa, karshen ci gaba a yanzu kuma wayar salula, wadannan wayoyi da suke hannunmu sun sa a yanzu babu jahili sai dai dakiki wanda ya ki sani da gangan, amma wayar nan babbar farfesa ce ta kowane karni, idan fannin jinya ne za ta fada ma har abin da hankalinka ba zai taba kawowa ba, haka a fannin alheri, idan fannin tarihi ne za ta kai ka har inda kudinka ba zai iya kai ka ba. Alhamdu Lillah, mun gode Allah.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Dausayin Musulunci Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya October 17, 2025 Dausayin Musulunci Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2) October 10, 2025 Dausayin Musulunci Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi October 3, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
  •  Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati
  • Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi
  • Dan Wasan Taekwando Na Kasar Iran Abulfazl Zandi Ya Zamo Shi Ne Na Daya A Duniya
  • Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa
  • Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil
  • Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)
  • An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo