Leadership News Hausa:
2025-11-10@11:58:29 GMT

Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

Published: 10th, November 2025 GMT

Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.

 

“A yau, a cikin nuna goyon baya, dubban ‘yan mazaɓarmu a garinmu na Ƙofa, Bebeji, Kano sun yi min maraba sosai.

Taron ya tabbatar barinmu jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya, zuwa APC, da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a kan mulki,” in ji Jibrin.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025 Labarai NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna November 9, 2025 Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya gana da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a.

Sarkin Musulmi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya gana da Shugaban Ƙasa ba tare da ’yan jarida ba.

Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800

Ganawar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya gana da Archbishop Ignatius Kaigama na Katolikan Abuja, a wani yunƙuri na inganta dangantakar addinai da zaman lafiya a Najeriya.

Ko da yake ba a bayyana abin da suka tattauna ba, amma ganawar ba za ta rasa nasaba da ƙarfafa fahimtar juna tsakanin addinai da kuma bunƙasa haɗin kan ƙasa da ci gaba.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya bisa zargin cin zarafin Kiristoci.

Bayan ganawar, Sarkin Musulmi, ya raka Shugaba Tinubu zuwa sallar Juma’a a Masallacin Fadar Shugaban Ƙasa.

A lokacin huɗubar sallar Juma’ar, limamin masallacin, Alhaji Abdulwaheed Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa zaman lafiya da tsaro.

Ya tunatar da jama’a cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shi
  • Yarin Fika ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a Yobe
  • Yarin Fika ya sauya sheƙa PDP zuwa APC a Yobe
  • Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
  • Minista Goronyo ya Duba Ci Gaban Aikin Titin Abuja Zuwa Kano
  • Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata
  • Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja
  • Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock
  • Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja