Aminiya:
2025-11-12@17:18:11 GMT

’Yan sanda sun kama mutum 14 kan zargin ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Jigawa

Published: 12th, November 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu mutum 14 da ake zargi da ta’amali da miyagun ƙwayoyi da kuma aikata wasu laifuka daban.

Kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse, babban birnin jihar.

MDD ta sanya Najeriya cikin ƙasashe 16 da ke fama da tsananin yunwa DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotu

A cewar SP Shiisu, jami’an rundunar sun kama mutanen ne a wurare daban-daban da suka haɗa da Dutse, Guri, Babura, Kanya Babba, Bulangu da kuma ‘Yankwashe.

Ya ce rundunar ta ƙwato miyagun ƙwayoyi iri-iri da suka haɗa da Exol guda 8,271, D5, Tramadol, Diazepam, Sholisho, Sukudayin, tabar wiwi, da kuma kuɗi Naira 235,225.

SP Shiisu, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da farautar duk wanda yake da hannu a harkar.

Ya ƙara da cewa za su gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu da zarar sun kammala bincike, domin su fuskanci hukuncin da ya dace da laifukansu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Jigawa Miyagun Kwayoyi

এছাড়াও পড়ুন:

DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar.

A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko wasu ‘yan kaɗan ke da ɗaruruwan masu tsaro a gefensu.
Ko yaya tasirin tura ‘yan sanda tsaron wasu daidaikun mutane maimakon tsaron alummar kasa gaba daya?

NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai

Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotu
  • AIG Zubairu Ya Umurci ‘Yan Sanda a Kwara Su Ninka Kokarinsu Don Karfafa Tsaro
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina
  • Araghchi: Matsalar Yammacin duniya ita ce ci gaban kimiyyar Iran ba makaman nukiliya ba
  • Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba
  • DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma
  • ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa
  • Gwamnatin Tarayya Ta Jinjinawa Gwamnan Jigawa Bisa Ayyukan Ci Gaban Jihar