Aminiya:
2025-12-13@13:12:14 GMT

Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo

Published: 12th, November 2025 GMT

Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.

Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko biyu masu zuwa.

Troost-Ekong ya gargaɗi Super Eagles kan wasan da za ta fafata da Gabon Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro

“Eh, tabbas wannan shi ne Kofin Duniya na ƙarshe da zan halarta. Zan kai shekara 41, kuma ina ganin wannan ne lokacin da ya dace na ajiye takalmi,” in ji shi a wata tattanawa a Saudiyya.

Ronaldo, wanda yanzu ke bugawa kulob ɗin Al-Nassr ta Saudiyya, ya ce yana fatan cimma burin zura ƙwallo 1,000 kafin ya yi ritaya gaba ɗaya daga tamaula.

Tsohon ɗan wasan Manchester United, Real Madrid da Juventus, shi ne kan gaba a tarihin cin ƙwallo a matakin ƙasa, inda ya zura ƙwallo 143 a tawagar Portugal.

Ronaldo ya fara buga Kofin Duniya a shekarar 2006, lokacin da Portugal ta kai matakin kusa da na ƙarshe amma ta sha kashi a hannun Faransa.

A halin yanzu, zaƙaƙurin ɗan wasan bai taɓa lashe Kofin Duniya ba, sai dai ya taimaka wa ƙasarsa ta lashe Gasar Euro ta 2016 da kuma UEFA Nations League har sau biyu.

Yanzu haka, tawagar da Roberto Martínez ke jagoranta tana daf da samun gurbin shiga gasar ta 2026 da za a gudanar a Amurka, Kanada da Mexico, idan ta doke Jamhuriyar Ireland ranar Alhamis.

Ronaldo wanda ya zama ɗan wasan farko da ya ci ƙwallo mafi yawa a tarihin cancantar Kofin Duniya da ƙwallo 41 ya ce ritayarsa ba za ta zama abu mai sauƙi ba.

“Zai yi wuya sosai. Zan iya kuka ma, domin ni mutum ne mai buɗaɗɗiyar zuciya. Amma lokaci ya kusa,” in ji shi a wata hira da ya yi a shirin Piers Morgan Uncensored.

Ronaldo ya koma Saudiyya daga Manchester United a ƙarshen shekarar 2022, inda rahotanni suka nuna yana samun kusan euro miliyan 200 duk shekara.

A watan da ya gabata, mujallar Forbes ta bayyana shi a matsayin ɗan wasan da ya fi kowa samun kuɗi a duniya, yayin da jaridar Bloomberg ta tabbatar da cewa ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa na farko da ya zama biloniya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gasar Kofin Duniya Kofin Duniya

এছাড়াও পড়ুন:

Farfesa na Farko a fannin Ilimi a Arewa, Adamu Baikie, ya rasu yana da shekara 94

Allah Ya yi wa Farfesa Adamu Baikie, wanda ya kasance Farfesa na farko a fannin Ilimi daga Arewacin Najeriya, rasuwa.

Farfesa Adamu Bakie ya rasu yana da shekaru 94 ne a daren Jumma’a a gidansa da ke Zariya, Jihar Kaduna.

Babban ɗansa, Manjo Muhammad Adamu (Ritaya), ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a sanar da jama’a cikakkun bayanai da lokacin da za a gudanar da jana’izarsa daga baya.

Baikie ya shahara sosai wajen gina fannin ilimi a Najeriya, inda ya yi aiki a manyan makarantu da dama.

Kotu ta sa ranar yanke hukunci a Shari’ar Abba Kyari da NDLEA Gwamnatin Kano ta haramta kafa hukumar Hisbah mai zaman kanta

Ya taɓa zama Shugaban Jami’a a wasu jami’o’in Najeriya, kuma ya jagoranci wata jami’a a Kudancin Afirka a lokacin aikinsa.

An haifi Farfesa Adamu Baikie ne a Wusasa, Zariya a 1931 saidai ya girma ne Sabon garin Kano, inda ya yi karatun firamare kafin daga baya ya dawo makarantar middle a Zaria a shekarar 1948.

Ya zama farfesa na farko a ɓangaren ilmi daga Arewacin Najeriya a 1971.

Ana kallon da a matsayin jigo wajen kafa tsare-tsaren koyar da malamai, tare da samar da gudummawar da ta ɗore a bangaren ilimi na Najeriya.

Ya rasu ya bar ’ya’ya biyar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Farfesa na Farko a fannin Ilimi a Arewa, Adamu Baikie, ya rasu yana da shekara 94
  • 2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe
  • Majalisar Dinkin Duniya Za ta Yi Zama Da Bangarorin Da ke Yaki A Sudan
  • Osimhen Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa Na Bana A Kasar Turkiyya
  • Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci
  • Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya
  • Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 
  • Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025
  • Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago
  • Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro