Gwamnatin Jigawa Ta Himmatu Wajen Inganta Harkokin Kiwon Lafiya a Jihar
Published: 12th, November 2025 GMT
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al`ummar jihar.
Babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim ya bada wannan tabbacin a dakin taro na ma’aikatar lafiya ta jihar a Dutse.
Yace ayyukan da za’a gudanar a asibitocin sun hada da samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da ruwan sha.
Sauran sun hada da kewaye asibitocin domin inganta yanayin aiki da al’amuran tsaro.
Dakta Kabiru Ibrahim ya kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa kokarinta na tallafawa harkokin kiwon lafiya a jihar.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Kiwon Lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki.
Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse.
Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni.
Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba.
Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari fili domin yin karin gine gine a asibitin.
Tunda farko a nasa jawabin, Babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura yace sun kai ziyarar ce domin gabatar da kansu da kuma neman karin hadin kai da goyan bayan gwamnatin jihar wajen ci gaban asibitin.
Dr. Salisu Babura ya shedawa Gwamnan ma’aikatan asibitin da gwamnatin tarayya ke biyan albashi sun kai 877.
Ya kuma yi nuni da cewar cikin adadin, guda 250 sun fito ne daga jihar jigawa.
Kazalika, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa hadin kai da goyan bayan da ke baiwa asibitin.
Yana mai fatan kara bullo da wasu hanyoyi domin magance kalubalen da ke fuskantar asibitin a yanzu.