Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta
Published: 14th, November 2025 GMT
Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Sun Weidong ya gana da jakadan Japan a Sin Kishi Nobuo bisa umurnin gwamnatin kasar a jiya Alhamis, inda ya yi tsokaci a hukumance kan kalaman da firaministar Japan Takaichi Sanae ta yi game da kasar Sin.
Sun ya ce, batun Taiwan na da matukar muhimmanci cikin muradun Sin, kuma ba za a iya tauye shi ba.
Ya kara da cewa, a shekaru 80 da suka gabata, jaruman jama’ar Sin sun yi yaki na tsawon shekaru 14 domin nuna turjiya ga maharan Japan. A yau, duk wanda ya yi yunkurin katsalandan a harkokin dunkulewar Sin, ko shakka babu Sin za ta mayar da martani mai tsanani!
ADVERTISEMENTSun ya kuma bukaci Japan da ta yi tunani mai zurfi game da laifuffukanta na tarihi, ta daidaita kura-kuranta, kuma ta janye kalamanta marasa kyau, kuma ta dakatar da tafiya a kan hanyar da ba ta dace ba. In ba haka ba, Japan za ta dauki alhakin duk wani sakamako da ya biyo baya, kuma tabbas kaikayi zai koma kan mashekiya! (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Kara Azamar Kirkiro Da Fasahar Sadarwar 6G
Kasar Sin ta kara azamar kirkiro da fasahar sadarwa mai karfin 6G a cikin ’yan shekarun nan, inda ta samu ci gaba a bangaren binciken fasalin tsarin fasahar ta 6G da kuma zayyanar hanyar sadarwarta, kamar yadda ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani ta kasar ta bayyana a jiya Alhamis.
A yayin gudanar da taron bunkasa fasahar 6G na shekarar 2025, mataimakin ministan masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani na kasar Sin Zhang Yunming ya bayyana cewa, yanzu haka kasar tana da muhimman fasahohi na kirkiro da fasahar sadarwar 6G sama da 300.
Zhang ya kara da cewa, kasar ta hada kan kamfanoni sama da 100 na cikin gida da na waje a fannin tsarin masana’antu, kuma ta gayyaci kamfanonin duniya su zo su shiga cikin gwajin da ake yi na fasahar 6G.
ADVERTISEMENTZhang ya yi nuni da cewa, a wannan shekarar an fara gudanar da cikakken bincike kan tabbatar da ingancin fasahar 6G, inda ya kara da cewa yanzu haka aikin kirkiro da fasahar 6G yana kan wani muhimmin mataki wanda ke bukatar hikima da kuma cimma matsaya guda. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA