Super Falconets ta lashe gasar WAFU ta ’yan ƙasa da shekaru 20
Published: 12th, November 2025 GMT
Tawagar matan Najeriya ’yan ƙasa da shekaru 20, Super Falconets, ta lashe gasar Yammacin Afirka ta bana WAFU B U-20, bayan ta doke Black Princesses ta Ghana da ci 3-0 a wasan ƙarshe da aka buga a safiyar Talata.
An fafata wasan ne a filin Stade Omnisports da ke Jamhuriyar Benin, inda Akekoromowei, Alaba Olabiyi da Ramotalahi Kareem suka zura ƙwallaye uku da suka bai wa Najeriya nasara.
Wannan shi ne karo na farko a tarihi da Super Falconets ke lashe wannan kofin tun lokacin da aka fara gasar.
Ghana, wadda ta lashe kofin a shekarar 2023, ta kammala wannan karo da maki shida kacal, yayin da Najeriya ta ɗaga kofin bayan samun nasara a duk wasanninta.
Yanzu hankalin Super Falconets zai koma kan wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta Mata ’Yan Ƙasa da Shekaru 20 ta 2026, inda za su kara da Senegal a watan Fabrairu mai zuwa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe
Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanninta a Jihar Gombe, inda ta jaddada muhimmancin haɗin kai da farfado da jam’iyyar tun daga matakin ƙananan hukumomi zuwa jiha gabanin zaɓen 2027.
Taron ya halarta bayan zuwan wakilai daga dukkanin ƙananan hukumomin jihar.
Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – Bago Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 2, sun ƙwato makamai a BornoMambobin jam’iyyar sun yaba da yadda komai ya gudana cikin lumana da tsari, abin da suka ce alama ce ta daidaito a cikin jam’iyyar.
Elder Ambrose Ismail Mairungu ne, ya zama sabon shugaban NNPP na jihar, yayin da Yakubu Adamu Tela, ya zama mataimakinsa.
Abdullahi Ali Mohammed, ya samu kujerar sakataren jiha, sannan Hon. Amatiga Yila Naboth (ACG) ya zama sakataren yaɗa labarai.
Sauran da aka zaɓa sun haɗa da Musa Mohammed Gargajiga (Jagoran Matasa), Hajiya Hauwa Mohammed (Shugabar Mata), da Kabiru Mohammed Puma (Sakataren Tsara Ayyuka).
A jawabin da ya gabatar bayan rantsar da su, Mairungu, ya gode wa ’yan jam’iyyar bisa amincewa da suka nuna gare shi, inda ya bayyana cewa sabbin shugabannin za su yi aiki da adalci da tsari, tare da haɗa kowa domin ci gaban jam’iyyar.
Ya ce za su mayar da hankali wajen gina jam’iyyar daga matakin unguwanni, ƙara yawan mambobi, da ƙarfafa shiga matasa da mata a harkokin jam’iyya.
Wasu masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yaba da sabbin shugabannin, inda suka ce suna da damar gyara jam’iyyar kafin tunkarar babban zaɓe.
Haka kuma, sun yi godiya ga Jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, bisa tallafi da goyon bayan da ya bai wa taron.