Sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mutum 94
Published: 15th, November 2025 GMT
Dakarun Sojin Najeriya, sun ci gaba da ƙaddamar da hare-hare a faɗin ƙasar nan, domin murƙushe ’yan ta’adda a yankunan daban-daban.
A cikin makonni biyu da suka wuce, sojoji sun kashe ’yan ta’adda da dama, sun cafke mutum 94, kuma sun ceto 67 da aka yi garkuwa da su.
Mahara sun kashe matan aure sun ƙona gidansu a Kano Yadda ’yan bindiga suka kashe banga 16 suka sace mutane 42 a NejaDaraktan Hulɗar da Jama’a na Rundunar Tsaro, Manjo-Janar Olatokunbo Bello ne, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja, yayin da yake bayyana rahoton ayyukan rundunar daga 3 zuwa 14 ga watan Nuwamba.
Ya ce sojoji sun ƙwato bindigogi masunyawa, ciki har da rokoki, bindigogi ƙirar gida, da kayan haɗa bam.
Hakazalika, ya ce sun lalata sansanonin ’yan ta’adda da wuraren da ake ƙera musu makamai.
Arewa Maso GabasA Jihohin Borno da Adamawa, sojojin Operation Haɗin Kai, sun ci gaba da fatattakar Boko Haram da ISWAP, inda suka kashe adadi mai yawa.
Haka kuma sun kama mutane 45 da ake zargin su da bai wa ’yan ta’adda bayanai da makamai, sannan sun ceto mutum ɗaya da aka sace.
Arewa Maso YammaA ƙarƙashin Operation Fagge Yamma, sojoji sun kashe ’yan ta’adda da yawa a Jihohin Sakkwato, Zamfara, Neja, Katsina, Kebbi da Kano.
Sun kama mutum biyu, sun kuma ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato makamai, motocci da dabbobi.
Arewa ta TsakiyaA Jihohin Filato da Kaduna, sojoji sun yi artabu tare da kashe mahara, sun kama mutum 16, sannan sun ceto mutum biyar.
Haka kuma, sun kama wani ƙasurgumin ɗan ta’adda mai suna Ibrahim Wakili a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna a ranar 9 ga watan Nuwamba.
Sauran Hare-hareA Jihohin Kogi, Kwara, Binuwai, Nasarawa da Taraba, sojojin Operation Whirl Stroke, sun kashe ’yan ta’adda da dama, sun kama mutum 10, sannan suka ceto mutun 48 da aka sace.
Sun kuma kama wasu da ke yin safarar makamai da masu taimaka wa ƙungiyoyin ta’adda guda biyu a Nasarawa.
A yankin Neja Delta kuwa, sojojin Operation Delta Safe, sun daƙile yunƙurin satar mai da darajarsa ta kai Naira miliyan 15.8.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Arewa maso Gabas Arewa maso yamma Arewa ta tsakiya Garkuwa yan ta adda da
এছাড়াও পড়ুন:
Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya
Haka zalika, a 2025, an samu kararraki 28 na ‘yan Nijeriya da suka kashe kansu. Shari’ar ta shafi mutane daga kowane jinsi da kuma masu matsayi daban-daban, ciki har da dalibai da kuma ‘yan kasuwa.
Da yake zantawa wani dan jarida, masanin ilimin halayyar Dan’adam, kuma kwararre a kan lafiyar kwakwalwa, Dakta Shuab Waidi ya ce; batun kisan kai a halin yanzu, na bukatar da kulawar gaggawa ga mahukuntan kasa.
Ya ce, “Kididdigar na nuna cewa, a kowane minti 33; ana asarar rai a Nijeriya sakamakon kashe kai, don haka, akwai bukatar cikin gaggawa a bude tattaunawa game da kashe kai ta hanyar gwajin lafiyar kwakwalwa.
“Cutar tabin hankali, wani bangare ne na kisan kai da kai, amma kashe kai ba cutar tabin hankali ba ce, domin kuwa tana da alaka da yanayin dabi’a mai rikitarwa da kuma yanayin zamantakewa.
“A yayin da sama da mutum 720,000 ke mutuwa a duk shekara daga masu kashe kansu a duk duniya, Nijeriya ba za ta iya daukar wannan batu a matsayin gazawar dabi’a ko kuma sakamakon shan muggan kwayoyi kawai ba.
Har ila yau, shugaban sashen kula da masu tabin hankali na cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Keffi a Jihar Nasarawa, Dakta Hassan Galadima ya ce; yanayin kashe kai a halin yanzu, na nuna matukar halin damuwa da ake ciki.
“An fi samun maza fiye da mata wajen yunkurin kisan kai, ta yadda suka mayar da al’amarin tamkar wata gasa. Har ila yau, ana samun yukurin afkawa cikin teku, wanda a halin yanzu ya zama ruwan dare fiye da rataye kai ko shiga gaban motoci,” in ji shi.
Ya kuma alakanta hakan da abubuwa da dama da suka hada da matsin lamba na ilimi, tabarbarewar arziki da ramuwar gayya da asiri da sauran makamantansu da suka zama ruwan dare a tsakanin matasa.
Dalilan Da Ke Haifar Da Matsalar Kisan Kai
A nasa ra’ayin, Shugaban Kungiyar Likitocin Iyali na Nijeriya (SOFPON), shiyyar Kudu-maso-Kudu, Dakta Iyang Aniete ya ce; Nijeriya na fuskantar matsalar kunar-bakin-wake da ta barke, aka kuma yi shiru, ba a magana a kai.
Ya kara da cewa, “Tare da kiyasin mutuwar mutane 15,000 a duk shekara da kuma aikata laifin yunkurin kashe kai a kasar, inda kuma ake hana mutanen da ke cikin wahala neman taimako.
Kashi 77 cikin 100 na kashe-kashen da ake yi, na faruwa ne a kasashe na masu karamin karfi da matsakaita, Nijeriya mai yawan al’umma sama da miliyan 200, na daya daga cikin wuraren da ake samun masu kashe kawunansu a duniya, inda aka kiyasta masu kashe kansu da kashi 17.3 cikin 100,000, wanda ya zarce na duniya (10.5 cikin 100,000) da kuma Afirka (10.00) da kuma Afirka (10.00).
Ya ci gaba da cewa, yawan kunar bakin wake a Nijeriya ya zarce 10.5/100, 000 a duniya, sai kuma na Afirka 12.0/100,000, yayin da Lesotho ke kan gaba a 72.4/100,000. A shekarar 2023, an samu rahoton kashe mutane kusan 83 a Jihar Legas kadai.
Kashi 15 cikin 100 na wadanda suke kashe kansu, mutanen da ba a kula da su ne.”
A cewarsa, a wani bincike da aka gudanar a Nijeriya, kashi 80.6 cikin 100 na wadanda abin ya shafa maza ne, kashi 51.8 cikin 100 sun yi aure, kashi 33.6 cikin 100 dalibai ne, kashi 2.3 cikin 100 kuma suna tsakanin shekaru 25 zuwa 34.
“Mutuwar kashe kai, ana ganinta a matsayin wani babban zunubi, kuma haramun; wanda mugaye ne kadai ke iya yi, don haka; iyalan da abin ya shafa, galibi ana kyamar su tare da kin sakin jiki da su ta hanyar zamantakewa, don haka; sun gwammace su boye mutuwar ’yan’uwan nasu, domin kuwa suna bayyana irin wannan kisan kai a matsayin mutuwar ganganci.
“Yawancin shari’o’in da aka ruwaito, sun dogara ne da bayanan ‘yansanda da kuma na asibiti.
“Shaidar bincike kan halin kashe kai a Nijeriya sun hada da amfani da sinadarai, yanka kai, kona kai da kananzir, rataye kai da kuma amfani da bindigogi a matsayin hanyoyin kashe kai,” in ji shi.
A cewar wata mai ilimin sanin halayyar Dan’adam, Charity Dogo, “Daga cikin manyan abubuwan da ke jawo kashe kai, akwai abubuwa masu hadari na mutum, ciki har da matsalolin kudi, tarihin iyali na wani ya kashe kansa, rashin lafiya, rashin lafiyar jiki da shaye-shaye da sauran makamantansu.”
Ta kara da cewa, “Yayin da alakar da ke tsakanin kashe-kashe da tashe-tashen hankula, musamman bakin ciki da matsalar shan barasa ya samu wurin zama sosai a Nijeriya, yawancin kashe-kashen kuma na faruwa ne da gangan a lokutan rikici tare da rashin iya magance matsalolin rayuwa, kamar matsalolin kudi, rabuwar dangantaka ko ciwo mai tsanani da kuma rashin lafiya.
“Bugu da kari, fuskantar rikici, bala’o’i, tashin hankali, cin zarafi ko asara da kuma kebewa wuri guda na da alaka da wadannan kashe-kashe na kai, kai tsaye.”
Ta ci gaba da cewa, “Akwai alaka tsakanin yadda ake yada shafukan sada zumunta, ba tare da wata ka’ida ba; da kuma karuwar kashe-kashen da matasa ke yi.”
Charity ta kara da cewa, “Matsakaitan matasa a duniya a yau, suna kokawa game da matsalolin yau da kullum, wadanda ka iya taimakawa wajen fadawa wannan mummunan hali.
“Yanayin zama na yau da kullum, shi ma na taimakawa. Don haka, yawancinsu suna kokarin sarrafa shi tare da wuce gona da iri a kafofin watsa labaru, sannan muna da yawan cin zarafin juna a wadannan kafofi na watsa labaru.
“Wani abu da amfani da kafofin watsa labaru ke yi shi ne, yana bude wasu kofofi ko hanyoyi masu matukar cutarwa.”
Wata likitan mahaukata, Abimbola Owoeye, a nata ra’ayin, ta bayyana tabarbarewar zamantakewa a tsakanin iyalai a matsayin abin da ke matukar taimakawa.
Sannan ta lura cewa, yawancin matasa ba sa yin hulda tare da danginsu, suna zabar yin hulda ko abota da fasahar sadarwa (AI), a kan su yi alaka da dan’uwansu Dan’adam.
“Wannan rashin kyawawan dabi’u a tsakanin iyali da kuma hadin kai,” in ji ta, “na iya haifar da rashin matsaloli, musamman a kan lafiyar kwakwalwa.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA