Kwamitin Tsaro ya tsawaita da shekara guda wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya
Published: 14th, November 2025 GMT
Kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita da shekara guda wa’adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Duk da shakkun da Amurka ta yi, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya tsawaita wa’adin aikin tawagar ta MINUSCA, a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya har zuwa ranar 15 ga Nuwamba, 2026.
Duk da haka, Majalisar ta nuna yiwuwar rage wa’adin saboda shiryen shiryen zaben da ake yi a shekarar 2026.
An amince da kudurin da kuri’u 14 sai kuma kin amincewa daga Amurka.
An samar da tawagar ta MINUSCA a watan Afrilun 2014 don kokarin kawo karshen yakin basasar da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kan Shugaba François Bozizé.
Rage kasafin kudin Amurka, ya tilasta wa Majalisar Dinkin Duniya rage yawan sojojinta da aka tura a duk duniya, wanda ya sanya kwamitin tsaro ya dan rage yawan sojojin MINUSCA zuwa (14,046 daga 14,400 a baya) tare da jaddada “aniyar sake duba adadin ma’aikatan bayan kammala nasarar aiwatar da zaben da aka tsara a 2025 da 2026.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin November 14, 2025 Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka November 14, 2025 Iran da China na bunkasa alakoki da hadin gwiwa a tsakaninsu November 14, 2025 Abdoulaye Diop: ‘Yan Tawaye Ba Za Su Iya Mamaye Dukkan Kasar Mali Ba November 14, 2025 Ramaphosa Ya Caccaki Trump Kan Kauracewa Taron G20 A Johannesburg November 14, 2025 MDD ta nuna damuwa game da rahotannin kisan gilla a El Fasher November 14, 2025 Rasha Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Amurka November 13, 2025 Iran Da Qatar Sun Tattauna Kan Dangantakar Dake Tsakaninsu November 13, 2025 Yahudawa Yan Share Wuri Zauna Sun Kona Masallaci A Yammacin Kogin Jodan November 13, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Fara Karbar Harajin Man Fetur November 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta soki Kasashe Masu Karfi Na Bawa Isra’ila Dama Ta Musamman Wajen Kai Hare-hare
Shugaban kasar Iran Masud pezeshkiyan a wajen taron zaman lafiya na turkmanistan ya bayyana cewa siyasar kasashe masu karfin fada aji a yammacin Asiya ne suka bawa isra’ila wata dama ta musamman ta kai hare-hare gaba gadi, da hakan ya bata damar kai harin soji kan kasashen yankin ciki har da kasar iran ba tare da fuskantar wani sakamako ba.
Har ila yau shugaba peszeshkiyan da yake bayani a wajen taron zaman lafiya a garin Ashgabat na kasar Turkministan ya kara da cewa harin da Isra’ila ta kai wa iran a watan yuni da ya kai ga shahadar mutane da dama da basu san hawa ba balle sauka ya samu kyakkawar tarba ne ma mai makon yin Allah wadai
Yace babu wani mataki na ladabtarwa da aka dauka ga wadda ta kai harin , ta ma samu cikakkiyar goyon bayan siyasa da soji ne daga kasahen masu ikirarin kare hakkin bil adama da kuma samar da zaman lafiya, matukar aka ci gaba da bada irin wannan dama ta musamman to babu wanda zai iya yin Magana kan zaman lafiya ko kuma wani umarni na kasa da kasa.
Daga karshe shugaba pezeshkiyan ya godewa Turkmenistan da ta dauki nauyin shirya wannan taro wanda ya zo dadai da aka cika shekaru 30 da amincewa da zama yar baruwanmu a wannan kasa, kana kuma yayi kiran cewa suna goyon bayan duk wani shiri na karfafa tunani kan zaman lafiya da tsaro da ci gaban dan adam da na dabi’a .
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shuwagabannin Kasashen Iran Da Iraqi Sun Tattauna A Wajen Taron Zaman Lafiya A Kasar Turkmanistan December 12, 2025 Kungiyar NLC A Najeriya Ta Shirya Zanga-Zanga Kan Matsalar Rashin Tsaro A Fadin Kasa December 12, 2025 Duniyarmu A Yau: Iran Da Kokarin Juyin Mulkin Amurka A Yakin Kwanaki 12, Wa Ya Sami Nasara? December 12, 2025 Pezeshkian: Duniya Tana Bukatar Amintaccen Madogara, Zaman Lafiya Da Kuma Hadin Kai December 12, 2025 Iran Zata Dauki Bakoncin Taro Dangane Da Kasar Afganistan Da Tsaron Yankin December 12, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut December 12, 2025 Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba December 12, 2025 Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026 December 12, 2025 Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza December 12, 2025 Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci