Jihar Kwara Ta Jaddada Kudirin Tallafa wa Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafin Jinsi
Published: 13th, November 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar.
Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa Cin Zarafi (SARCs) da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) a Ilorin da kuma Asibitin Kwarari ta Sobi da ke Alagbado.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa cibiyar an kafa ne tare da hadin gwiwar ofishin Uwargidar Gwamna, domin jinya kyauta da kuma kwantar da hankali, da tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafi a jihar.
Afolashade ta ƙara da cewa bincike da tantancewar da ake yi yanzu zai taimaka wajen tantance ingancin kulawar da ake bayarwa, da gano wuraren da ake bukatar gyara domin samar da tsarin taimako mai inganci da niyya kai tsaye ga masu bukata.
Ta kuma jaddada bukatar ƙara haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki tare da horar da ma’aikatan cibiyoyin SARC a fannin tattara bayanai da bayar da rahoto domin inganta tsarin tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafin jinsi.
Ali Muhammad Rabiu/Ilorin
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jinsi Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Ya Yi Kira Ga Jama’a Su Yi Rijista Kuma Su Karɓi Katin Zaɓe
Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano, Yusuf Shuaibu Imam, ya yi kira ga mazauna yankin da su ziyarci ofisoshin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin yin rijistar zaɓe da kuma karɓar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC).
Imam ya yi wannan kiran ne yayin da yake kaddamar da jerin ayyukan raya al’umma a mazabar Tudun Wada da Gama.
Ya jaddada muhimmancin matasa, musamman waɗanda suka kai shekaru 18 a kwanan nan, da kuma waɗanda suka rasa ko katinsu ya lalace, da su tabbatar sun yi rijista domin su samu damar shiga cikin zaɓuɓɓukan da za su zo nan gaba.
Shugaban karamar hukumar ya ce yin rijistar zaɓe hanya ce ta bai wa ‘yan ƙasa damar cika haƙƙin su na dimokuraɗiyya da kuma zaɓar shugabanni na gari masu cancanta da gaskiya.
A wani bangare na jawabin nasa, Imam ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na haɓaka ci gaban, inda ya kaddamar da ayyuka sabbi guda bakwai, wanda suka haɗa da gine-ginen magudanan ruwa da gadaje da akwaku a wasu yankuna na Tudun Wada da Gama.
Khadijah Aliyu/Kano