Aminiya:
2025-11-12@06:46:00 GMT

Yadda muka daƙile yunƙurin tsige Akpabio daga shugabancin Majalisa – Orji Kalu

Published: 12th, November 2025 GMT

Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana yadda wasu yan majalisa suka haɗa kai suka daƙile yunkurin tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a Majalisar Tarayya da ke Abuja, Sanata Kalu ya tabbatar da cewa akwai yunkuri daga wasu ’yan majalisa na tsige Akpabio daga mukaminsa, wanda bai yi nasara ba.

Babu wani gwamna da zai yi ƙorafin ƙarancin kuɗi a mulkin Tinubu — Sanwo Olu Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe

Kalu wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Abia ne ya ce, “Kodayake an yi yunkuri, amma ba mu bari hakan ta faru ba. Shi ya sa kullum nake cewa mu ’yan gida daya ne, kuma hakan ba zai faru ba,” in ji shi.

Ya jaddada cewa Majalisar Dattawa na da hadin kai kuma tana mayar da hankali kan aikinta na doka, musamman wajen tallafa wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin fuskantar kalubalen tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta.

‘Soludo zai iya komawa APC’

Dangane da ci gaban siyasa a Kudu Maso Gabas, Kalu ya nuna yiwuwar Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, zai sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

A yayin da yake amsa tambaya kan makomar siyasar Soludo, Kalu ya ce: “Ina ganin bayan shari’o’in da ke gabansa, Soludo mutum ne mai ra’ayin cigaba kamar ni, Shugaba Tinubu, da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da kuma gwamnonin APC na Imo, Ebonyi, Enugu da sauransu. Don haka Soludo mutum ne mai ra’ayin ci gaba.”

“Ba na ganin wani abu ne da ba daidai ba idan ya shigo APC. A gaskiya, an tabbatar da cewa zai shiga jam’iyyar. Babu wani zabi da ya fi dacewa da shi face ya zo mu hada kai.”

Kalu ya kuma bayar da tabbacin cewa Shugaba Tinubu zai samu wa’adi na biyu, yana mai cewa a halin yanzu babu wata gagarumar adawa da ke kalubalantar shi.

“Shin akwai wani da ke fafatawa da shi? Zaben nan Tinubu ne da Tinubu, kamar yadda Soludo ya fafata da kansa a zaben Abia.”

“Shugaban kasa ba shi da adawa. Jam’iyyarmu tana da karfi a kasa kuma muna tare da jama’a. Babu wanda zai ce ba mu da jama’a. Za mu ci gaba da yin iya kokarinmu domin ganin talakawan Najeriya sun samu ci gaba,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da niyyar haɗa kai da hukumar wajen inganta jin daɗin ‘yan sanda da kyautata yanayin ayyukansu.

 

Ya ce, “Gwamnatina na ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa an kula da walwala da jin daɗin ‘yan sanda. Wannan ne dalilin da ya sa muke gyaran hedikwatar ‘yan sanda ta Zamfara a halin yanzu.

 

“Haka kuma, muna gina wasu muhimman gine-gine a hedikwatar rundunar ‘yan sanda na Moble. Mun samu nasarori da dama a wajen, kuma muna da ƙarin shirye-shirye na gaba.

 

“Na ji daɗin yadda sakataren hukumar ya ambaci batun ginin sabon unguwar ma’aikatan ‘yan sanda. Idan ka duba halin da barikin ‘yan sanda ke ciki yanzu, za ka fahimci cewa abin ya fi ƙarfin misali.”

 

Gwamna Lawal ya ƙara da cewa, yana daga cikin kwamitin shugaban kasa kan sauya fasalin ‘yan sanda, inda ya bayyana yadda suka ziyarci makarantu da cibiyoyin horas da jami’an ‘yan sanda a jihohi daban-daban.

 

“Abin takaici ne yadda muke sa ran ‘yan sanda za su yi ayyuka masu girma, alhali suna fama da mummunan yanayin rayuwa. Ina daga cikin masu fafutukar ganin an sake fasalin tsarin walwala da albashin ‘yan sanda gaba ɗaya. Wannan dai lokaci ne kawai.”

 

Ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta bayar da ƙasa domin gina sabon gidajen ‘yan sanda, yana mai cewa, “Ina farin ciki da kasancewar kwamishinan gidaje a nan tare da mu. Ya zama dole mu fara aiki da gaggawa wajen tantance filin da za a miƙa wa hukumar domin fara aikin.”

 

Tun da farko, Sakataren Zartarwa na Hukumar Tallafa wa ‘Yan Sanda, Mohammed F. Sheidu, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa haɗin kai da goyon baya da yake bai wa rundunar, musamman a bangaren walwala da gine-gine a Zamfara.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa November 11, 2025 Manyan Labarai Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina November 11, 2025 Ra'ayi Riga CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin  November 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babu wani gwamna da zai yi ƙorafin ƙarancin kuɗi a mulkin Tinubu — Sanwo Olu
  • Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal
  • An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba
  • Larijani : ‘babu wani sabon sako’ da muka aika wa Amurka
  • ’Yan ta’adda na kafa doka da karɓar haraji a Arewa — Dambazau
  • Wani mutum ya rasu a gidan karuwai bayan ziyartar ’yan mata
  • Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC
  • Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa
  • NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna