Leadership News Hausa:
2025-12-13@12:52:18 GMT

‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi

Published: 12th, November 2025 GMT

‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi

Wakil ya ce, bayan samun rahoton, tawagar ‘yansanda karkashin jagorancin jami’in ‘yansanda na sashin, CSP Holman Simon, sun ziyarci wurin nan take domin tantance irin barnar da aka yi.

 

Ya bayyana cewa, binciken farko ya nuna cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da Alhassan Jibrin, wanda aka fi sani da Babani Biri, matashi mai shekaru 20 mazaunin yankin Danjuma Goje, Bauchi, ya jefar da wayarsa ta Android a wurin da aka yi fashin.

 

“Binciken ya kai ga kama wasu mutane uku: Lawan Adamu, da Lawan Idris, mai shekaru 20, da Muhammad Yau, wanda aka fi sani da Madugu, mai shekaru 22, duk mazauna Bauchi ne” in ji CPRO

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista November 12, 2025 Labarai Majalisar Jihar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Kan Laifin Rashin Ɗa’a November 12, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka November 12, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda

Kotun Kolin Najeriya ta soke afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, inda ta ce shugaban ya wuce makadi da rawa ta hanyar yin afuwa ga wacce har yanzu kararta ke gaban kotu.

A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, kotun ta yanke hukunci da rinjayen alƙalai huɗu cikin biyar, inda ta tabbatar da hukuncin kisa da Babban Kotun Abuja ta yanke, kuma Kotun Daukaka Kara ta tabbatar.

‘Haduwata da masu garkuwa da ɗan uwana a dajin Zamfara’ Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa

An yanke wa Sanda hukunci ne a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, a lokacin rikicin cikin gida a gidansu da ke Abuja.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da ta shigar, tana mai cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin kisan kai ba tare da wata shakka ba.

A hukuncin jagoran alkalan, Mai Shari’a Moore Adumein ya ce Kotun Daukaka Kara ta yi daidai wajen tabbatar da hukuncin kotun farko.

Ya ce shiga tsakani na shugaban ƙasa bai dace ba a irin wannan yanayi.

Mai Shari’a Adumein ya ce: “Ba daidai ba ne ga bangaren zartarwa ya yi ƙoƙarin amfani da ikon afuwa kan laifin kisan kai, wanda har yanzu kararsa na gaban kotu.”

A watan Oktoba, an rage hukuncin Maryam zuwa shekaru 12 a kurkuku bayan Shugaba Tinubu ya amince da jerin sunayen wadanda ya yi wa afuwa.

Wannan mataki ya biyo bayan nazari da ya fara da sunaye 175, kafin daga baya a cire wasu saboda irin laifukan da suka aikata.

A lokacin, Mai Ba da Shawara na Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce rage hukuncin Sanda “ya dogara ne da tausayi saboda amfanin ’ya’yanta da kuma kyakkyawan halinta,” sannan ya ce ta nuna “nadama.”

Wannan mataki ya janyo suka a fadin Najeriya, ciki har da adawa daga dangin marigayi Bello.

Hukuncin na Kotun Kolin yanzu dai ya soke afuwar ta Shugaban Ƙasa.

Maryam Sanda ta shafe kusan shekaru shida a kurkuku, kuma hukuncin da aka rage zai bar ta da kusan shekaru shida nan gaba. Amma da hukuncin na ranar Juma’a, an dawo da hukuncin kisa da aka yanke mata tun farko.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka ta kama jirgin ruwan dakon man Najeriya
  • Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda
  • Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina
  • Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
  • Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su
  • Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi AkanDoron Ruwa
  • Ba ni da shirin ficewa daga PDP — Gwamnan Bauchi
  • Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila
  • Rikicin Iyakar Thailand da Cambodia Ya Tilasta wa Dubban Mutane Barin Muhallansu
  • An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara