HausaTv:
2025-11-12@08:44:47 GMT

Sheikh Qassem: Kawar Da Hizbullah Ne Babban Burin Isra’ila A Lebanon

Published: 12th, November 2025 GMT

Babban Sakataren Hezbollah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa “Amurka, ta hanyar wakilanta na Isra’ila, tana neman kawar da karfin gwagwarmayar Lebanon da kuma ba sojojin kasar makamai don fuskantar Hezbollah,” yana mai jaddada cewa manufar wannan matakin shine “kawar da karfin soja da duk wani karfi  fadin Lebanon domin Isra’ila ta ci gaba da cin karenta babu babbaa duk inda ta ga dama a cikin kasar.

Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa “An kafa Hezbollah ne bisa ka’idojin jihadi,  kare mutunci mutunci, da alfaharin Lebanon, da goyon bayan Falasdinu,” yana mai cewa “daga 2000 zuwa 2023, mun kasance cikin yanayi na tsoro.”

Ya bayyana cewa yakin baya-bayan yana a matsayin shinge ga mamayar Isra’ila, wanda ya tsayar da hankoron mamayar Isra’ila kan Lebanon a wasu iyakoki a kudancin Lebanon,” yana mai nuna cewa “Yarjejeniyar Nuwamba tana da muhimmanci domin ya haɗa da tura sojojin Lebanon a kudancin Kogin Litani.”

Ya ƙara da cewa, “Mu masu nasara ne saboda sojojin Lebanon suna nan a kudancin Kogin Litani, domin su ‘ya’yanmu ne. Kuma mu masu nasara ne a cikin wannan yarjejeniyar saboda ƙasar ta yi alƙawarin cika alkawalin da ta dauka.”

Sheikh Qassem ya zargi Amurka da “kasa aiwatar da alkawullanta ta hanyar tursasa Isra’ila yin aiki da yarjejeniyar, domin Lebanon za ta dawo da ‘yancinta da mutuncinta ne kawai idan Isra’ila ta janye.” Ya jaddada cewa “Amurka da Isra’ila suna tsoma baki a cikin makomar Lebanon, suna tantance ayyukan sojojinta, tattalin arzikinta, siyasa, da matsayinta na yankin.”

Ya bayyana cewa “matsin lamba da ake yi wa gwamnati domin ta yi sassauci ba tare da wani lamuni ba, zai kara karfafa gwiwar Isra’ila ne wajen yin gaban kanta a kasar Lebanon.”

Sheikh Qassem ya ci gaba da cewa, “Isra’ila tana son ta mallaki Lebanon ta mayar da ita wurin da za ta kara faɗaɗa matsugunan yahudawa ‘yan share wuri zauna, a matsayin wani ɓangare na Shirin kafa Isra’ila Babba.” Ya nuna cewa “kowace rana suna fito da sabbin hujjoji, tun daga batun  kwance damarar makamai zuwa gindaya wa gwamnatin Lebanon sharudda masu tsauri kan Hizbullah, wanda hakan ke nuni da cwa Hizbullah da karfinta su ne Babbar matsala a gare su.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar Da Sudan Sun Jaddada Wajabcin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin November 12, 2025 Venezuela: Maduro Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tsaron Kasa Mai Cikakkiyar Kariya November 12, 2025 UNICEF: Isra’ila ta hana allurar rigakafin yara masu mahimmanci shiga Gaza November 12, 2025 Ministocin harkokin wajen kasashen yamma sun yi Allah wadai da ta’asar RSF a El Fasher Darfur November 11, 2025 Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya November 11, 2025 Larijani : ‘babu wani sabon sako’ da muka aika wa Amurka November 11, 2025 Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita November 11, 2025 Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar November 11, 2025 Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar November 11, 2025 Hamas ta soki kudurin Isra’ila na yin dokar hukuncin kisa kan laifin ta’addanci November 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Isra ila ta

এছাড়াও পড়ুন:

Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar a ranar Lahadi cewa adadin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen da aka gudanar ya kai kashi 82.42%, wanda ya tabbatar da sahihanci da kyakkyawan tsarin gudanar zaɓen, a cewar hukumar.

Shugaban Hukumar  Omar Ahmed, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai cewa hukumar ta nuna daidaito da adalaci ga dukkan ‘yan Takara.

Ahmed ya bayyana cewa hukumar ta sa ido kan tsarin zaɓe a duk faɗin jihohin ƙasar ta hanyar ƙungiyoyin da ke aiki, yana mai jaddada cewa sakamakon ya nuna jajircewar masu kaɗa ƙuri’a da kuma tafiyar da harkokin zaɓe cikin sauƙi da kuma sahihin tsari.

A cikin wannan yanayi, mai ba da shawara kan harkokin shari’a na hukumar Hassan Salman, ya tabbatar da cewa tsarin zaɓen ya yi armashi kuma an gudanar da shi ba tare da wani cikas ko keta doka ba, yana mai nuna cewa fitowar jama’a a zaben ya zama abin buga misali, domin kuwa ba a taɓa yin irinsa ba.

Salman ya ƙara da cewa na’urori  suna aiki da inganci sosai a duk lokacin zaɓen, kuma ba a sami wata matsala ta fasaha ko katsewar layukan yanar gizo  ba, yana mai jaddada cewa hukumar ta ci gaba da ayyukanta don tabbatar da gaskiya da sahihancin tsarin zaɓen.

An fara gudanar da zaɓen ‘yan majalisar dokoki na musamman na shekarar 2025 a safiyar jiya Lahadi, a tsakiyar tsauraran matakan tsaro da kuma tsarin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (IHEC) ta tsara domin tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Maduro ya kirayi taron CELAC da ya yi tir da ayyukan tsokana na Amurka a yankin Caribbean November 10, 2025 Lebanon: Mutane 28 ne suka yi shahada a hare-haren Isra’ila tun daga watan da ya gabata November 10, 2025 Gwamnan Darfur: Babu zaman lafiya da masu yi wa al’ummar Sudan kisan gilla November 10, 2025 Araghchi : Iran na yunkurin warware rikicin Pakistan da Afghanistan November 9, 2025 Kasashen (AES) za su hanzarta kafa rundunar hadin gwiwa ta tsaro November 9, 2025 Najeriya: An yi zanga-zangar tir da barazanar Trump November 9, 2025 Sudan : MDD ta yi Allah wadai da ta’addancin El-Fasher November 9, 2025 Lebanon: Akalla mutane uku sun mutu a hare-haren Isra’ila November 9, 2025  An Kafa  Mutum-mutumin  Tarihi Na Sarkin Daular Roma Da Ya Durkusa A Gaban Sarkin Iran November 9, 2025  Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati November 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF ta ce Isra’ila ta hana allurar rigakafin yara masu mahimmanci shiga Gaza
  • Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita
  • Hamas ta soki kudurin Isra’ila na yin dokar hukuncin kisa kan laifin ta’addanci
  • Lebanon: An Saki Hannibal Kaddafi Bayan Zaman Kaso Na Shekaru 10
  • Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Isra’ila” A Yankin Saida
  • Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa
  • Lebanon: Hare-haren Isra’ila a watan da ya gabata sun yi sanadin shahadar mutane 28
  • Gwamnan Darfur: Babu zaman lafiya da masu yi wa al’ummar Sudan kisan gilla
  • Lebanon: Akalla mutane uku sun mutu a hare-haren Isra’ila