2025-11-01@12:43:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 952
«Gwarzuwar Hukumar»:
Dan wasan da ya lashe kyautar a bara, Ademola Lookman na Nijeriya ba ya cikin jerin ‘yan wasan da aka lissafo a bana, inda hukumar kwallon kafa ta Afirka (Caf) ta samar da kwamitin kwararru wanda ya zakulo masu horarwa da ‘yan wasan da suka “Taka rawar gani” a tsakanin 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Oktoban wannan shekara. An bayyana sunan mai horar da tawagar ‘yan kwallon kafa ta kasar Cape Berde, Bubista a matsayin mai neman lashe kyautar mai horarwa mafi kwazo bayan jagorantar tawagar kasar ta Blue Sharks wajen samnun gurbin gasar kofin duniya a karon farko a tarihi. Haka nan tawagar ta tsibirin Cape Berde na cikin masu gogayyar lashe kungiya mafi hazaka a...
3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe. “Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano October 31, 2025 Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Daga Usman Muhammad Zaria Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma. Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade. Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su. Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin noma daban daban. A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya...
Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin kariya a harkokin sufurin ruwa, inda ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi, da shugabannin al’umma, da direbobin kwale-kwale da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da sauran wadanda suka dace su kara kaimi wajen ganin ana kiyaye duk ka’idojin kariya don magance sake afkuwar ibtila’in a nan gaba. Ya umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da Majalisar. Karamar Hukumar Nafada su bayar da duk wani tallafin da ya dace ga iyalan da abin ya shafa tare da hada hannu da hukumomin da abin ya shafa don inganta tsaro da wayar da kan al’ummomin da ke yankunan kogi. Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’a yana mai cewa “A madadin...
Madagascar ta sanar da kafa sabuwar gwamnati wadda ta kunshi fitattun ‘yan adawa guda uku a manyan mukamai na ministoci. An gabatar da majalisar ministoci mai mambobi 29, wacce ta kunshi mata 10, a wani biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Yavoloha da ke babban birnin kasar, Antananarivo. Shugaban rikon kwarya Michael Randrianireina ya bayyana a lokacin bikin cewa manyan abubuwan da sabuwar gwamnatin ta sa gaba sun hada da yaki da rashin adalci, aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu, da kuma samar da yanayin kasuwanci mai dorewa. Ya kara da cewa kowane minista dole ne ya samar da sakamako mai kyau cikin watanni biyu, yana mai gargadin cewa rashin yin hakan a cikin wannan lokacin zai zama gazawa...
Shugaban karamar hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho, ya yi gargaɗi ga mazauna yankin kan mummunan ɗabi’ar shan magani ba tare da shawarar likita ba, yana mai bayyana hakan a matsayin babban haɗari ga lafiya da ka iya janyo matsalolin da ke barazana ga rai. Dr. Tsoho ya yi wannan gargaɗi ne yayin da yake ziyarar duba asibitin Gwarzo General Hospital, inda ya gana da marasa lafiya, ya duba yadda ake gudanar da ayyuka, tare da yabawa ma’aikatan lafiya bisa jajircewarsu wajen kula da jama’a. Ya nuna damuwa cewa, yawancin matsalolin lafiya da ake fuskanta a cikin al’umma na faruwa ne sakamakon amfani ko wuce gona da iri wajen shan magunguna ba tare da shawarwarin ƙwararru ba. Ya shawarci jama’a da...
Killace Gaza da gwamnatin mamayar Isra’ila take ci gaba da yi tun bayan tsagaita bude wuta ya yi sanadiyyar mutuwar masara lafiya 1000 a yankin Majiyoyin lafiya na Falasdinawa sun tabbatar a yau Alhamis, 30 ga watan Oktoban shekara ta 2025 cewa: Tun bayan tsagaita bude wuta, gwamnatin mamayar Isra’ila ta hana shigar da kayan aikin likita da kayayyakin bukatu cikin Gaza, yayin da marasa lafiya dubu suka mutu sakamakon tsauraran matakan tsaro da kuma rufe hanyoyin shiga cikin yankin. Majiyoyin sun bayyana cewa kashi 10% ne kawai na bukatun lafiya suka shiga yankin Gaza, kuma babu na’urorin MRI masu aiki a yankin Gaza. Dr. Muhammad Abu Salmiya, Darakta Janar na Al-Shifa Medical Complex, ya bayyana cewa tun bayan karshen...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki October 29, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest October 29, 2025 Daga Birnin Sin An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin October 29, 2025
Zhai Kun, mataimakin shugaban kungiyar nazarin yankin kudu maso gabashin Asiya na Sin, kuma farfesa a jami’ar Peking, ya bayyana cewa, tun daga sigar 1.0 zuwa 2.0 har zuwa 3.0, an samu ci gaba mai zurfi ta hanyar sabbin ka’idoji na fasahar zamani da kare muhalli, da sabunta tsarin amince da ka’idojin juna, da kara karfin hadin gwiwar samar da kayayyaki, inda ya inganta yankin ciniki daga matsayin “kara adadi” zuwa “ingantacciyar bunkasa”. A yayin da ra’ayin bangaranci da babakere ke takura tsarin hadin gwiwa na duniya, wannan sabon tsarin ya samar da wata hanya iri ta Asiya don kiyaye tattalin arzikin duniya mai bude kofa. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Tataunawa...
An sanya dokar hana zirga-zirgar jama’a a Dar es Salaam, babban birnin Tanzania, bayan da ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsarin gudanar da zaɓen ƙasar. Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun riƙa yaga hotunan Shugaba Samia Suluhu Hassan tare da ƙona wani ofishin ’yan sanda, yayin da suke zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya na fifita jam’iyya mai mulki, tare da neman gwamnati ta gyara tsarin zaɓe da kuma ba kowa damar faɗar albarkacin baki. Gwamnati ta bai wa ASUU N2.3bn domin biyan bashin albashin malamai Sassauci na yi wa Maryam Sanda ba afuwa ba — Tinubu Zanga-zangar dai ta ɓarke ne yayin da ake tattara sakamako bayan kammala kaɗa ƙuri’a a zaɓen na...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC October 29, 2025 Labarai COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa October 29, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci October 29, 2025
Kakakin ma’aikatar kula da muhalli ta kasar Sin Pei Xiaofei ya bayyana a yau cewa, yanayin ruwa da na iska a kasar ya ci gaba da ingantuwa a cikin watanni 9 na farkon bana. A cewarsa, matsakaicin nauyin burbushin abubuwan dake cikin iska na PM2.5, wanda shi ne muhimmin ma’aunin gurbatar iska, ya tsaya kan microgram 26 kan kowane cubic mita, a cikin birane ko garuruwan Sin 339, daga watan Janairu zuwa na Satumba, wannan ya nuna cewa an samu raguwar ma’aunin da kaso 5.1 kan mizanin shekara-shekara. Haka kuma, cikin watanni 9 na farkon bana, an samu ingantacciyar iska a kaso 87.6 na kwanakin, wanda ya karu da maki kaso 1.8 kan na bara. Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa...
Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan.
Rahotanni sun bayyana cewa cewa kasar Pakistan ta bayyana cewa za ta dauki mataken da suka dace wajen kare tsaron alummarta da kasarta bayan kawo karshen yajejeniyar dakatar da bude wata ta kwanaki 4 tsakaninsu da kasar Afghanistan ba tare da wani ci gaba da aka samu ba, Yarjejeniyar ta waste ne kwana daya kafin cikarta bayan wani mummunan fada da aka tsakanin kasashen biyu da ya jawo dama suka mutu ciki har da fararen hula, Pakistan na zargin Afghanisatan da boye kungiyoyin yan ta’adda dake kai hare-haren ketare iyaka, sai da Kabul ta musanta wannan zargin kuma ta dage akan ikonta, A karshen mako ne minsitan tsaron Pakistan Khawaja Asif ya yi barazanar barkewar yaki tsakani, idan dai mataken...
Ƴan sanda a kasar Tanzania sun saka dokar hana zirga-zirga a fadin kasar bayan zanga-zangar da ta barke yayin zaben shugaban kasa da ya rikide ya koma tashin hankali a wasu sassa daban-daban na kasar. Rahotanni sun nuna cewa, zanga-zangar ta barke ne musamman a birnin Dar es Salaam da wasu garuruwa yayin da jama’a ke nuna rashin jin daɗi kan yadda ake gudanar da zaben shugaban kasar. Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya a tsarin zaben, kuma sun nemi gwamnati ta gyara tsarin zabe da kuma ba kowa damar fadin albarkacin baki. A cewar jami’an tsaro, an sanya dokar ne domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Sai dai wasu kungiyoyin kare hakkin dan...
Shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na kasar Turkiya Rajab dayyib ardogan da ma alummar kasar na farincikin zagayowar ranar da kasar ta samu yancin kai, kuma ya jaddada muhimmancin kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Iran da Turkiya suna da alaka mai zurfa ta tarihi aladu da kuma dabarun yaki, a daidai lokacin da ake samun sauyi a yankin , akwai bukatar kasashen biyu sun kara hadin guiwa a fannonin kasuwanci tsaro da kuma diplomasiya, sakon na pezeshkiyan ya nuna aniyar iranta fifita yin hulda tsakanin kasashen biyu Akwai abubuwa da dama da suka yi kama da juna tsakanin kasashen biyu masu abokantaka da yan uwantaka, pezeshekiyan, ya kara da cewa ta...
Don haka, an mayar da hukuncin kisa na Maryam Sanda zuwa shekaru 12 a gidan yari, wanda hakan ya nuna tana da kasa da shekaru shida na zama a gidan gyaran halin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October 29, 2025 Manyan Labarai Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II October 29, 2025
Shugaba Bola Tinubu, ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu laifukan da suka haɗa da kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu. Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa saboda zargin kashe mijinta, ba ta cikin sabon jerin sunayen wadanda aka yafe wa laifi. Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar a ranar Laraba cewa an cire sunayen mutane kimanin 50 daga tsohon jerin bayan ce-ce-ku-ce daga jama’a. “Bayan duba martanin jama’a, Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunayen wadanda aka samu da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun kwayoyi, da fataucin mutane daga jerin wadanda aka bai wa afuwa,” in ji Onanuga. Ya kara da cewa an dauki wannan...
Rikici tsakanin bangarori biyu a garin Donga na Jihar Taraba, ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a kan limancin masallacin Juma’a na garin. Bayanai sun nuna baya ga mutanen da suka mutu, wasu da dama sun jikkata kuma an lalata dukiyoyi. An ceto jaririya ’yar mako daya da haihuwa da aka sayar a Anambra An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna Rikicin, kamar yadda Aminiya ta gano, ya faru ne a ranar Talata kan limancin masallacin Juma’a na garin da ke gaban fadar Sarkin Donga. Wata majiya daga garin ta shaida wa wakilinmu cewa rikicin ya samo asali ne daga sabani tsakanin kungiyoyi biyu na al’ummar Musulmi a garin kan wanda ya kamata ya zama...
Kuri’un na jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin, da jami’ar Renmin ta kasar suka gudanar, karkashin cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani, sun tattaro ra’ayoyin jama’a daga manyan kasashen duniya masu tasowa, da ma na kasashe masu samun saurin ci gaba. (Mai fassara: Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas October 28, 2025 Daga Birnin Sin Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika October 28, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 October 28, 2025
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa duk da jajircewar kungiyar na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da ita, firaministan gwamnatin Isra’ila yana kokarin karya sharuddanta. Hazem Qassem, kakakin kungiyar, ya ce “Mun yi wa masu shiga tsakani bayani kan cikas din da ke hana neman gawarwakin fursunonin Isra’ila kuma mun nemi su samar mana da karin kayan aiki.” Mai magana da yawun Hamas ya kuma bayyana cewa: “Mun sanar da Alkahira game da ayyukan bincike na ‘yan Isra’ila, kuma muna ci gaba da sanar da masu shiga tsakani game da ci gaban binciken. Duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin gwamnatin Tel Aviv da kungiyar Hamas, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare. Na...
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar. Taron ya samu haɗin...
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan kasar. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar. Taron ya samu haɗin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025
A ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1945, wato bayan da kasar Sin ta samu nasara a yakin kin harin mayakan Japan, kasar ta Sin ta karbi yankin Taiwan daga hannun Japanawa da suka yi rabin karni suna mamayar yankin, inda suke aiwatar da mulkin mallaka. Sa’an nan zuwa ranar 25 ga watan Oktoban bana, babban yankin kasar Sin ya gudanar da biki na musamman don tunawa da dawowar yankin Taiwan cikin harabar kasar. Dangane da batun, dimbin kafofin watsa labaru na kasashe daban daban suna ganin cewa, bikin da aka shirya ya nuna nasarar da Sinawa suka samu a yakin duniya na biyu, kana ya shaida cewa, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, wanda ba za a iya...
Gyaran da aka fara ya yi daidai Nambobi suna ba da labarin wani ɓangare na labarin, amma suna bayyana lamarin ne kawai, amma suna bayyana lamarin gaba ɗaya. A shekarar 2023, FIRS ta samu Naira Tiri liyan12.36, abinya zarce kuɗaɗen da ake tsammanin shigowa daga gare ta, har ma wuce kashi 7 na kuɗaɗen shigar da ake sa ran da ake zata kawo, hakan kuma shi yasa mafi kayu ɗin kuɗaɗen shigar da aka samu a tarihin tara kuɗaɗen haraji. A shekarar 2024, an kuɗaɗen shigar suka ƙaru da—Naira Titiliyan 21.7, ba kamar na shekarar 2023 ba , inda aka nsamu Naira Tiriliyan19.7. Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar Gwamnan Bauchi...
Sai dai ya yabawa masu ba da agajin gaggawa, da jami’an tsaro da kuma ‘yan sa-kai da suka yi aiki tuƙuru wajen ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da ba su agaji, yana mai cewa ɗaukin gaggawan da suka kai ya taimaka wajen rage munin ibtila’in. A yayin da take addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa, ƙungiyar Gwamnonin Arewan ta bada tabbacin cewa za ta ci gaba da haɗa hannu da hukumomin tarayya dana jihohin da abin ya shafa don ƙarfafa tsarin rigakafi da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin...
Wannan nasara mai ban mamaki ta sa kungiyar Niger Tornadoes ta koma matsayi na biyu a teburin gasar, inda yanzu take da maki 17 a kasan Nasarawa United. Hakazalika, sakamakon ya bar Kano Pillars a cikin mawuyacin hali a gasar yayin da ta ke matsayi na 19 da maki 8 kacal. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus October 25, 2025
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Gombe, ta bayyana alhini bisa rasuwar Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (mai ritaya). Haka kuma hukumar ta bayyana jimami kan da ɗan sandan da ke tsaron kwamishinan, Sajan Adamu Husaini, da direbansu, wadanda suka rasu a wani mummunan hadarin mota da ya afku ranar Juma’a. Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar, Kwamandan hukumar, Jibrin Idris, ya ce rasuwar babban rashi ce ba ga iyalan mamatan kawai ba, har ma ga Gwamnatin Jihar Gombe da al’ummar...
Aikin, wanda ke wakiltar tashar fitar da ɗanyen fetur ta farko da kamfanin Afirka mai zaman kansa ya bunƙasa a ƙasar, yana nuna babban jarin da ya wuce dala miliyan 400 a matakin farko, inda ake sa ran kuɗin zai ci gaba da bunƙasa har ya haura dala biliyan 1.3. GEIL, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Anthony Olusegun Adegbulugbe, wani sanannen malami kuma ƙwararren masani a fannin tsare-tsaren makamashi, yana da ƙwarewa mai sosai a tsawon shekaru masu yawa. Yana aiki a matsayin shugaban jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Jihar Osun, ya kuma kasance babban mai ba da shawara kan makamashi ga tsohon shugaba ƙasa, Olusegun Obasanjo. Haka kuma ya kasance shugaban shirin “National Gas to Power” na Nijeriya kuma ya...
Yana magana ko jawabi cikin hankali, amma kuma shawarwarin da yake badawa suna da matuƙar amfani wajen kawo gyaran wurare da dama. Mai ilimi, tsara yadda za’a ɓullo ma al’amura, mutunci ga kuma kwarjini da ƙwarewa An haife Kalu 5 ga Mayu, 1971, a Agbamuzu, a ƙaramar hukumar Bende ta Jihar Abia State, tarihin rayuwar Kalu ya fara ne daga aiki da kuma samun tallafin ƙaro ilimi. Yana da digirin digirgir PhD a tsarin al’umma da kuma karatun abinda da wayo ake koyonsa (Jami’ar Abuja), da kuma LL.M akan ta’addanci da taimakawa kan jin ƙai (Distinction, daga Jami’ar Kalaba), da MBA daga Jami’ar Oɗford Brookes (UK), da kuma LL.B (Hons.) daga Kalaba. Ya cigaba da karatu— halin yanzu yana karanta...
Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje, da inganta dogaro da kai a ɓangaren fasaha, da samar da ayyukan yi. NASENI tana ba da ababen more rayuwa da tallafin manufofin, yayin da ɓangaren da ke kula da masana’antu, yana mai da hankali kan haɗin gwiwa, ƙirƙira da kasuwanci don kafa Nijeriya a matsayin cibiyar fasahar Afirka. Wannan dabarar da NASENI ta yi ya tabbatar da cewa ba a bar kasar a baya...
Ana haka ne Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ƙaramar hukumar, inda ya gana da Misis Duaka a cibiyar lafiya da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da sauran ma’aikatan duk sun tashi. Wannan aiki na sadaukarwa, juriya da biyayya ga aikinta, ya sa Gwamna Zulum ya fahimci cewa ta himmatu wajen kula da lafiyar mutanen Mafa, mahaifar sa. Gwamnan dai a wasu ziyarce-ziyarcen da ya kai har sau biyu, ya ware ta, ya kuma yaba wa sadaukarwar da ta yi, tare da yaba mata kan yadda ta tsaya tare da jama’arsa duk kuwa it aba ‘yar asalin yankin ba ne. Kyautar kwazo da rikon amana da ta samu ya zo ne a lokacin da Gwamna Zulum, wanda ya...
Aƙidar Dr Bello abu ne mai saƙin gaske kuma akwai hikima a ciki sosai. Shi ne kuma samar da ingantacciyar kiwon lafiya wand aba wai sai kana da kuɗi mai yawa ba. Tsarinsa shi ne haɗa yi wa mutane aiki, ilimantar da su tared fda kuma tsugunar da su. Wannan mataki ne da yake tabbatar da an samun cikin gaggawa da kuma sauƙin gaske.. Daga Legas zuwa Kano, daga Ondo zuwa Kuros Riba, kungiyar CFDF tana tafiya da kayan aiki na tafi da gidanka da kuma rundunar likitoci masu tiyata na sa kai, masu aikin jinya, da ma’aikatan jinya. Kowace manufa asibiti ce mai motsi – duba marasa lafiya, yin hadaddun tiyata, da bayar da shawarwari da tallafin abinci mai...
“Gudanar da harkokin kuɗaɗe ba bayar da taimako ba ne, haƙƙi ne.” Ƙoƙarin Cike Gibi Tare Da Gina Makoma Mai Kyau Lokacin da OPay ya shiga fannin harkokin kuɗaɗe na zamani a Nijeriya, ƙalubalen ya kasance bayyane suke, kusan rabin yawan mutanen Nijeriya ba su da damar samun shiga harkokin kuɗaɗe. Waɗanda suka kafa kamfanin sun gano cewa yawancin ‘yan Nijeriya sun yin isa da bankuna, tsarin yana haifar da jinkiri, kuma tsarin yana da barazana mai yawa. OPay ta kasance mai sauƙin gudanarwa, wani tsarin kuɗi na wayar hannu da ya dace da rayuwar yau da kullum ba tare da tangarda ba. Daga biyan kuɗi ta walat zuwa biyan kuɗin kayayyakin more rayuwa, daga sayan katin waya zuwa mu’amaloli...
Sauyin shugabannin tsaro dai ya nuna matakin da Tinubu ke ɗauka wajen sake fasalin tsaro, amma kuma ya buɗe sabon babi na tattaunawa kan yadda ake kula da tsofaffin hafsoshin da suka ba ƙasa hidima tsawon shekaru. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 Manyan Labarai Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe October 25, 2025
Babban magatakardar MDD Antonio Gutrress ya bayyana cewa majalisar tana da bukatuwa da a yi kwaskwarima da gyare-gyare. Gutrress dai ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin cika shekaru 80 da kafuwar MDD. Gutrress ya kuma ce, tare da cewa ayyukan da Majalisar take aiwatarsa suna da matukar muhimmanci,amma kuma halarcinta yana tangal-tangal, sannan kuma ya kara da cewa an dade ana sauraron a yi ma ta kwaskwarima. A wani sashe na jawabin nashi, ya zargi wasu daga cikin mambobin MDD da cewa a lokuta da dama suna yin abubuwan da suke cin karo da dokokin majalisar, da hakan yake sa ake yin shakku akan ita kanta majalisar ta dinkin duniya. Har ila yau, Guterres ya ce; Majalisar...
Mahaifin Rukayya, Muhammad Adamu mazaunin ƙauyen Bayan Dutse da ke Wailo, a gundumar Kubi cikin ƙaramar hukumar Ganjuwa a ranar 17 ga watan Oktoba ya kai rahoton caji ofis ɗin Soro ya ke shaida cewar wani matashi mai suna Auwal Dahiru mai shekara 17, ya kai farmaƙi wa yarsa da ƙoƙarin kasheta da kwaƙule mata idanuwanta. Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil a ranar Litinin, ya ce, lokacin da ‘yansanda suka samu rahoton faruwar lamarin cikin gaggawa a ƙarƙashin Baturen ɗansanda da ke kula da caji ofis ɗin Soro, CSP Aliyu Mohammad Goni, sun kai agaji inda lamarin ya faru. A lokacin da aka ɗauki Rukayya zuwa asibitin koyarwa na...
A shekara biyu kaɗai,ya yi ƙoƙarin maida Jihar Kaduna da aka sani da rarrabuwar kai, yanzu ta koma tsintsiya ɗaya sanadiyar hakan. Yin gyara ta hanyar ci gaba Gwamna Sani ya hau kan karagar mulki ne a shekarar 2023 ba a matsayin wanda ya iya lamarin siyasa sosai ba, sai dai mai son kawo agyara. Aikinsa na farko ba siyasar bace —mutane ne yafi maida hankali kansu. Ya fara ƙaddamar da lamarin gaggarumin ci gaban ƙauyuka ta yadda abin ya zama a kowace ƙaramar hukumar akwai aikin da ake yi.Gina hanyoyi, asibitoci, makarantu, kasuwanni an fara gigginasu a ƙananan hukumomi 23 . Cikin ci gaban daya samu sun haɗa da: Haɓaka ƙananan asibitoci 225 inda aka mayar da su matsayi...
Ga Dukkan Alamu Kaikayi Zai Koma Kan Mashekiya Gwamna Biodun Ya Amince Da ₦70,000 Mafi Ƙarancin Albashi Ga Ma’aikatan Ekiti Waɗannan ginshiƙai, an tsara su ne bisa manufofin sanya hannun jari a cikin dukkanin ƙananan hukumomi 16 na jihar. A cikin shekaru uku, manyan ayyuka 577 zuwa 368 aka kammala, sannan kuma 209 da ake kan gudanar da su a halin yanzu, sun shafi garuruwa da ƙauyuka sama da 200, ana kuma ci gaba da haɓaka harkokin ilimi, kiwon lafiya, wutar lantarki, noma da kuma samar da haɗin kai. Ayyukan Da Suka Game Mutane Babu ayyukan da Oyebanji ya yi fiye da na abubuwan more rayuwa. Sabbin hanyoyi kamar Ikere zuwa Igbara zuwa Odo, Ogotun zuwa Ikogosi, Isinbode zuwa Ara...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa matasa dubu ɗaya (1,000) za su samu horo kan tsaron yanar gizo (cyber security) da fasahar binciken dijital (digital forensics) ta hanyar Cibiyoyin Koyon Fasahar Dijital ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) a Jihar Nasarawa. Uwargidan Shugaban Ƙasan ta bayyana haka ne yayin bikin kaddamarwa da miƙa Cibiyar Koyon Fasahar Dijital (Digital Learning Center) a Lafia da wasu jihohin ƙasar. Sanata Oluremi Tinubu ta ce, shirin horon matasan wanda za a rika gudanarwa a kowane mako daga yanzu har zuwa watan Disamba na shekara mai zuwa, yana da nufin yakki da laifukan yanar gizo (cyber crimes) da kuma ƙarfafa matasa su samu ƙwarewa ta yadda za su dogara da kansu a...
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da Dijital E-Learning Library a Gusau, Jihar Zamfara — ɗaya daga cikin jihohi goma da aka zaɓa a faɗin ƙasar domin aiwatar da wannan muhimmin aiki ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da haɗin gwiwar Hukumar bunkasa ayukkan fasaha ta kasa (NITDA). A yayin bikin kaddamarwar, Sanata Tinubu ta bayyana cewa wannan aiki ba wai game da fasaha da kwamfuta kawai ba ne, amma yana nufin ƙarfafa matasa, rage gibin fasaha (digital divide), da kuma buɗe sabbin ƙofofin ilimi da ƙirƙira ga al’ummar Zamfara da ma Najeriya baki ɗaya. Uwargidan Shugaban Ƙasa, wacce Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta wakilta, ta bayyana cewa ilimi shi ne...
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa gobara ta lalata rumfuna 529 daga cikin rumfuna na wucin gadi a Kasuwar Shuwaki da ke ƙaramar hukumar Gari, Jihar Kano. Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Kano. A cewarsa, hukumar ta samu kiran gaggawa misalin ƙarfe 3:25 na rana daga Abdulmalik Muhammad na ofishin kashe gobara na Gari, yana sanar da aukuwar gobara a kasuwar. Ya bayyana cewa, da zarar sun samu bayanin, hukumar ta aika jami’ai da motocin kashe gobara zuwa wurin domin kashe wutar tare da hana ta yaduwa zuwa sauran sassan kasuwar. Saminu ya ce yankin kasuwar yana da fadin kimanin...
Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP Har ila yau, shirin nan nata Mata A Aikin Noma, ya bai wa matan karkara sama da 20,000 tallafi da horarwa da ƙara samun kuɗin shiga ga iyalai da kuma wadatar da al’umma. Kazalika, shirin Tallafin Ilimi, ya samar wa fiye da ɗalibai 3,000, guraben karatu, kwamfiyutoci da kuma jagoranci na gari. Ga tsofaffi kuma, Asusun Tallafa wa Tsofaffi ya bai wa tsofaffi 5,000 alawus-alawus da kula da lafiyarsu tare kuma da maido da martabar musamman waɗanda aka yi watsi da su, aka kuma manta da su. Lokacin da iftila’i ya afku a Jihohin Filato da Benuwe a tsakiyar 2025,...
Baya ga haka, sabon ginin ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Jihar Zamfara da aka sake ginawa da kuma sabon ginin kwalejin fasaha da kimiyya na Jihar Zamfara (ZACAS) da aka gyara, sun yi matuƙar haskaka Gwamnatin Dauda Lawal. Har ila yau, jihar ta samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar zuba jari, wajen gyarawa da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a faɗin jihar. A ƙoƙarinsa na rage mace-macen mata masu juna biyu da mace-macen jarirai, an ɗauki ma’aikatan kiwon lafiya tare da horar da su da sayen magunguna da kayan aiki da ɓullo da ayyukan kula da lafiyar mata da ƙananan yara kyauta. Sannan, an gyara asibitin ƙwararru na...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare. Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati. Rahotanni daga Borno da Yobe da ma wasu sassan kasar nan sun nuna yadda ‘yan ta’adda suka sake samun karfi wajen kai hare-hare cikin dare, tare da amfani da dabaru irin na soji da kuma kayan yaki na zamani. Wannan lamari ya jawo tambaya daga al’umma: shin wannan karin hare-hare alama ce ta dawowar kungiyar Boko Haram da...
Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka
A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka. Wannan ya kasance wani bakon abu a fili kuma abin kyama. An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar...
A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sakamakon matakan takunkumi da kasar Amurka ta dauka kan kamfanonin fasahohin zamani na kasar Sin, kasar Sin ta kara saurin yin kirkire-kirkire a matsayin mai zaman kanta, wanda ya haifar da karuwar sabbin nasarori a fannonin da suka hada da fasahohin kere-kere, da na’urar mutum-mutumi, har ma ta zarce sauran kasashe a wasu muhimman fasahohin zamani. Sa’an nan, dangane da takunkumin da wasu kasashen yammacin duniya suka kakaba mata, kasar Sin ta yi kokarin inganta karfin jure wahalhalu da tabbatar da kiyaye bangaren masana’antu da samar da kayayyaki, tare da rage tasirin matsalolin da kan taso daga waje yadda ya kamata. Wadannan ingantattun hanyoyin mayar da martani ga matsin lamba daga ketare sun nuna...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa zata kara karfafa dankon zumunta da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin da mahukunta hukumar NAFDAC suka ziyarce shi a ofishin sa dake Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana farin cikinsa da ziyayar, inda ya jaddada bukatar aiki tare domin cimma dukkan nasarar da ake bukata a tsakanin hukumomin biyu. Da yake bayani dangane da shirin da hukumar alhazan take yi, Labbo yace dukkanin shirye-shirye sunyi nisa na rigistar kujerun aikin hajji shekarar 2026. Yana mai cewar, hukumar NAFDAC tana cikin masu ruwa da tsaki na hukumar jin dadin alhazan jihar. Alhaji Ahmed Labbo, yayi nuni...
Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan mummunar haɗarin fashewar motar mai da ta faru a ƙauyen Essa, cikin Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa. A cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Tsarin Ƙasa, Mohammed Idris, ya sanya wa hannu, Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Neja da al’ummar jihar bisa wannan babban rashi, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin tunawa da illar da ke tattare da haɗarin motocin mai a ƙasar. Sanarwar ta nuna damuwa kan yadda, duk da wayar da kai da gargadin da ake yi a kai a kai, wasu ’yan ƙasa har yanzu ke shiga...
Wani mutum mai suna Mallam Surajo Muhammad Shehu ya rasa ’yan uwansa takwas, lokacin da tankar mai ta yi bindiga a garin Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida, a Jihar Neja. Lamarin ya auku a ranar Talata, wanda aƙalla mutum 28 ciki har da mata da ƙanana yara, suka rasa rayukansu lokacin da tankar ta kife kuma ta kama da wuta yayin da jama’a ke ƙoƙarin ɗibar mai. Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi Wasu da dama sun ji rauni kuma an garzaya da su Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Bida. Shehu, ya ce mata ne suka fi...
Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi. Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin wadannan bala’o’in da za a iya rigakafin su, na nuna bukatar kara wayar da kan jama’a game da haɗurran da ke tattare da hakan cikin gaggawa. Ya ce, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), an umurce ta da ta hada karfi ga kokarin Gwamnatin Jihar ta hanyar samar da kayan agaji da taimakon magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalansu. ShareTweetSendShare...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars October 22, 2025 Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025
Hukumar Kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa a nahiyyar Afirka (CAF) ta fitar da sunayen ‘yan takarar da za su lashe kyautar CAF ta shekarar 2025 – rukunin maza. Cikin wata sanarwa da CAF ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce an yi la’akari da rawar da ’yan wasa da masu horarwa suka taka wajen bunƙasa kwallon ƙafa a nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya. Hukumar ta ce fitattun masu takarar sun ba da muhimmiyar gudunmawa a fagen tamaula wanda za a yi la’akari da rawar da suka taka a tsakanin ranar 6 ga Janairu zuwa 15 ga Oktoba, 2025. Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani Waɗanda ke...
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF), ta bayyana hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a ƙauyen Essa a Ƙaramar Hukumar Katcha a Jihar Neja, a matsayin abin baƙin ciki da tausayi. Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne, ya yi alhinin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II Majalisar Yobe ta nemi a dauki mataki kan yawaitar hadura a hanyar Damaturu–Potiskum Ya miƙa saƙon ta’aziyyae ga gwamnatin Jihar Neja da al’ummarta da kuma iyalan da abin ya shafa. “Wannan lamari abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske. Addu’o’inmu suna tare da iyalan mamatan da kuma jama’ar Jihar Neja a wannan lokaci na...
Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma, gwamnan ya gyara Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Zamfara (ZACAS). A ɓangaren lafiya kuwa, gwamnatinsa ta gyara asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama a faɗin jihar. Don rage mace-macen mata da jarirai a yayin haihuwa, ya ɗauki ƙarin ma’aikatan lafiya, tare da samar da magunguna da kayan aiki, tare d harkar kyautata kiwon...
A karon farko a tarihi, an gano sauro a ƙasar Iceland, tare da gano samfura guda uku a wannan watan a Kjos, wani yanki mai ƙwari a kusa da Hvalfjordur. Wani mai sha’awar ƙwari, Bjorn Hjaltason ne ya fara ba da rahoton ganowar a cikin wani zaure na Facebook mai suna Skordyr a Islandi (wato ƙwari a Iceland), kamar yadda Hukumar Watsa Labarai ta Iceland ta faɗa a ranar Litinin. Gwamnatin Borno rufe makarantun jihar saboda rigakafin ƙyanda da Polio Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya An miƙa samfuran ga Cibiyar Tarihin Halittu ta Iceland domin bincike, inda masanin ilimin halitta Matthias Alfredsson ya tabbatar da cewa lalle sauro ne. An bayyana samfurin a matsayin Culiseta annulata,...
Cikakken bayani na tafe… ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja October 22, 2025 Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago. Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya “Tunaninmu yana tare da iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna godiya ga ma’aikatan agajin gaggawa bisa taimakon da suka bai wa waɗanda abin ya rutsa da su,”...
Har ma abun da ba kasafai ake gani ba, tattalin arzikin Sin yana cike da karfin tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai. Ba sabunta kayayyaki kirar kasar da kara musu inganci kadai aka samu ba, har ma abokan cinikin kasar a ketare suna ta kara yawa. A jiya Litinin ne aka bude cikakken zama na 4 na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a nan Beijing, inda za a tattauna da kuma ba da shawarwari kan shirin shekaru biyar-biyar na 15 na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin. Kasashen duniya na sa ran cewa, kasar Sin za ta ba da sababbin damammarkin neman samun ci gaba ga duniya, bisa ga...
Ana fargabar cewa aƙalla mutum 30 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon fashewar wata tankar man fetur a ƙauyen Essa da ke hanyar Agaei zuwa Bida a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa, akwai kuma kimanin mutum 40 da suka jikkata wadanda suka wawason kwalfar man fetur bayan kifewar tankar. Bayanai sun ce da misalin karfe 11 na safiyar wannan Talatar ce tankar ta kife a titin Essan da aka bayyana cewa lalacewar hanyar ce ta haddasa hatsarin.
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da shirinsa na ɗaga darajar Kwalejin Jinya ta Nafisatu da ke Kwankwaso zuwa cikakkiyar Jami’ar Kiwon Lafiya albarkacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Taron na wannan Talatar, 21 ga watan Oktoban 2025, ya gudana ne a garinsa na Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi, inda aka yaba da ci gaban da makarantar ta samu tun daga kafuwarta a 2019 zuwa yanzu. Tinubu ya naɗa sabon Minista Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru Kwankwaso ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ƙara buɗe damammaki ga mata matasa su sami ilimin kiwon lafiya mai zurfi. Ya jaddada cewa makarantar ita ce ta farko a Najeriya da ke karɓar dalibai...
Sun ce wadanda suka mutu yawancinsu wadanda suka je kwaso man fetur ne a lokacin da tankar ta yi hatsari kafin fashewar. Shugabannin Direbobin Tankar Mai na Jihar Neja (PTD) da Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NUPENG) ta kasa, Kwamared Farouk Mohammed Kawo, sun tabbatar wa LEADERSHIP faruwar lamarin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba October 21, 2025 Manyan Labarai NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi October 21, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar Cerebral Palsy, wato tsukewar ƙwaƙwalwa, na daga cikin manyan matsalolin lafiyar yara da ke tasowa tun daga haihuwa. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon rauni ko lalacewar wani ɓangare na ƙwaƙwalwa da ke kula da motsi, magana, da daidaiton jiki. A mafi yawan lokuta, cutar tana bayyana ne tun daga ƙuruciya, a wasu lokutan kuma kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana, cutar na faruwa ne tun kafin a haifi yaro. Ko ta waɗanne irin hanyoyi wannan cuta take kama yaro? NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta samu nasara a karo na biyu a gasar Firimiya ta Nijeriya (NPFL) bayan ta doke abokiyar hamayyarta Kano Pillars da ci 2–1 a wasan da suka buga a yau Lahadi a filin wasa na Sani Abacha, Kofar Mata, Kano. Rabiu Ali, kyaftin ɗin Kano Pillars, ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Barau FC a minti na 20 da fara wasa. Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Ibrahim ya farke ƙwallon ga Barau FC a minti na 50, sai kuma Stanley da ya ƙara ta biyu wanda ya tabbatar wa Barau FC nasara a wasan. NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3 Kocin Kano Pillars...
An bude taron sanin makamar aiki na kasa da kasa mai taken “Cika shekaru 80 da kafuwar MDD: Makomar tsarin duniya, dokokin kasa da kasa, da ra’ayin kasancewar bangarori da dama”, wanda jami’ar Wuhan ta kasar Sin, da jami’ar Benha ta kasar Masar suka hada kai suka karbi bakuncin shirya shi. Yayin bude taron a yau Asabar a birnin Wuhan na kasar Sin, tsohon mataimakin sakatare-janar na MDD Miguel de Serpa Soares, da babban sakataren kungiyar ba da shawarwari kan shari’a ta Asiya da Afirka ko (AALCO) Dr. Kamalinne Pinitpuvadol, da shugaban jami’ar Benha ta Masar Nasser EL-Gizawy, da farfesa a jami’ar Wuhan Ignacio de la Rasilla, da ma wasu mahalartan taron sun bayyana cewa, dole ne a kare...
Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo, ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Lawal Faruƙ da ake zargin ya bankawa tsohuwar masoyiyarsa wuta bayan da dangantakar su ta yi tsami. Majiyar PUNCH Metro ta samu labarin a ranar Alhamis cewa, lamarin ya faru ne a barikin sojoji da ke Ibadan babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun kama ’yan bindiga 2, sun ƙone sansaninsu a Kogi Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay Wani ƙwararre a fagen yaƙi da ’yan tada ƙayar baya, Zagazola Makama wanda ya bayyana yadda lamarin ya faru a shafinsa na sada zumunta na X, ya bayyana cewa, wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa shi...
An fara gina magudanan ruwa domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa. Tawagar Injiniyoyin jihar karkashin jagorancin Daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Injiniya Mukhtar Muhammad Usman sun ziyarci kananan hukumomin domin duba yadda aikin ke gudana. Haka zalika Daraktan da mataimakin sa Injiniya Mahdi Isyaku da sauran ma’aikata ssn ziyarci wurin da ambaliyar ruwa tayi ta’adi a garin malam Madori. A lokacin da tawagar ta fara auna fili da tona magudanun ruwan, daraktan ya ce an fara aikin tona magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2 a matsayin wani ɓangare na aikin karkatar da ruwan da ya lalata wurare zuwa sabon wurin da aka tsara. Yana mai cewar,...
Baya ga yi masu afuwa, Shuagaba Tinubu, ya kuma karama su da lambar yabo ta kasa. ‘Yan Ogonin su tara, sun dai fuskanci shari’a ne, bisa zarginsu da kitsa kisan sarakunan Ogoni Albert Badey, Edward Kobani, Theophilus Orage da kuma Samuel Orage. Kotu ta tuhumi ‘yan Ogonin su tara, ta kuma yanke masu hukuncin rataya a ranar 10 ga watan Numambar 1995. Hukucin na Kotun, a wancan lokacin, ya haifar da hatsaniya tare da yin suka daga bangaren manyan shugabannin kasasshen duniya, daidaikun mutane da sauran kungiyoyi, musaman duba da cewa, an yanke masu hukuncin ne, a lokacin da ‘yan kasar ke nuna tsanar mulkin soji, biyo bayan soke zaben shugaban kasa, da ake da yakinin an yi sahihin zabe...
A baya- bayan nan ‘yan ta’addan wadanda suka daura damarar hanawa al’umma kwanciyar hankali sun kashe daruruwan mutane, kona gidaje tare da garkuwa da mutane ciki har da mata da kananan yara. Rahotanni daga yankunan sun tabbatar da yadda al’umma suka gaji suka kosa da jin alkawura marasa adadi daga gwamnati wadda ke kasa cikawa a yayin da hare-hare ke karuwa a duk shekara duk da karin kudaden tsaro da ake warewa.. A Sakkwato, kauyuka da dama kamar Giyawa, Kurawa, da Unguwar Lalle a gabascin Sakkwato hedikwatar gawurtaccen dan ta’adda Bello Turji sun fuskanci hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a baya- bayan nan. A Karamar Hukumar Sabon- Birni, wasu mazauna yankin sun tsere domin tsira da...
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin tarihi, wanda Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka yi wa Sir Herbert Macaulay, daya daga cikin masu kishin kasa a Nijeriya. A takaice dai, kwamitin bai wa shugaban kasa shawara, kan jinkai, karkashin jagorancin babban mai shari’a; kuma ministan shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi, ya bayar da shawarar yin afuwa ga fursunoni biyu da 15 da aka yankewa hukunci, wadanda 11 daga cikinsu sun...
Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da KuraAfuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da Kura
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin tarihi, wanda Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka yi wa Sir Herbert Macaulay, daya daga cikin masu kishin kasa a Nijeriya. A takaice dai, kwamitin bai wa shugaban kasa shawara, kan jinkai, karkashin jagorancin babban mai shari’a; kuma ministan shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi, ya bayar da shawarar yin afuwa ga fursunoni biyu da 15 da aka yankewa hukunci, wadanda 11 daga cikinsu sun...
Kasar Saudiyya ta rage yawan guraben kujerun aikin hajjin da take ware wa Najeriya daga 95,000 zuwa 66,910 daga shekarar 2026. Aminiya ta ruwaito cewa a baya Najeriya ta shafe tsawon shekaru uku tana samun guraben na 95,000 a yayin Aikin Hajjin. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi A cewar Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), wannan sauyi ya biyo bayan gazawar Najeriya wajen cika guraben da aka ware mata a hajjin shekarun 2024 da 2025. Wata sanarwa da, Mataimakiyar Darakta a Sashen Yaɗa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara, ta sanya wa hannu, ta ce hakan na nufin za...
Wani binciken tattara ra’ayoyi da aka gudanar a shekarar nan ta 2025, ya nuna kaso 72.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun gamsu da manufar Sin ta bude kofa, da kasuwarta mai amincewa da kyakkyawar takara. Kana kaso 79.8 bisa dari na ganin babbar kasuwar Sin ta samar da muhimman damammaki ga kasashensu na asali. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya October 16, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona October 16, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba...
Bayan juyin mulkin da aka yiwa Andry Rajolina a kasar Madagaska kungiyar tarayyar Afirka ta bada sanarwan jingine kasar daga zama mama a cikinta har zuwa abinda hali yayi. \ Tashar talabijin ta Almayadin ta nakalto majiyar kungiyar AU na bada wannan sanarwan, kwana guda bayan da sojoji suka yi juyin mulki wa shugaba Andria Rajolina juyin mulki a tsibirin Madagaska. Sabon shugaban kasar Madagaska Micheil Rondri Yorinina ya bayyana cewa zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar zuwa lokacinda kasar zata koma cikin hayyacinta. Sannan a san abinda za’a yi. Mutanen kasar Madagaska dai sun dade suna zanga-zangar bukatar Rajolina ya sauka tunda ya kasa kyautata rayuwar mutanen kasar. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login...
Wani daga cikin waɗanda suka ji rauni, wanda shi ne mai kuɗin, ya gode wa jami’an FRSC bisa gaskiya da amana da suka nuna, yana mai cewa abin koyi ne ga kowa. FRSC ta gargaɗi direbobi da su riƙa kula da motoccinsu akai-akai tare da bin ƙa’idojin hanya domin guje wa aukuwar haɗura. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025 Labarai Kafafen Sada Zumunta Na Zamani Suna Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro A Arewa – Yari October 15, 2025
Hukumar kula da gidaje ta jihar Kano ta fara wani gagarumin aikin tsaftar muhalli kashi na biyu a birnin Kwankwasiyya, inda ta kara azama wajen gina tsaftataccen muhalli, lafiya da kuma dorewar muhalli a birane. Da yake jawabi yayin aikin, mukaddashin Manajan Daraktan Kamfanin, Engr. Isyaku Umar Kwa, ya bayyana cewa kashi na biyu ya mayar da hankali ne kan inganta harkar sharar gida, da inganta tsarin tattara shara, da kuma kawata wuraren jama’a a fadin birnin na Kwankwasiyya. A cewarsa, aikin na da nufin tabbatar da tsaftar tituna, wuraren shakatawa, da wuraren jama’a tare da inganta alkinta muhalli. Engr. Kwa ya bayyana cewa an tsara wannan shiri ne domin karfafawa mazauna garuruwan Kwankwasiyya da Bandirawo da...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da fitar da Naira biliyan 5.8 domin biyan haƙƙin tsoffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar. Kwamishinan kuɗi na jihar, Mohammed Abatcha Geidam, ya ce wannan mataki na nuna yadda gwamnatin ke ƙoƙarin inganta rayuwar ma’aikatanta, musamman waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar. Farashin kayayyaki ya sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba — NBS Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan Ya ce gwamnan ya bayar da umarni cewa daga yanzu, biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata zai zama cikin jadawalin kuɗin wata-wata kamar yadda ake biyan fansho. “Ina nufin daga yanzu za a riƙa biyan kudin a kowane wata tare da fansho, domin...
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani
A nata bangare, Sima Bahous ta yabawa ci gaban da Sin ta samu wajen cike gibin fasahohi tsakanin jinsi, da ingiza ci gaban harkokin mata ta kowanne bangare da kare hakkoki da muradun mata. Ta kuma yi kira ga kasa da kasa su hada hannu tare wajen karfafa gwiwar mata da ‘yan mata su samu ci gaba a zamanin amfani da fasahohi. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa October 14, 2025 Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025 Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude...
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad ta yi maraba da sako Falasdinawa kusan 2000 daga gidajen yarin Isra’ila, tare da cewa jarumtakar mayakan gwagwarmaya da hadin kan al’ummar Falasdinu ne ya haifar da wannan babbar nasara. A cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Ziyad al-Nakhalah ya fitar ya bayyana cewa, wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta samo asali ne sakamakon jajircewa da tsayin daka da hadin kan al’ummar Falasdinu, wanda idan ba tare da hakan ba yarjejeniyar ba za ta taba cimma ruwa ba. Bayan shafe sama da shekaru biyu ana kai hare-hare ba kakkautawa wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatan Falasdinawa, gwamnatin Isra’ila bisa matsin lambar kasa da kasa ta amince da yarjejeniyar da Amurka ta kulla...
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da PDP ke shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da za a yi a Ibadan, a Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan October 14, 2025 Siyasa Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi October 11, 2025 Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025
SP Shiisu ya ce bincike na ci gaba domin gano musabbabin ɓarkewar rikicin. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ƙara haɗa kai da jami’an tsaro da kuma gaggawar bayar da rahoto idan suka lura da wani abin da zai iya janyo rikici, domin kauce wa zubar da jini. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi October 14, 2025 Manyan Labarai Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa October 14, 2025 Labarai ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara October...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baqahea yayi gargadin game da barazanar da ake fuskanta na bazuwar fadan da ake yi a kan iyaka tsakanin kasar Afganistan da kuma kasar Pakistan, a yankin, inda dukkan bangarorin biyu suke musayar wuta a wurare daban daban dake kusa da iyakokin kasashen. Yace babban abin da ke da muhimmanci a wajen mu shi ne batun tsaro da zaman lafiya a kasashen dake makwabtaka da su, kasashen Pakistan da Afghanistan yan uwan mu ne musulmi dake makwabtaka da mu, kuma ya yi amanna cewa duk wani kace-nace tsakanin kasashen biyu to zai iya fantsama zuwa wasu kasashe, Jamhuriyar musulunci ta Iran ta yi kira ga kasashen biyu da su koma teburin tattaunawa, kuma...
Ɗan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Sabon Gari Daga Jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya fice daga Jam’iyyarsa ta PDP. Honorabul Abdullahi wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamishinan Hukumar Kula da Hanyoyi (FERMA) ya alaƙanta ficewarsa da rikicin cikin gida da rabuwar kai da ya ki ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar. A ranar Litinin ya aike da wasikar ta ficewa ga Shugaban PDP na Mazabar Hanwa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, yana mai cewa rikicin ya hana shi taɓukawa matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya. Ya cewa saboda haka yana dacewar ficewarsa daga jam’iyyar ba tare da la’akari da siyasa ba, domin amfanin ɗauƙacin al’ummar mazabar. Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary...
“Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”. Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana cewa, makon hako ma’adanai na Nijeriya ya yi nuni da yadda masana’antar ke sauya tunani zuwa tsari mai kyau, da sabbin abubuwa, da ke lalubo masu zuba jari na kasa da kasa. Ya bayyana cewa, sauye-sauyen sun tattara ne a kan gaskiya, rage haɗari, da inganta masana’antar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27...
An bayyana katin zabe a matsayin sheda da za a iya amfani da shi a muhimman wurare, kamar yadda ake amfani da fasfo da katin dan kasa a manyan kasashen duniya. Tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji, Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yi wannan tsokaci new a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse. Ya bayyana bukatar aiki tukuru a tsakanin masu ruwa da tsaki dan tabbatar da cewar dukkan wadanda su ka cancanta sun karbi katin zaben. Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa kafa kwamati na musamman a karkashin mai bada shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Garba Bullet, domin zaburar da kananan hukumomi su bada gudummawar da za ta taimaka...
Sanarwar ta kara da cewa, “mun yi farin cikin ganin cewar yan wasan kungiyoyin biyu da jami’an wasan duk sun bar filin wasan ba tare da samun wani rauni ba kuma jami’an tsaro suka yi musu rakiya, kungiyar ta kara da cewa an kama wasu da dama da ake zargi da hannu a rikicin tare da mika su ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya. Kungiyar ta jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da da’a, kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da ingancin wasan kamar yadda hukumar NPFL da hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta tanada, Pillars ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su...
An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki. Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11, ciki har da tsoffin muƙarrabansa. Ɗaya daga cikinsu shi ne Issa Tchiroma Bakary, tsohon ministan ma’aikata wanda ya yi murabus daga gwamnati a watan Yuni bayan fiye da shekaru 20 yana aiki tare da Biya. Bakary, mai shekaru 79, ya zama babban abokin hamayyar Biya bayan Kotun Tsarin Mulki ta ƙi amincewa da takarar fitaccen ɗan adawa Maurice Kamto — matakin da ƙungiyoyin kare haƙƙin...
Matar da ta daina ganin girman mijinta ta riga ta fara ruguza aurenta, da zarar kin yi masa maganganu na cin mutunci, kin yi kamar kin tozarta kanki da kanki ne, saboda girman mace a cikin aurenta yana da alaka da girman mijinta. 2. Rashin adalci tsakanin mijinki da danginsa Ki sani, mijinki zai iya jure miki a kuskuren da kike masa kai tsaye, amma zai dade yana daukar zafin abin da kika aikata wa iyayensa, ‘yan uwansa ko danginsa, wannan babban kuskure ne da mata da dama suke yi su kuma yi nadama daga baya. 3. Rashin Tausayi da Kulawa Ki sani, koda kuwa mijinki yana da kudi, yana bukatar jin tausayi daga gare ki. Idan ya dawo gida...
Mahukuntan kasar Afirka Ta Kudu sun sanar da cewa, ya zuwa yanzu ba a sami wani dalili na musabbabin mutuwar jakadan kasar Nathi Mthethwa A Afransa ba. Jami’an tsaron kasar Faransa suna aiki tare da takwarorinsu na kasar Afirka Ta Kudu da su ka isa kasar domin gano musabbabin mutuwar jakadan. An ga gawar jakadan na kasar na Afirka Ta Kudu a kasar Faransa,Mthethwa a Hotel din Hyatt Regency dake birnin Paris. Alamu sun nuna cewa ya bude kofar dakinsa dake hawa na 22 ya fado kasa, ba tare da wata alama dake nuni da cewa turo shi aka yi baa. Gabanin faruwar lamarin jakadan ya aike da sako na waya ga maidakinsa da a ciki ya bayyana mata shirinsa...
Rahotanni sun tabbatar da cewa bababn jami’in kungiyar Hamas Basen Naim yayi watsi da duk wani kokor nai ya yiyuwar sanya hannu tsohon fira ministan birtaniya Tony Blair a gwamnatin da za’a kafa a yankin gaza bayan sanar da dakatar da bude wuta da aka yi a baya bayan nan. Har ila yau Basem ya kara da cewa kungiyar tana maraba da kokarin da shugaban Amurka Donal trump yake yi na kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ta kwashe shekaru 2 tana yi a yankin Gaza, sai dai sun yi gargadin cewa basa maraba da tony Blair game da taka wata rawa a sabuwar gwamnatin Gaza da za’a kafa bayan tsagaita wuta. Yace idan aka zo batun Blair kila mu...
Kungiyoyin matasa na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Morocco, Sarkin Mohammed na shida, ya bukaci zababbun jami’ai a kasar da su daina jan kafa wajen kyautata rayuwar al’ummar kasar, yana mai cewa inganta harkonin ilimi da kiwon lafiya shi ne abinda ya kamata a fi ba muhimmanci. An jima ana dakon jawabin sarkin na wannan juma’a, tun bayan da masu zanga-zangar, suka fara mamaye titunan biranen kasar kusan ko wanne dare tun daga ranar 27 ga watan da ya gabata na Satumba. Masu zanga-zangar dai wadda ake yiwa lakabi da Gen Z, na ci gaba da ƙ kiraye-kirayen kawo sauyi, ko da yake a yayin jawabin Sarkin na wannan Juma’a bai yi magana kai tsaye game da ita...
Shugabannin masana’antu sun kuma yi kira ga gwamnati da ta daidaita tattalin arziki, inganta saukin gudanar da harkokin kasuwanci, da aiwatar da shirye-shiryen tallafi ga masana’antu na cikin gida. Bugu da kari, masana sun nuna cewa rikicin kudin waje da rashin daidaito a kimar musayar kudi su ne manyan matsaloli ga kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen waje, inda kalubalen samun damar mayar da ribar kamfani zuwa kasashen waje da samun kudin waje ke rage amincewar masu zuba jari sosai kuma yana karfafa su su bar kasar. Binciken da LEADERSHIP Sunday ta gudanar ya nuna cewa yanayin tattalin arzikin Nijeriya ya sha wahala tun daga shekarar 2020, inda wasu kamfanoni suka rufe ayyukansu, ko suka yi kaura, ko...
Li ya ce kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jam’iyyar WPK, don ta bayar da jagoranci ga al’ummun kasar Koriya ta Arewa, wajen neman ci gaba bisa halin da kasar take ciki. A sa’i daya kuma, kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama, kamar aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare da kara musayar manyan jami’ai, da mu’amala kan manyan tsare-tsare, ta yadda za a inganta fahimtar siyasa a tsakanin kasashen biyu, tare da cimma sakamako mai kyau bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Koriya ta Arewa. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Wajen...
Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4, 2025 Tsaro Bayan Sulhu Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina September 22, 2025
Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya October 10, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025
Tawagar da ke karkashin jagorancin, Barry Andrews ta kuma ziyarci hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), inda shugabanta, Mahmood Yakubu, ya yi gargadin cewa jinkirin da ‘yan majalisa ke yi wajen gyaran dokar zabe ta 2022 na iya kawo cikas ga shirye-shiryen gudanar da zabe a 2027. Wakilan, wadanda suke Nijeriya tun kusan makonni uku domin nazarin matakin aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahotonsu na bayan zaben 2023, sun kuma yi tattauna da babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Abbas, a cikin wata sanarwar da sakataren yada labaransa, Leke Bayeiwu, ya shaida wa tawagar EU cewa rahotanninta kan zabukan shekarar 2023 ana la’akari da su a cikin sauye-sauyen gyara dokar zabe da na dimokuradiyya da...
Wannan lamari ya haifar da tambaya kan yiwuwar dorewar shirin sauye-sauye da na zamani da ake gudanarwa a karkashin jagorancin Babban Kwanturola Janar, Adewale Adeniyi. Adewale Adeniyi, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara wa wa’adin mulki na shekara guda, shima zai yi ritaya daga hukumar a watan Agusta, 2026. A halin yanzu, za a dauki babban mataki kafin a cike gibin ma’aikata da ake bukata a hukumar kwastam, musamman idan aka yi la’akari da cewa jami’ai 825 za su bar aiki ba tare da sabon daukar ma’aikata ba. Binciken da leadership Hausa ta gudanar ya gano cewa ritayar ta shafi kowane mataki a hukumar daga manyan shugabanni, zuwa matsakaita, har da kananan jami’ai. Daga cikin...
“Akwai da yawa malamai marasa cancanta a cikin aikin. Muna da wadanda ke koyarwa a ajujuwa amma ba su da takardun shaidar koyarwa, musamman a makarantu masu zaman kansu,” in ji ta. Ta bayyana cewa, yayin da wasu mutane ke da sha’awar koyarwa da gaske, rashin horo na hukuma ya hana su shiga aikin koyarwa. Dr. Soyombo ta bayyana cewa TRCN a halin yanzu na da malamai masu rijista kusan miliyan 1.4, tare da shirin kara wannan adadi zuwa miliyan 20 cikin shekaru biyu masu zuwa ta hanyar dijital da saurin rajista. “Mun zamanantar da tsarinmu domin mutane da yawa su sami damar yin rijista,” in ji ta. “Kowane malami yana da bai wa ta musamman...