Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL
Published: 10th, November 2025 GMT
Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar.
Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani.
Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin GamuwarsuA cewar sanarwar NPFL, an ci tarar Katsina United Naira miliyan ɗaya bisa laifuka uku: jefa abubuwa cikin fili, rashin tsawatarwa magoya baya, da haddasa hargitsi a wasa. Haka kuma, ƙungiyar za ta biya Naira miliyan biyu saboda gazawa wajen samar da isasshen tsaro, tare da ɗaukar nauyin gyaran motocin Barau FC da aka lalata.
Jimillar tarar da Katsina United za ta biya ta kai Naira miliyan tara (₦9m), tare da umarni daga NPFL cewa duk sauran wasanninta na gida a kakar bana za ta buga su a garin Jos, jihar Filato. Hukumar ta kuma bai wa ƙungiyar awa 48 ta ɗaukaka ƙara idan bata gamsu da hukuncin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Babban Matsalar Jin Kai A Falasdinu, Inda Falasdinawa Miliyan 1.5 Suke Cikin Halin Musiba Da Bala’i
Bala’in jin kai da ke tafe: Falasdinawa miliyan 1.5 ba tare da tanti ko iskar gas ba
Babban Darakta na Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Gaza, Dr. Ismail al-Thawabta, ya yi gargadin game da wani bala’i na jin kai da ke tafe yayin da hunturu ke gabatowa, ganin yadda Isra’ila ke ci gaba da hana shigar da tanti, tarpaulins, da iskar gas zuwa yankin Gaza, duk da yawan lalata gidaje da matsugunan fararen hula.
A cikin sanarwar manema labarai da Cibiyar Ba da Bayani ta Falasdinawa ta ruwaito, al-Thawabta ya bayyana cewa wannan haramcin ya kara ta’azzara wahalhalun da mutane sama da miliyan 1.5 da suka rasa matsugunansu ke fuskanta a fili ko a cikin tantuna da suka lalace wadanda ba su da kariya daga sanyi ko ruwan sama. Ya jaddada cewa hana shigar da kayan mafaka, mai, da iskar gas ta girki ya zama babban laifi wanda ya karya mafi mahimmancin haƙƙin ɗan adam kuma ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da Yarjejeniyar Geneva, waɗanda suka tilasta wa matsugunan ikon samar da buƙatun fararen hula.
Ya nuna cewa waɗannan matakan sun faɗi cikin manufar hukunta jama’a da mamayar ke yi wa mazauna yankin Gaza kuma suna wakiltar ci gaba da abin da ya bayyana a matsayin “yaƙin yunwa, korar jama’a, da kuma kisan gilla a hankali” da ake yi wa al’ummar Falasdinawa tun farkon harin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya November 7, 2025 Karuwar Matsalar Jin Kai Mafi Girma A Duniya A Sudan Saboda Ci Gaba Da Masifar Yaki A Kasar November 7, 2025 An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas November 7, 2025 Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar November 7, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jinin Isra’ila . November 7, 2025 Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne November 7, 2025 Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar November 7, 2025 Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani November 6, 2025 Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu November 6, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci