Aminiya:
2025-11-15@11:23:52 GMT

’Yan bindiga sun kashe ’yanga 16 sun sace mutane 42 a Neja

Published: 15th, November 2025 GMT

’Yan banga 16 sun kwanta dama a yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 a wani hari na daban a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja.

Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hare-haren ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sa mutane da dama yin ƙaura daga ƙauyuka

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun fara kai farmaki ne a ƙauyen Dutsen Magaji, inda suka yunwa mutane 22 kisan gilla.


“Da suka kawo hari, ’yan banga sun bi su, ɓangarorin suka yi musayar wuta, amma suka kashe ’yan Banda biyar, wasu uku na karɓar magani a Asibiti.”

Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU Mutum ɗaya ya rasu yayin da ’yan sanda da ’yan bindiga suka yi artabu a Kwara

Ya ce daga baya ’yan bindiga suka kawo sabon hari da asuba, ranar Alhamis a yayin da ake Sallar Asuba a ƙauyen Magama, suka yi garkuwa da mutane 20.

“Nan ma da ’yan bindiga suka bi su, ashe sun yi kwanton ɓauna, suka kashe ’yan banga 13, suka jikkata wasu da dama.”
Sakataren Yaɗa labaran Shugaban Ƙaramar Hukumar Mashegu, Isah Ibrahim Bokuta, ya tabbatar da hare-haren, tare da jinjina wa ’yan bangar bisa yadda suka sadaukar da ransu domin kare al’umnarsu.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Neja, Wasiu Abiodun, amma ya ce zai tuntuɓe shi daga baya, idan ya bincika.

A gefe guda, mazauna yankin sun shaida mana cewa tun ranar Litinin al’ummomi da dama sun yi gudun hijira zuwa Mashegu, Kawo-Mashegu, Manigi da wasu wurare. Wasu kuma sun fake a gidajen ’yan uwansu a nesa domin tsira.

Majiyoyi sun ce cikin ƙauyukan da aka watse har da Dutsen Magaji, Borin Aiki, Gidan Ruwa da Magama.

Hakazalika har yanzu masu garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Neja, Alhaji Alhassan Bawa Niworo, ba su sake shi ba, makonni bayan rahoton cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa na Naira miliyan 70.

An yi garkuwa da Niworo ne a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025, tare da Kwamishina na Dindindin II na Hukumar Zaɓe ta Jihar Neja (NSIEC), Barrister Ahmad Mohammed, direbobinsu da wasu matafiya a kan titin Mokwa–New Bussa, a Karamar Hukumar Borgu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan banga Yan Bindiga Garkuwa yan bindiga suka

এছাড়াও পড়ুন:

Mutum ɗaya ya rasu yayin da ’yan sanda da ’yan bindiga suka yi artabu a Kwara

An kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne, yayin wani artabu da ’yan sanda da ’yan sa-kai suka yi da wasu mahara a Jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Adekanbi, kusa da garin Bode Saadu.

Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun yada zango a saman wani dutse da ke kallon ƙauyen.

Suna hangar jami’an tsaro sai suka fara harbi ba ƙaƙƙautawa.

’Yan sanda da jami’an sa-kai sun yi artabu tare da tarwatsa maharan, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunin harbin bindiga.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

Bayan an artabun, jami’an tsaro sun duba yankin, inda suka samu gawar mutum ɗaya da ake zargin ɗan bindiga ne.

Haka kuma an gano bindiga ƙirar AK-49 da harsasai 32 a wajen.

SP Adetoun, ta ce wannan aikin wani muhimmin ci gaba ne a ƙoƙarin da rundunar ke yi wajen kawar da masu aikata laifi a jihar.

Ta kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa yaƙi da laifuka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mayaƙan ISWAP sun sace Janar sun kashe sojoji a Borno
  • Yadda ’yan bindiga suka kashe banga 16 suka sace mutane 42 a Neja
  • Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola
  • ’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi
  • Mutum ɗaya ya rasu yayin da ’yan sanda da ’yan bindiga suka yi artabu a Kwara
  • Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70
  • HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya
  • Jihar Kwara Ta Jaddada Kudirin Tallafa wa Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafin Jinsi
  • Jihar Jigawa Za ta Kashe Sama da Naira Biliyan Daya Domin Inganta Ayyukan Wutar Lantarki