Leadership News Hausa:
2025-11-13@12:57:04 GMT

Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu

Published: 13th, November 2025 GMT

Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu

 

Daga karshe Tanimu Akawu ya shawarci matasa masu sha’awar shiga harkar fim da su kasance masu hakuri kada suyi hassada kuma su dage da addu’oi, Harkar fim sana’ace da ake samun rufin asiri da daukaka, kuma fim sana’ace wadda sai dai kai ka barta ba dai ta barka ba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Nishadi Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala November 8, 2025 Nishadi Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar November 1, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales October 25, 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25

1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo 

Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari a gaba.

Ko da yake ƙungiyar sau da yawa tana saumn rinjayan samun kwallo da kirkirar damar kai hari, amma kash suna gaza amfani da waɗannan damarmaki zuwa nasara. Wanda hakan yake nuna rashin ‘yan wasa masu ƙwarewa da zasu ci kwallon, wanda ya sa ake dogaro da wanda suka kwana biyu kamar Rabiu Ali, yana iya kokarinsa amma ba aikinsa ba ne kuma tsufa ya cimmasa.

2. Tallafin Gwamnati — Jin Dadi Ba Tare da Tasiri Ba

Ba kamar mafi yawan ƙungiyoyi a gasar NPFL ba, Pillars suna samun cikakken tallafi na kudi da walwala da duk goyon bayan da suke bukata daga Gwamnatin Jihar Kano. Albashi da ƙarin lada (bonus) suna samu a kai a kai, kuma wuraren horonsu yana ɗaya daga cikin mafi kyau a arewacin Nijeriya. Sai dai jin dadi ya gaza nunawa a cikin fili.

Samun jin daɗi ga kuma rashin nasara ya nuna cewa motsa sha’awa a ƙwallon ƙafa ba kawai maganar kudi ce ba, yana bukatar babban buri daga kungiya da yan wasa, da hangen nesa, da sha’awar yin nasara a aikace. Wasu ‘yan wasan ba su da yunwar kafa wani sabon tarihi, ba su da babban burin samun wata dama ko nuna kansu ko kuma fito da sunansu.

3. Tsoma Baki a Shugabanci

Wani muhimmin dalili da ya cefa ƙungiyar cikin wannan mummunan hali shi ne tsoma baki a shugabanci da yadda ake tafiyar da kungiyar. Wasu bayanai sun nuna cewa ana matsa lamba ga masu horarwa kan zaɓin ‘yan wasa, ko salon dabarun shiga fili a taka leda, da yayin sayen ‘yan wasa.

Wannan tsoma bakin yana rage amincewa daga magoya baya sosai, yana haifar da rikici na zaman doya da manja tsakanin yan wasan da wasu mahukunta, kuma yana hana masu horarwa aiwatar da amfani da dabarun da zasu iya kai wa ga nasara.

Ci gaba na gaske zai zo ne kawai idan kowa ya janye hannu ya bar ƙungiyar da masu horarwa su ɗauki cikakken hukunci da alhakin duk wani sakamako da ya biyo baya na nasara ko akasaninta.

4. Matsalar Gane Dabarun Ƙungiya

Idan aka kalli Pillars a yau, yana da wahala a iya bayyana wane dabaru su suke amfani da shi. Shin ƙungiya ce mai matsawa gaba-gaba (attacking)? Ko suna jiran dama don kai hari (counter attack)? Ko ƙungiya ce mai riƙe kwallo kamar Manchester city ko Barcelona?

Gaskiyar ita ce, suna haɗa komai amma ba ko yaushe ne ake iya ƙwarewa a komai ba. A yanzu sun haɗa komai ba tare da ƙwarewa a ko ɗaya ba.

Ta hanyar dogaro da wasannin baya na salon da suke amfani da shi na amfani da gefe da kuma yawan aika dogayen ƙwallo ta sama ya sa abokan taka leda sun gane Pillars Cikin sauƙi, musamman idan ana wasa da ƙungiyoyin da suke rufe gida sosai. Don dawo da martaba, ƙungiyar ana buƙatar sabunta dabaru da koyon saurin sauya salo idan wata dabara ta gaza aiki.

5. Matsin Lamba Daga Magoya Baya Da Koyon Sarrafa Fushi

Kano Pillars suna da magoya baya mafi ƙarfi a Nijeriya. Amma ƙauna na iya sauyawa zuwa matsin lamba. Wasannin gida a filin Sani Abacha, wanda a da ya kasance tsani mai tsoro gare su, amma a yanzu sun kasance da damuwa ga ‘yan wasa da ke tsoron fushin magoya baya a kowane wasan da suka yi rashin nasara.

Sarrafa tsammanin magoya baya ta hanyar magana a fili da nuna cewa nasara da rashin duk wani fanni na rayuwa da kuma a wasanni na da mahimmanci wajen dawo da ƙwarin gwuiwar masu kallo da kuma ɗakin sauya kaya.

A rubutu na biyu nazarina ya zurfafa cikin matsalolin tsarin fasalin ƙungiyar, al’adu, da wasu abubuwan ke hana ƙungiyar ci gaba tun daga damuwa kan lafiyar ‘yan wasa fargabar zuwan Azumin da ƙarancin ‘yan wasa a wasu sassan, da rashin tabbas na shugabanci, da buƙatar gaggawa yin hangen nesa don samar da ci gaba mai ɗorewa.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Nijeriya Za Ta Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Gusau November 13, 2025 Wasanni ‘Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 10 Da Za Su Iya Buga Gasar Cin Kofin Duniya Ta Ƙarshe A 2026 November 13, 2025 Wasanni Kofin Duniya 2026 Zai Zama Na Ƙarshe A Wuri Na – Ronaldo  November 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25
  • MDD ta sanya Najeriya cikin ƙasashe 16 da ke fama da tsananin yunwa
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina
  • Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfado Da Filin Jirgin Sama Na Kano
  • An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba
  • Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Gina Hanyoyi Ba Naira Biliyan 81 A Malam Madori
  • Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin