2025-11-11@22:03:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 51
«tsara shirye shirye»:
Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar Ansarullah Abdul-malik al-houthi yayi gargadin cewa yankin yana gab da fuskantar gagarumin rikici da isra’ila da kasashen yamma a yanki, don haka yasha alwashin cewa tsayin dakar dakarun kasar yafi karfi fiye da baya kuma a shirye take ta kalubalanci duk wanda yayi mata shisshigi a nan gaba. Wadannan kalaman suna nuna irin yadda ake samun karuwar fadace-fadace a yammacin asiya yayinda kungiyoyin dake goyon bayan yan gwagwarmayar daga yaman da labanon ke ciin shirin ko ta kwana na yaki da isra’ila da kawayenta na kasashen turai, haka kuma jawabin ya jaddda irin dabarun yaki da kungiyoyin yan gwagwarmaya da isra’ila suka bi bayan yakin gaza da kuma sabunta kokarin sojojin Amurka a yankin...
Sakamakon da aka fitar a jiya Litinin ya bayyana cewa, Alassan Outara dan shekaru 83 ya lashe zaben a kaso 89.77 na jumillar shugaban. Mutum na biyu wanda yake bin Outara a baya shi ne tsohon ministan kasuwanci Jean-Lous Billon da kaso 3%, sai kuma mai dakin tsohon shugaban kasar Simone Gbango da ta sami kaso 2.4%. Tuni dai Billon ya taya Ouattara murnar cin zaben, bayan da ya yarda ya sha kaye. Tare da cewa a karkashin shugabancin Ouattara kasar ta Ivory Coast ta sami ci gaban tattalin arziki, sai dai masu bin diddigin siyasar kasar suna yin suka akan wasa da tsarin mulkin kasar domin bayar da damar ci gaba da tsayawa takarar Alassan Ouarrata. A zaben da...
Shugaba Alassane Ouattara, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙasar Ivory Coast wanda ya ba shi sabon wa’adin mulki a karo na huɗu. Ouattara mai shekaru 83, ya samu kashi 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar a ranar Litinin. Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Fiye da mutane miliyan tara ne suka cancanci kada ƙuri’a a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, wanda aka gudanar cikin yanayi na fargaba, bayan da manyan abokan hamayyarsa biyu — tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo da tsohon shugaban Credit Suisse, Tidjane Thiam — aka hana su tsayawa takara. Sakamakon ya nuna cewa, duk da ƙarancin fitowar...
A Ivory Coast sakamakon wucin gadi na zaben shugaban ya nuna cewa Shugaba Alassane Ouattara, wanda ke jagorantar kasar tun 2011, na kan lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Oktoba, 2025 da gagarumin rinjaye. Rahotanni sun ce Ouatara ya samu kashi 89.77% na ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga sakamakon wucin gadi da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (IEC) ta fitar dazu. Duk da cewa sakamakon zaben bai ƙare ba tukuna, amma Ouatara da ke jagorantar tun 2011 yana kan hanyarsa ta zuwa wa’adi na huɗu a kan karagar mulkin ƙasar, bayan sake zaɓensa a 2015 da 2020. A wannan Litinin, Hukumar zaɓe ta ƙasa da ƙasa (IEC) ta sanar da cewa Alassane Ouattara, mai shekaru 83, na...
Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i. Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000 daga gwamnatin tarayya wanda zai taimaka wa sana’o’insu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen ƙirƙirar ayyuka, wanda yanzu haka an samar da kuɗaɗai har naira biliyan 5.5, inda aka raba biliyan ɗaya ga mutane 701 a faɗin jihar. Gwamna Raɗɗa...
Mataimakin babban kwamandan rundunar sojin Iran kan hadin gwiwa ya jaddada cewa: Sojojin Iran a shirye suke su fuskanci kowace barazana Mataimakin Babban Kwamandan Rundunar Sojin Iran kan Hadin Gwiwa, Rear Admiral Habibullah Sayyari, ya ce: An zabi Sojojin Iran daga cikin mafi kyawun matasa a kasar kuma suna shirye su fuskanci kowace barazana. A gefen bikin bude gasar cin kofin duniya ta 4 ta sojojin masu harba kibau (SIZM 2025), wadda rundunar sojin sama ta shirya a kungiyar masu harbi a ranar Juma’a da yamma, Rear Admiral Sayyari ya yi magana da manema labarai game da matakin shirye-shiryen Sojojin da kuma rawar da wasanni ke takawa wajen inganta karfinsu. Ya jaddada cewa, “Wasanni suna da matukar muhimmanci ga lafiyar...
Sashen haƙar ma’adinai na Cote d’Ivoire da ke samun ci gaba cikin sauri zai fuskantar matsala da tsaiko kafin zaɓen shugaban ƙasa na ranar Asabar, yayin da Shugaba Alassane Ouattara ke neman wa’adi na hudu. A cewar Reuters, haƙar ma’adinai muhimmin ɓangare ne daga cikin ayyukan da Ouattara yake mayar da hankali a kansu, don haɓaka tattalin arzikin kasar wadda ita ce ta farko wajen samar da koko a duniya. Tun lokacin da ya hau mulki a 2011, ayyukan samar da zinare suka habaka daga kimanin tan 10 na metric a 2012 zuwa fiye da tan 58 a 2024, tare da burin kaiwa tan 100 nan da 2030. Majiyoyi uku na masana’antar haƙar ma’adinai sun ce masu hakar ma’adinai suna...
Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, shi ne wanda aka fi yi wa hasashen nasara a zaɓen da za a gudanar a Ivory Coast ranar Asabar, sakamakon rashin wasu jiga-jigan ’yan adawa da za a fafata da su a zaɓen. Ouattara, mai shekara 83, yana riƙe da madafun iko tun daga shekarar 2011, lokacin da ƙasar ta fara warwarewa daga rikicin siyasa kuma ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke taka rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin yammacin Afirka. Jerin ’yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon Afirka na bana Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani A ƙarƙashin mulkinsa, Ivory Coast — wacce ita ce babbar mai...
An Fara Nuna Hotuna Da Shirye-Shiryen Bidiyo Da Matasan Kasa Da Kasa Suka Dauka Don Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafa MDD A Kasar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An samu damar tattauna muhimman abubuwa a babban taron kamar hanyoyin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara na Nijeriya da kuma yankin Bungoma na ƙasar Kenya. Manyan mambobin kwamitin sun tattauna damarmakin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara a Nijeriya yankin Bungoma na Kenya. A jawabin sa ga masu zuba hannun jari a duniya, Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen sauya labarin Zamfara daga ƙalubale zuwa wani babban matsayi mai cike da damarmaki. “Gwamnatina ta himmatu wajen samar da ingantaccen yanayi da ɗorewar yanayin zuba jari. Ina nan a yau a matsayin abokin tarayya, a shirye nake na ba ku cikakken haɗin kai don buɗe hanyoyin jin daɗin gare mu duka....
Ƙungiyar masu kafafen yada labarai na Arewa za ta daukaka kara kan hukuncin kotu a kan tashar Arewa24
Ƙungiyar masu kafafen yaɗa labarai ta Arewacin Najeriya (NBMOA) ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na yin watsi da ƙarar da ta shigar a kan tashar Arewa24, inda ta ce za ta ɗaukaka ƙara. Idan za a iya tunawa, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a watan Agusta, ta yi watsi da karar da kungiyar NBMOA ta shigar a kan Arewa24, saboda “rashin hukunci da rashin cancanta”, kamar yadda aka gani a cikin kwafin takardar hukuncin kotun (CTC). Kotun, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta tabbatar da cewa AREWA24 tana gudanar da harkokinta ne bisa ƙa’ida, kuma ba ta da hurumin samun ƙarin lasisin gudanar da ayyukanta, ba tare da karya wata doka...
Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari. Abba ya yi wannan kira ne ta bakin wani mai fassara a taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen tattaunawa kan kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka shirya don inganta aiki. Ya ce rashin masu fassara a asibitoci alama ce ta rashin kula da kurame a jihar, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don tabbatar da samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum...
Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC). Kilishiyar Waja ta tallafa wa matan gidan yari da kayayyaki a Gombe Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata Babban Daraktan Kamfanin Media Trust, Malam Ahmed I. Shekarau ne, ya bayyana wannan ci gaba. Ya bayyana hakan a matsayin abin alfahari, inda ya ce Trust Radio za ta mayar da hankali kan yaɗa shirye-shirye na gaskiya, adalci da kuma abin da ya shafi jama’a. Za a riƙa watsa shirye-shirye daga Abuja...
Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya. A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.” Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan. Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka...
Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya. A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina. An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa, shekaru arau-aru. Mahaya dawaki da sauran mahalarta bikin daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje da mazauna garin Daura sun fara tururuwa zuwa filin bikin, wanda zai samu. An kuma shirya gudanar da gagarumin hawan daba a Fadar Sarkin Daura, albarkacin zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na 10. A wannan ranar ake cika shekara 10 da fara wannan gagarumin biki,...
An gabatar da dukkan shirye-shirye bisa tsari da inganci kuma ba tare da tangarda ba, inda aka cimma dukkan abubuwan da ake buri. An shirya gudanar da katafaren taron wanda zai kunshi faretin soja ne a ranar 3 ga watan Satumba. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A fannin noma ma, watsa shirye-shiryen da Sinanci zai taimaka wajen bayyana burin Nijeriya na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, musamman yadda take neman aikewa da karin kayayyakin amfanin gona zuwa babbar kasuwar kasar Sin, tare da bai wa masu ruwa da tsaki na kasar Sin damar sanin abubuwan da Nijeriya za ta iya yi, da ka’idojinta ta yadda hakan zai kara daidaita al’ummomin kasashen biyu kan dabarun kasuwanci da kara habaka musayar noma. A halin yanzu, masana’antun kirkire-kirkiren fikira da na fina-finai, da na kayan kwalliya, da kide-kide da wake-wake suna taka rawar gani wajen harkokin al’adu da kasuwanci. Watsa shirye-shirye da Sinanci zai bai wa masu ruwa da tsaki a wannan fani na kirkire-kirkiren fikira na Nijeriya...
Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba. Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki. Ya bayyana cewa, “Ni dan takara...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Litinin a lokacinda yake ganaw da sabon jakadan kasar Faransa a Tehran pierre Cochard wanda ya mika masa tarkardun fara aikinbsa. Shugaban ya kara da cewa an takurawa kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya a bayan. Amma daga yanzun kuma ba zata amince da irin takurawa ta bay aba. Ya kuma bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da kasashe...
Daraktan Gidajen Rediyon Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Ndace, ya bayyana cewa an kammala shirin fara watsa shirye-shirye da harshen Mandarin, wanda shi ne harshe a hukumance na ƙasar China. Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai tare da tawagar VON ga Jakadan China a Nijeriya, Yu Dunhai. Ndace ya ce ƙara harshen Mandarin zai kawo yawan harsunan da VON ke amfani da su zuwa tara. A yanzu, hukumar na watsa shirye-shirye da Hausa, Igbo, Yarbanci, Fulfude, Turanci, Faransanci, Larabci da Swahili. Ya bayyana cewa dukkan kayan aiki da tsare-tsare sun kammala don fara aikin, da nufin tabbatar da ɗorewar wannan sabon shiri. China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga...
A kokarin ta na inganta jin dadin al’umma, Gwamnatin jihar Jigawa ta gudanar da aikin tantance masu bukata ta musamman 200 a yankin Karamar Hukumar Birnin Kudu. A jawabin daya gabatar, shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammad Uba ya godewa gwamnatin jihar bisa kula da jin dadin masu bukata ta musamman a yankin da ma jihar baki daya. Dr. Builder Muhammad, yace a baya akwai masu bukata ta musamman mutum 61 da ke con gajiyar shirin a yankin amma a yanzu kuma gwamnatin jihar ta amince a kara 139 da za a zabo daga mazabu 11 na yankin. Builder, wanda ya sami wakilcin Kansila mai kula da shirin walwalar jama’a na yankin, Alhaji Ahmed magaji Bashir, yace Karamar Hukumar za...
Ya ce, nan da shekarar 2030 za a bukaci hekta miliyan 300 domin samar da bukatar abinci. Don haka ne ya ce taken taron ranar yaki da kwararowar hamada na 2025 na da matukar tasiri domin tabbatar da daukan matakan da suka dace wajen kiyaye hamada da gurbacewar muhalli. A cewarsa, yunkurin zai tunkari manyan kalubale kamar matsalar tattalin arziki da karancin abinci, karancin ruwa, da sauyin yanayi. Lawal ya jaddada cewa cimma muradun ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya ba zai yuwu ba idan ba tare da kare muhalli da kuma kula da filaye da albarkatun kasa ba. Ya kara da cewa gwamnati na ba da fifiko ga al’amuran muhalli kuma ta samar da cibiyoyi, manufofi, tsare-tsaren ayyuka,...
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM), sun fara aikin tantance ɓarnar da ambaliya da iska suka yi a yankunan Kudancin Kaduna. Manufar aikin ita ce su tattara sahihan bayanai daga jama’a da shugabanninsu domin a samu taimako da kuma tsara hanyoyin kare aukuwar hakan a gaba. Sabon harin Iran ya hallaka mana mutum 8 – Isra’ila NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je Ko’ina Ba Yayin da suka kai ziyara Ƙaramar Hukumar Jama’a, Ko’odinetan KADSEMA na Kudancin Kaduna, Mista Ayyuka Shemang, ya ce sun fara wannan aiki ne saboda hasashen ambaliya daga Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMet). Ya jaddada muhimmancin...
A yau Jumma’a, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya yi hadin gwiwa da kawancen gidajen rediyon Turai na EBU wajen gabatar da rahoton Report ITU-R BT.2550, wato fasahar tsara shirye-shiryen bidiyo da rediyo ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta 5G, a shafin intanet na kwancen harkokin sadarwa na duniya wato ITU. Lamarin da ya nuna cewa, CMG ya taka muhimmiyar rawa a fannin tsara shirye-shirye masu inganci, ya kuma kai matsayi na gaba a fannin fitar da fasahohin tsara shirye-shiryen zamani masu inganci. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya. Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu. Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran. A yayin taron manema labarai na mako-mako a birnin Paris, Christophe Lemoine ya jaddada cewa: “Muna ci gaba da jajircewa wajen warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye muke mu ci gaba da tattaunawa da Tehran.” Wannan bayanin na zuwa ne bayan da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X cewa, Tehran a shirye ta ke...
Kujeru dubu daya da dari hudu da bakwai ne aka ware wa hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Taraba domin maniyyata bana. Babban Sakataren Hukumar mai barin gado Umar Ahmed Chiroma ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan matakin da ake na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana na 2025 ba tare da tangarda ba. Aikin Hajji daya ne daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar kuma Musulmin muminai na gudanar da aikin Hajji a kowace shekara akalla sau daya a rayuwarsu. Chiroma ya ce hukumar ta kai wani mataki na ci gaba ta fannin shirye-shirye kamar yadda hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayar, inda ya ce sama da maniyyatan jihar...
Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na kawo sauyi da kuma zamanantar da kafafen yada labarai na Najeriya da watsa shirye-shirye ta hanyar hadin gwiwa da inganta fasaha. Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ne ya bayar da wannan tabbacin a taron manema labarai na 2025 da aka gudanar a cibiyar ‘yan jarida ta kasa da ke Abuja ranar Alhamis. Da yake jawabi bayan dawowar sa daga taron kungiyar masu yada labarai na duniya (NAB) a birnin Las Vegas na kasar Amurka, ministan ya ce taron mai taken “Fasahar, The Trend, The Future,” ya samar da wani dandali na yin cudanya da masu ruwa da tsaki a duniya kan sabbin abubuwa da suka...
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa, Iran a shirye take yin aiki tare da Saudiyya a dukkanin bangarori, domin cin gajiyar al’ummomin kasashen biyu da ma duniyar musulmi, tare da yin ishara da cewa, dukkanin ci gaban da Iran ta samu a dukkanin bangarori na ilimin kimiyya da fasaha, a shirye take ta taimaka ma Saudiyya a wadannan bangarori. Wannan na zuwa ne a lokacin da Ministan tsaro Yarima Khalid bin Salman dan uwa ga Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya gana da Ayatollah Khamenei a Tehran da yammacin jiya Alhamis don mika sakon Sarki Salman na Saudiyya. Jagoran ya ce: “Mun yi imanin cewa dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna cike da takaici da fushi kan ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take samu A yayin ganawarsa da manyan kwamandojin sojojin kasar Iran a yau Lahadi, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa; Ci gaban da Iran ta samu ya fusata da kuma kara takaicin masu mugun nufi kan lasar ta Iran. Yana mai bayyana cewa, tabbas akwai rauni a fannonin da suka shafi tattalin arziki da ya kamata a magance. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi la’akari da cewa; Sojojin kasar suna matsayin kariya ta al’umma da kuma mafakar al’umma daga duk wani mai wuce gona da iri, sannan kuma ya jaddada...
Ministan Yaɗa Labarai Ya Zayyana Wa Masu Zuba Jari Na Faransa Irin Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Nijeriya
Idris ya gode wa kamfanonin Faransa da suka daɗe suna aiki a Nijeriya, irin su TotalEnergies, Lafarge, Peugeot, Danone, Alstom, Schneider Electric da sauran su, saboda gudunmawar da suke bayarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan kamar makamashi, ababen more rayuwa, noma, lafiya da masana’antu. Idris ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya tana kan “tafarkin sauyi da ba a taɓa ganin irin sa ba” wanda Ajandar Sabunta Fata ke ɗauke da shi. Ya ce: “Waɗannan sauye-sauyen tarihi na gina tattalin arzikin da ya fi gasa, mai gaskiya da amfanar masu zuba jari, suna mayar da Nijeriya ƙofar shiga kasuwar masu saye ta Afirka wadda ke bunƙasa, ƙarƙashin Yankin Ciniki Cikin ’Yanci na Nahiyar...
Kamfanin Media Trust Limited na farin cikin sanar da al’umma cewa daga ranar Juma’a 11 ga watan Afrilun 2025, Rediyonta na Tusts Radio zai fara shirye-shiryen gwaji. Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke bi na faɗaɗa aikin watsa labarai sama da shekaru 27 a Nijeriya. An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta Kamfanin Media Trust shi ne mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya a Nijeriya kuma mamallakin Trust TV da kuma Trust Radio a yanzu. Ga waxanda ba su a birnin tarayya Abuja ko kuma...
Manchester City na nace kan buƙatar ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 27, yayin da take shirin rabuwa da ɗanwasanta na Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33. (UOL esporte – in Portuguese) Chelsea a shirye take ta biya fam miliyan 102 kan ɗanwasan Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24. (Fichajes – in Spanish) Manchester City na nazarin taya ɗanwasan tsakiya na AC Milan da Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 26, kan tsakanin fam miliyan 42 zuwa fam miliyan 51 duk da ya sabunta kwangilar shi har zuwa 2030. (Calciomercato – in Italian) Ana sa ran Everton za ta rasa ɗanwasan bayanta na Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 22, yayin da Manchester United da Tottenham ke hamayya...
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in ji Araghchi a wata wayar tarho da takwaransa na Holland, Caspar Veldkamp, yau Laraba. Ya jaddada cewa wannan “yana bukatar yanayi mai kyau da kuma nisantar hanyoyin da suka shafi barazana.” Ministan ya yi Allah wadai da barazanar da jami’an Amurka suka yi wa Iran da cewa “ba za a amince da su ba”, ya kara da cewa sun saba wa kundin tsarin mulkin MDD...
Sunana Naja’atu Baffa Jihar kaduna: Ni dai a gaskia ban son akwai wani anko da za ai wannan sallar ko babu ba. Ina son saka takalmi mai dan tudu ba sosai ba, sai mayafi blue black, sai atamfa ta riga (half bubu) da ‘skirt’, sai sarka da dankunne da Awarwaro ‘silver’. Ina sha’awar cin Snacks irinsu meatpie, samosa, doughnut da kuma cake, sai kuma Yoghurt mai inibi. Ina son in ziyarci kanwar babata wacce take a cikin garin Adamawa. Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa: To batun shidimar sallah sai mu ce Alhamdullilah domin duk tanadin da mutum yayi sai ya kare, duba da yadda kayayyakin suturu ko tufafi suke tsada don haka sai mutum yayi amfani da...
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce ta samu nasarar kammala rijistar maniyyata aikin hajjin bana 3,155. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Danbappa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Kano a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gudanarwar Hukumar Shige da Fice a ofishinsa. Danbappa ya bayyana cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye da suka hada da kwasa-kwasan horas da aikin hajji, da takardu da kuma tattara kayanai. “Yanzu haka hukumar ta fara bayar da biza ga maniyyatan da suka yi rijista. Ya yabawa gwamnatin jiha bisa yadda take ci gaba da tallafawa kokarin hukumar na ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauki. ...
Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Similanayi Fubara daga muƙaminsa. Hakan na ƙunshe cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai cike da ƙorafi da majalisar ta fitar, inda take shirin tsige Gwamnan tare da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu. Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine Madalla da hutu ga ’yan makaranta domin azumi A cikin wasiƙar wadda take kafa hujja ta tanadin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya yi, ’yan majalisar sun zargin Gwamna Fubara da kashe kuɗaɗen jama’a ba bisa ƙa’ida ba. Haka kuma, wasiƙar ta ce Gwamna Fubara ya hana majalisar gudanar da aikinta, da kuma naɗa mutane a muƙaman gwamnati ba tare da tantancewa ba. Kazalika, tana tuhumar Gwamnan da ƙin biyan albashi da wasu alawus...
Kwamandan sojojin kasa na JMI Laftanar-Janar Kiyomars Haydari ya bada sanarwan cewa; A bisa umranin jagoran juyin musulunci Imam Sayyid Ali Khamnei , sojojin kasa na JMI suna cikin shirin ko ta kwana domin mayar da martani akan kowace irin barazana ga tsaron kasar. Laftanar janar Haidari ya kuma ce: A halin yanzu da akwai rundunoni 11 da su ke cikin shiri a kan iyakoki kasar domin sanya idanu da tattara bayanai saboda tabbatar da tsaron kasar. Kwamandan sojan kasa na Iran ya kuma ce; Saboda sojojin suna cikin shirin ko-ta-kwana ne, barazanar da ake fuskanta ta zagwanye, da hakan ya ke a matsayin kandagarko. Har’ila yau Laftanar janar Haidari ya yi ishara da rawar dajin da sojojin kasa su...
Bangaren soja na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ya ce a shirye yake kan komi ma, kuma zai ci gaba da kasancewa cikin “kyakyawan shiri”, yana mai jaddada cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake yaki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ba zai sa a sako Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su ba. Abu Ubaida, kakakin kungiyar al-Qassam Brigades, ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a faifan bidiyo a ranar Alhamis, yana mai jaddada cewa, abin da ‘yan mamaya suka kasa cimma ta hanyar “makamai da yaki” ba za a taba samun shi ba ta hanyar “barazana da yaudara ba.” Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan da shugaban Amurka...
Shugaban ma’aikatan Tsaron kasar Amurka ko Pentagon Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka a shirye take ta shiga yaki da China, bayan da Beijing ta tabbatar da cewa zata tunkari kasar Amurka da dukkan karfinta kan ko ta ina ta fito mana a adawar da take nunawa kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hegseth yana fadar haka a jiya Laraba a lokacinda yake hira da shirin labarai na tashar talabijin ta Foxnews na Amurka. Seketarin tsaron tsaron ya kara da cewa dok wanda yake son zaman lafiya to ya shiryawa yaki. Don haka kasar Amurka, inji Hegseth dole ta tabbatar da tana da sojojin masu karfi da makamai masu inganci don shiriwa ko ta kwana, saboda...
An bude cibiyar tattarawa da yada labarai game da manyan taruka biyu na kasar Sin na shekara-shekara, a otel na Media Center dake birnin Beijing a jiya Alhamis. Za a kaddamar da taro karo na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 ne a ranar 5 ga watan Maris, yayin da za a bude taro na 3 na majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 14, a ranar 4 ga watan na Maris. Sama da ‘yan jarida 3,000 ne suka yi rajistar daukar rahotannin tarukan biyu na bana, wanda zai kawo karshen wa’adin tsarin raya kasa karo na 14 da wa’adinsa ya fara daga shekarar 2021 zuwa 2025. Daga cikin ‘yan jaridar, sama da...
Bayan shekaru 47, Faransa ta janye daga sansanin sojinta mafi girma a kasar Ivory Coast A hukumance Faransa ta mayarwa kasar Ivory Coast babban sansanin soji da ta mamaye kusan shekaru hamsin a kusa da birnin Abidjan, a wani bangare na yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla. Filin tashar jiragen ruwa na Port Bouet, wanda ke dauke da bataliyar sojoji na 43 da na ruwa, ya shaida bikin mika ta, inda aka daga tutar Ivory Coast a farfajiyar sansanin, kuma an canza sunan ta da sunan babban hafsan soji na farko a Ivory Coast, Thomas Dakine Ouattara, wanda hakan ya kawo karshen kasancewar Faransa a kasar tun shekarar 1978. Ministan tsaron kasar Ivory Coast, Tene Berahima Ouattara, ya jaddada cewa:...
Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran. Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin. Bangarorin sun bayyana kyakyawan fatan musayar bayanai da shirye shirye a tsakaninsu da nufin karya laggon kafofin yada labarai na kasashen yamma dake yada gurbatattun bayanai da rahotanni kan kasashen. jakadan na NIjar, ya kuma yi tinu da irin kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.
Shugaban kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Son Shiga Yaki Amma Tana Shirye Wajen Fuskantar Barazana
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin lamba, yana mai jaddada cewa; Kasarsa ba ta neman yaki da wata kasa, sai dai tana kokarin karfafa dangantakar abokantaka da kasashen makwabta. Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai lardin Bushahar inda ya gana da al’umma tare da jinjinawa sadaukarwar shahidai musamman shahidan wannan lardin, a daidai lokacin da ake cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci,...
Sojojin Sudan suna kokarin canza ma’aunin yaƙin kasar bayan da suka sun tunkari birnin Khartoum fadar mulkin kasar domin yantar da shi gaba daya Babban birnin kasar Sudan, Khartoum, shi ne tushen rikicin kasar da a halin yanzu aka shafe makonni ana gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan dakarun kai daukin gaggawa, amma fadan ya kara kamari a ‘yan kwanakin da suka gabata. Sojoji suna kara ci gaba da tunkarar babban birnin kasar bayan fitattun sojojin kasar da suka hada da sojoji da mayaka masu goyon bayan sojoji da hukumar leken asiri da dakarun tsaron Sudan da suke sansanin Haddab da ke bangaren arewa maso gabashin yankin Gabashin Nilu a arewa maso gabashin Khartoum suka doshi birnin na Khartoum da...
Mahukunta gidan Radiyon tarayya na kaduna sun kai wa iyalan Alhaji Bala Albabello ta”aziya wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar litini 3 ga watan fabrairu na shekarar 2025. Shugaban gidan Radion, Malam Buhari Awwalu ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan marigayin dake Tudun Jukun a zaria. Malam Buhari Awwalu ya jajantawa iyalan marigayin,inda ya yi addu’ar Allah ya bai iyalan hakurin rashin sa,kuma ya sa a rinka tunawa da kyawawan dabi’un sa na taimakawa marasa karfi da kuma Dora al’umma akan turbar kasuwanci. Ya kuma roki Allah da ya sanya shi a aljannar firdausi. Da ya ke jawabi a masadin iyalan,Alhaji Hassan Abdulwahab ya yi bayanin cewa marigayi Albabello ya sadaukar da rayuwar sa ce wajen hidimtawa al’umma. Cikin...
Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa A Shirye Take Ta Fara Tattaunawa, Marhala Ta Biyu Na Tsagaita Wuta A Gaza
Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, wani jami’in kungiyar wanda baya son a bayyana sunansa ya ce kungiyar a shirye take a fara tattaunawar.. A wannan tattaunawa dai ana saran za’a fayyace filla-filla kan yadda al-amura zasu kasance a nan gaba a zirin gaza. Labarin ya kara da cewa jami’an Hamas sun bayyana haka ne a ranar da aka yi musayar fursinoni da HKI a garin Khan Yunus....
Ya kara da cewa, “a halin yanzu ,ana gudanar da aikin shimfida tagwayen hanyoyi a cikin tsakiyar garin Argungu da sauran wasu ayyukan ci gaba a masarautar. Saboda haka, wannan wata dama ce na kara shirye-shirye don tarbar baki da ke zuwa kallon shirin daga cikin gida da ketare. Wannan al’ada ce fitacciya a masarautar Argungu. “Muna godiya da fahimta da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, da mahalarta wannan biki,” in ji Mataimakin Gwamnan jihar Kebbl Sanata Abubakar Umar Tafida.
Shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na shekarar 2025 sun gabatar da wata “liyafar al’adu” mai kyau da ban sha’awa, kuma mai fasahohi ga masu kallo na gida da waje, bisa sabbin dabaru. Ya zuwa karfe 2 na sanyin safiyar yau Laraba, a dukkan kafafen yada labarai, yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG ya kai sau biliyan 16.8, wanda ya karu da kashi 18.31 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Bugu da kari, yawan masu kallon shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na 2025 ta hanyar talabijin yayin da aka watsa shi kai tsaye a cikin kasar, ya kai kashi 78.88 cikin dari, wanda ya kafa sabon tarihi a cikin...
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya fitar da jerin shirye-shiryen shagalin murnar bikin bazara na bana a yau Talata. Shagalin na bana zai kunshi nau’o’in shirye-shirye daban-daban, kamar wake-wake da raye-raye da wasannin kokawa na gargajiya da na siddabaru da sauransu, domin murnar zuwan sabuwar shekarar gargajiya ta Sin tare da masu kallo dake fadin duniya. A lokaci guda, wasu kafafen yada labarai 2,900 a kasashe da yankuna sama da 200 dake fadin duniya, za su kama tashoshin talabijin na CGTN na kasar Sin na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Rashanci da sauran dandamali dake amfani da harsunan waje har 82, wajen watsawa tare da bayar da rahotannin shagalin bikin bazara na bana....