Aminiya:
2025-11-16@12:16:25 GMT

Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang

Published: 16th, November 2025 GMT

Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato, ya ce ba da yawunsa jam’iyyarsu ta PDP ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike ba.

Yayin da yake nisanta kansa daga matakin da PDP ta ɗauka na korar Wike daga jam’iyyar, ya yi gargaɗin cewa hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa

A jiya Asabar ce jam’iyyar ta kori ministan, wanda ya daɗe yana rigima da shugabancin jam’iyyar, da sakatarenta na ƙasa Samuel Anyanwu, da tsohon Gwamnan Ekiti Ayo Fayose yayin babban taronta na ƙasa tana mai zargin su da yi mata zagon ƙasa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Muftwang ya ce majalisar gwamnonin PDP da kwamatin zartarwa ba su tattauna batun ba kafin a bijiro da shi yayin taron.

Ya ƙara da cewa “korar jiga-jigan jam’iyyar a wannan lokaci mai muhimmanci ba shawara ce mai kyau ba wajen shawo kan rikicin da ya dabaibaye PDP.”

Kalaman Muftwang na zuwa ne jim kaɗan bayan Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri shi ma ya ce bai goyi bayan korar Ministan Abujan da abokan siyasarsa ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Caleb Muftwang Jihar Filato

এছাড়াও পড়ুন:

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

Sarki Sanusi II, ya yaba da ci gaban da jami’ar ke samu tare da farin ciki kan yawan mata da suka kammala karatu, yana fatan hakan zai ƙara yawan rawar da mata ke takawa a mulki da sauran ɓangarorin rayuwa.

Tun da farko, Shugaban Jami’ar, Farfesa Ajith Kumar, ya bayyana cewa cikin ɗalibai 180 da suka kammala karatun 24 sun samu sakamako daraja ta ɗaya (First Class), tare da bayyana cewa wannan bikin yaye ɗaliban shi ne karo na farko da jami’ar ta raba digiri na biyu tun bayan amincewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), da ta samu.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama November 15, 2025 Siyasa Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa November 15, 2025 Manyan Labarai Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola November 15, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa
  • Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP
  • Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7
  • PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu
  • Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso
  • Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa
  • Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa
  • Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP
  • Ina girmama sojojin Nijeriya — Wike