Aminiya:
2025-11-10@07:43:56 GMT

Mahaifiyar Minista Balarabe Lawal Abas ta rasu

Published: 10th, November 2025 GMT

Allah Ya yi wa Hajiya Ɗayyabatu, mahaifiyar Ministan Muhalli, Balarabe Lawal Abas, rasuwa tana da shekara 93.

Hajiya Dayyabatu Lawal Aliyu, ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da jinya, a gidanta da ke unguwar Bambale da ke birnin Zariya.

Ta rasu ta bar ’ya’ya hudu da jikoki da dama.

Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi NAJERIYA A YAU: Dalilan Yaɗuwar Cututtuka A Irin Wannan Lokaci

Ana sa ran gudanar da Sallar jana’izarta a safiyar Litinin daina nan da misalin ƙarfe 11, a gidan nata da ke Bambale, Birnin Zariya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: mahaifiyar rasuwa

এছাড়াও পড়ুন:

Minista Goronyo ya Duba Ci Gaban Aikin Titin Abuja Zuwa Kano

Ministan Kasa a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Bello Muhammad Goronyo, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na tabbatar da kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano, da kuma wasu manyan tituna a Arewacin ƙasar nan.

Ministan, Barrister Bello Goronyo (ESQ), ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara don duba yadda aikin ke gudana, domin tabbatar da cewa ana sa idanu sosai, kuma ‘yan kwangila suna gudanar da aikin cikin inganci da nagarta.

Ministan ya fara duba aikin tun daga Tungan Maje, Madalla, Zuma Resort, Sabon Wuse, Jere, Abuja Junction, Gwanin Gora, sannan ya ci gaba zuwa Zaria har zuwa Kano, inda aikin ke ci gaba yadda ya dace.

Haka kuma, Ministan ya ja kunnen kamfanonin da ke gudanar da aikin; Mother Cat, Infeouest, da Halis Matrix Limited Construction Company, da su tabbatar sun kammala aikin kafin karshen shekarar 2025, kamar yadda Shugaban Kasa ya bayar da umarni.

Barrister Bello Muhammad Goronyo ya bayyana cewa Shugaban Kasa Tinubu na da damuwa matuƙa kan wahalar da matafiya ke sha wajen amfani da wannan hanyar, wanda hakan yasa gwamnati ta maida hankali sosai kan aikin.

A cewar Ministan, kamfanonin sun riga sun yi alkawarin kammala aikin a kan lokaci tare da tabbatar da ƙyakykyawan aiki kamar yadda aka shimfiɗa ka’idoji.

Wannan ziyarar duba aikin dai an gudanar da ita ne bisa umarnin Shugaban Kasa ga Ministan Kasa na aikin, Honourable Bello Muhammad Goronyo (ESQ), domin tabbatar da cewa aikin yana tafiya yadda ya kamata ba tare da tangarda ba.

Kaura Namoda/ Wababe

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Minista Goronyo ya Duba Ci Gaban Aikin Titin Abuja Zuwa Kano
  • Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal
  • Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano