2025-11-15@09:25:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1805

«bayanai masu»:

    Babban taron dandalin kafafen yada labarai na kasashe masu tasowa da kwararru na kawancen Sin da Afirka da aka bude a jiya Alhamis a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu, zai lalubo hanyoyin karfafa hadin gwiwa, da fadada yin magana da murya daya a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma habaka gudanar da tsarin shugabancin duniya na bai-daya. Wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da Tarayyar Afirka (AU) da kamfanin Independent Media na kasar Afirka ta Kudu da sauran abokan hulda suka shirya, taron na kwanaki biyu ya samu halartar wakilai sama da 200 daga kafofin watsa labarai fiye da 160, da kungiyoyin kwararru, da hukumomin gwamnati da sauran cibiyoyi daga kasar Sin da kasashen Afirka 41, da...
    Kwanan baya, firayim ministan Japan Takaichi Sanae ta yi ikirari a fili cewa, “lamarin Taiwan lamari ne na Japan”, kuma tana da alaka da aiwatar da ikon kare kai na gama kai, inda a karon farko hakan ya nuna tsoma baki cikin batun Taiwan ta hanyar amfani da makamai, kuma a karon farko ya yi barazanar yin amfani da karfin tuwo kan kasar Sin. Kalaman Takaichi game da Taiwan sun tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma sun saba wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin asali na dangantakar kasa da kasa, da lalata tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, kana sun saba wa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” da ruhin takardu hudu...
    Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa ci gaba da cin ganda da ake samu daga fatar shanu na barazana ga masana’antar fata ta Najeriya wadda darajarta ta kai kusan Dala biliyan biyar. Yayin jawabi a taron ƙaddamar da yaƙi da cin ganda da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja, Darakta-Janar na Hukumar Bincike da Ci gaban Kayan Masana’antu, Farfesa Nnanyelugo Ikemounso, ya ce wannan dabi’a tana hana masana’antu na cikin gida samun muhimman kayayyakin da ake buƙata wajen samar da fata da kuma fitar da ita ƙasashen waje. Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Ikemounso ya ce kasuwar kayan fata ta Najeriya...
    Rasha, China, da wasu kasashen Larabawa da dama sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yaki da kuma rashin wani muhimmin matsayi ga Hukumar Falasdinu bayan yakin Gaza da aka gabatar a daftarin kudirin shirin tsagaita wuta na Shugaba Donald Trump na Amurka. Duk da cewa jami’an diflomasiyyar kasashen sun yarda cewa tattaunawa ta kai ga cimma yarjejeniyar, amma rarrabuwar kawuna tsakanin Washington da wasu membobin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya, bayan fiye da shekaru biyu na kisan kare dangi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce ya kamata a amince da kudurin nan take, yana mai jaddada bukatar gaggauta amincewa da shirin. Daftarin farko na Amurka, wanda aka rarraba a makon da ya gabata, ya yi...
    Tehran ta yi Allah wadai da sanarwar da kasashen gungun G7 suka fitar kwanan nan, wadda ta amince da matakan da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana zarge-zargen kin jinin Iran dake kunshe a cikin sanarwar karshe ta gungun kasashen da suka hada da (Faransa, Amurka, Kanada, Japan, Burtaniya, Italiya, da Jamus), a matsayin “marar tushe, kana mai cike da karairayi.” Baghhai ya yi ikirarin cewa yunkurin Amurka da Tarayyar Turai na mayar da takunkumin kai tsaye daidai yake da amincewa da wani laifi na kasa da kasa. Da yake sukar kasashen kungiyar...
    Portugal ta shiga wasan ne da kwarin gwiwar cewa nasara za ta tabbatar mata da gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka, Kanada da Mexico. Sai dai kwallaye biyu na Troy Parrott suka tarwatsa burinsu a Dublin. Duk da haka, Portugal har yanzu tana saman rukunin F da maki biyu a gaban Hungary, kuma za ta iya kammala tikitin shiga gasar idan ta doke Armenia a ranar Lahadi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4 November 13, 2025 Wasanni Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25 November 13, 2025 Wasanni Nijeriya Za...
    Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici. Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta bari wasu kasashe su raba kawunansu, ya kuma bayar da tabbacin cewa; duk da kalubalen da ake fuskanta, Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa mai girma da kuma ci gaba da samun hadin kai. Har ila yau, Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Abubakar Danbazau, a jawabinsa ya bayar da shawarar cewa; dole ne a magance matsalar rashin tsaro, matsalolin fatara, sauyin yanayi, rashin aikin...
    Wasu Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna sun lalata tare da kona wani masallaci da ke gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Falasɗinu (WAFA) ya ruwaito a ranar Alhamis. WAFA ya ce Yahudawan sun kuma yi rubuce-rubucen batanci a bangon masallacin da ke cikin wani ƙauye a arewa maso yammacin yankin, da safiyar ranar. HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani Wasu kafafen yaɗa labarai kuma sun ce rubuce-rubucen da aka fesa da fenti sun haɗa da cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) da harshen Ibrananci. Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana gudanar da bincike kan zargin. Babu rahoton rauni...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk shekara bayan girbin damina, ana sa ran manoma su ci gaba da noma a lokacin rani domin tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arziki. Sai dai hakan na fuskantar kalubale da dama da ke hana yawancin manoma shiga noman rani.   Kamar yadda masana suka sha bayyanawa, akwai dalilai da dama dake hana manoma shiga noman rani a duk lokacin da aka ce damina ta tattara inata intat. Shin ko wadanne kalubale ne ke hana manoma shiga noman rani bayan damuna ta wuce? NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar...
    Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Comoros Azali Assoumani, sun aika wa juna sakon taya murnar cika shekaru 50 da kulla alakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. A cikin sakonsa, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, yana mayar da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Comoros, kuma yana son hada hannu da shugaba Azali, da amfani da cikar alakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu shekaru 50, a matsayin wata dama ta ciyar da dangantakarsu ta gargajiya gaba, da ma inganta tabbatar da nasarorin da aka cimma a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), da bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Comoros bisa manyan tsare-tsare, da kuma...
    Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila da Dr Abdullahi Umar Ganduje, sun ziyarci zauren Majalisar Wakilai ranar Alhamis domin shaida sauya sheƙar ƴan majalisa biyu daga NNPP zuwa APC. Ƴan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Hon. Abdulmumin Jibrin, wanda ke wakiltar Kiru/Bebeji a Kano, da Hon. Sagir Koki, wakilin Kano Municipal. A cikin wasiƙunsu da Kakakin Majalisar Abbas Tajudeen ya karanta, sun bayyana rikici mai sarƙakiya da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar NNPP a matsayin dalilin barin jam’iyyar zuwa APC. ADVERTISEMENT Duk da jayayya da Hon. Kingsley Chinda daga bangaren marasa rinjaye, wanda ya dage wajen ɗaga batun sanarwar a lokacin...
    Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa da taron NIQS karo na 31 da kuma babban taron cibiyar na kasa. Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle Nzekwe, wanda ya bayyana cewa, Cibiyarsa tana bai wa gwamnati shawarwari amma ya nanata cewa, alhakin gwamnati ne ta ɗauki mataki da kuma daidaita kuɗin...
    1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo  Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari a gaba. Ko da yake ƙungiyar sau da yawa tana saumn rinjayan samun kwallo da kirkirar damar kai hari, amma kash suna gaza amfani da waɗannan damarmaki zuwa nasara. Wanda hakan yake nuna rashin ‘yan wasa masu ƙwarewa da zasu ci kwallon, wanda ya sa ake dogaro da wanda suka kwana biyu kamar Rabiu Ali, yana iya kokarinsa amma ba aikinsa ba ne kuma tsufa...
    Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta fitar da wani rahoto da shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya fitar da a ciki yake tabbatar da cewa, Iran tana aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Rahoton dai ya kunshi cewa, tun bayan yarjejeniyar birnin Alkahira na kasar Masar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran da kuma shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa Refael Grossy, Iran din ta yi aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Grossi ya rubutawa Iran wasika a ranar 7 ga watan Nuwamba na 2025 yana mai cewa; Bayar da dama ga hukumar domin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a cikin Iran, yana...
    Wani babban ɗan Kasuwar Singa da ke Jihar Kano, Alhaji Salisu Abdullahi, ya ce ya yi asarar kaya da kuɗinsu ya haura Naira miliyan 120 a gobarar da ta auku da safiyar ranar Alhamis, wadda ƙone shaguna da yawa. “An kira ni da misalin ƙarfe 6 na safe, na garzaya zuwa kasuwa, sai kawai na tarar komai ya ƙone. “Na karɓi kaya bashi a makon da ya gabata domin ci gaba da sayarwa. Yanzu ban san ta yadda zan tunkari masu kayan ba,” in ji shi. Gobarar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 5 na Asuba, ta ƙone shaguna 44 da dukiya mai tarin yawa. Hukumar Kashe Gobara Jihar Kano, ta ce gobarar ta samo asali ne daga matsalar wutar...
    Tawagar matan Najeriya ’yan ƙasa da shekaru 20, Super Falconets, ta lashe gasar Yammacin Afirka ta bana WAFU B U-20, bayan ta doke Black Princesses ta Ghana da ci 3-0 a wasan ƙarshe da aka buga a safiyar Talata. An fafata wasan ne a filin Stade Omnisports da ke Jamhuriyar Benin, inda Akekoromowei, Alaba Olabiyi da Ramotalahi Kareem suka zura ƙwallaye uku da suka bai wa Najeriya nasara. An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo Wannan shi ne karo na farko a tarihi da Super Falconets ke lashe wannan kofin tun lokacin da aka fara gasar. Ghana, wadda ta lashe kofin a shekarar...
    Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. A cewarsa, wannan mataki na daga cikin jajircewar gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma bunkasa ci gaban al’umma musamman a yankunan karkara. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, aikin na nuna kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da karin samun wutar lantarki, kara habakar tattalin arziki,...
     A yau Laraba ne aka sanar da zaman Iran memba a cikin wannan kungiyar ta ( ISKO) wacce aka bude reshenta a cikin kasa tun a 2011. Farfesa Rahmatullah Fattahi ne ya bude reshen kungiyar ta ” Ilimomin Tattara Bayanai Da Kere-Kere” wacce kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa 2019. An sami tsaiko a yadda kungiyar take tafiyar da ayyukan nata, saboda bullar Korona, amma ta ci gaba da aiki a karkashin wani tsari na musamman  ( IranDoc.). Aikin wannan cibiyar shi ne tsara gudanar da nazarori da bincike na ilimomi mabanbanta da kuma hana yin maimaici akansa. A halin yanzu da akwai mutane 20 da suke aiki a karkashin wannan kungiyar daga asalin su 20...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12, 2025 Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12, 2025 Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025
    Laftanar Janar Shaibu ya bayyana cewa, bayanin da ya yi wa Shugaban Kasa, ya yi ne kan sakamakon rangadin aikinsa na yankin Arewa maso Gabas da kuma sabbin bayanai kan yanayin tsaro a fadin kasar.   “Na zo ne domin in yi masa bayani kan sakamakon ziyarar da na kai yankin Arewa maso Gabas sannan da kuma bitar wasu yanayin tsaro a fadin kasar, wanda hakan ya gamsar a wannan lokacin,” in ji Babban Hafsan Sojan Kasa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina November 11, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Sake Hana PDP Gudanar Da Babban Taronta Na Ƙasa November 11, 2025 Manyan...
    An kama mutane 18 bisa laifin fashi da makami, mutane 28 bisa laifin kisan kai, mutane biyar bisa laifin yunkurin kisan kai, mutane 20 bisa laifin fyade da laifukan da ba su dace ba, da kuma mutane 28 bisa laifin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.   Jami’in ‘Yansandan, ya kara da cewa, daga cikin jimillar kararrakin 120, an gurfanar da mutane 97 a gaban kotu, yayin da ake gudanar da bincike kan 22 a halin yanzu.   Bugu da kari, an ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka yi safarar su amma tuni an hada su da iyalansu.   Jami’in ya kuma nuna wasu kayayyaki da aka kwato a hannun masu laifin da...
    Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan mamayar Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza sau 282 tun bayan aiwatar da ita. Sanarwar ta nuna cewa tun lokacin da aka fara yarjejeniyar tsagaita wuta, an kashe fararen hula 242 tare da raunata wasu sama da 620, wanda hakan ya zama keta dukkan ka’idoji da kudurori na kasa da kasa da aka amince da su. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna Allah wadai da karya wannan yarjejeniya da aka yi akai-akai kuma muna daukar ‘yan mamayar da alhakin sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro da na jin kai. Muna jaddada cewa ci gaba da wannan lamari yana barazana ga yarjejeniyar...
    Gidauniyar Tallafawa Al’umma ta Abba Aliyu Gandu da ke jihar Kano ta bada horo sana’o’in hannu tare da raba tallafin Solar ga al’umma 500. Wannan shi ne karo ba adadi da wannan gidauniyar ta Kogunan Kasar Hausa kuma shugaban hukumar Samarda Lantarki a yankunan Karkara Alhaji Abba Aliyu ta gudanar. An raba kayan Solar guda 500 da kuma kudin fara sana’o’in hannu ga wadanda suka sami horo a karkashin wannan gidauniya. Mataimakin Shugaban wannan gidauniya Suleiman Aliyu Abubakar ya bayyana cewa sama da shekara suna rana kyayyakin sun hada da solar domin kawo karshen matsalar wutar lantarki. Suleiman Aliyu Abubakar wanda ya wakilci MD Abba Aliyu a wajen taron yace Kayayyakin sun hada da fanka da kayan caji da na...
    Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno. A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Litinin, an gudanar da wannan samame ne a ranar 9 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ’yan ta’adda suna garkuwa da fararen hula a kan hanyar Buratai–Kamuya. Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi Sojojin Bataliyar Musamman ta 135 da ke ƙarƙashin...
    Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno. A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Litinin, an gudanar da wannan samame ne a ranar 9 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ’yan ta’adda suna garkuwa da fararen hula a kan hanyar Buratai–Kamuya. Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi Sojojin Bataliyar Musamman ta 135 da ke ƙarƙashin...
    Wannan faɗa na daga cikin mafi muni a watannin baya-bayan nan, yayin da ƙungiyoyin biyu ke fafatawa kan ikon hanyoyin kamun kifi, da hanyoyin fasa ƙwauri a yankin Tafkin Chadi. Masana harkokin tsaro sun bayyana damuwa cewa ISWAP na iya kai farmakin ramuwar gayya a makonni masu zuwa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika November 11, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina November 11, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano November 10, 2025
    A kasar Lebanon an sanar da sakin dan tsohon shugaban kasar Libya, Hannibal bisa kudin fansa da sun kai dala 900,000. An tsare dan gidan Kaddafi din ne bisa tuhumarsa da boye bayanai masu alaka da bacewar Sayyid Musa As-Sadr da abokan tafiyarsa, wanda tsohon shugaban kasar ta Libya yake da hannu. Majiyar tsaro da kuma ta shari’a a kasar Lebanon ta bayyana cewa; An saki Hannibal ne bayan da aka kammala dukkanin matakan sharia,sannan aka bai wa gidan kurkukun da ake tsare da shi, umarnin su bude kofa ya fita. Tun a ranar 17 ga watan Oktoba ne dai wata kotu ta amince da a sake shi, bisa cewa zai bayar da dala miliyan 11, sai dai kuma daga...
    Gidauniyar Sarkin Musulmi kan Zaman Lafiya da Ci-gaba ta bayar da tallafin kayan da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.3 domin tallafa wa makarantun Jihar Kebbi. Kayan da aka bayar sun haɗa da kujeru da teburan karatu da aka samar karkashin shirin gidauniyar, domin rabawa makarantun jihar a matsayin gudummawa don inganta yanayin ilimi. Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya samu rakiyar Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera ya miƙa kayan ne a hukumance a ranar Litinin ga Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, a Bulasa Warehouse da ke kusa da Birnin Kebbi. Sarkin Argungu, wanda ya yi jawabi a madadin Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa wannan kyauta na cikin manufofin Gidauniyar Sarkin Musulmi na inganta ilimi da...
    Ƙungiyar Tsofaffin Sojoji ta Najeriya ta bukaci gwamnati da ta ɗauki matakai na gaggawa wajen inganta rayuwar mata zawarawan sojojin da suka mutu a bakin aiki tare da ba su goyon bayan da ya dace. Sabon shugaban ƙungiyar a Jihar Bayelsa, Mista Baratuaipre Allison-Alamini, ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan rantsar da shi. Ya yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙari ganin cewa muryar zawarawan sojojin da suka rasu ta isa inda ya kamata, ta yadda za a inganta rayuwarsu da kuma tabbatar da samun tallafin da suka cancanta. Allison-Alamini ya kuma sha alwashin ba da muhimmanci ga walwalar tsoffin sojoji a jihar, tare da gode wa mambobin ƙungiyar bisa yadda suka ba shi amanar shugabanci. Wani mutum ya...
    Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a tabbatar da abin da ya jawo mutuwarsa ba. Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ta ce an miƙa batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike. Wasu majiyoyi daga cikin gidan karuwan sun bayyana cewa wani ma’aikacin otal ɗin da ke kula da...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi gwamnatin tarayyar Nigeria da ta wanke ‘yan Ogoni 9 ta fuskar shari’a, bayan gushewar shekaru 30 da zartar musu da hukuncin kisa. “Ya Ogoni 9 da su ka hada da fitaccen marubuci Ken Saro Wiwa sun kasance masu fafutukar kare muhalli daga gurbata shi da kamfanin man fetur na Shell yake yi. Wannan kiran daga kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ya zo ne a daidai lokacin da ake bude taron kare muhalli na duniya a kasar Brazil. Shugaban kungiyar ta “Amnesty International” a Nigeria, Isa Sunusi ya bayyana cewa; Duk da cewa afuwar da gwamantin ta yi musu ci gaba ne,amma  masu rajin kare muhallin na...
    Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baghaei yayi tir da Amurka game da rashin kyakkawar nufi ko muhimmantar da tattunawa da ake Magana akai, yace sanarwar da shugaban Amurka trump ya fitar a baya bayan nan na amicewa da hannu Amurka wajen kai mata hari ya nuna cewa ta ma shiga cikin harin soji da aka kai mata. Kakakin yayi suka mai tsananin ga kamalan da shugaban Amurka  yayi dake tabbatar da hujjoji dake nuna cewa yana da hannun dumu dumu wajen kai mata harin soji,  wannan yana daya daga cinkin bayyanannun hujoji  dake tabbata da taka rawar Amurka wajen kai mata hari. Haka zalika ya nuna cewa iran ta mikawa kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya wadannan kalaman...
    Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa. Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa gyare-gyare, inda ya ce ya yi matuƙar kewar filin da kuma magoya bayan ƙungiyar ta Catalonia. An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP ’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, ɗan wasan mai shekaru 38 ya ce: “Na yi kewar wannan fili ƙwarai. Ina fata wata rana zan...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanya da kudinta ya kai Naira Biliyan 14 a Karamar Hukumar Malam Madori, wanda ke nuna jajircewar gwamnatinsa wajen bunkasa ababen more rayuwa1 karkashin shirin sabunta kudurori na gwamnatin tarayya wato “Renewed Hope Agenda.” A yayin taron kaddamarwar, an kuma gabatar da sabbin motoci ga shugabannin jam’iyyar APC guda takwas da masu tallata jam’iyyar a mazabar Arewa maso gabashin jihar, wanda Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya dauki nauyi. Wannan mataki na da nufin karfafa hadin kai a jam’iyyar da kuma tallata hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadin jihar. A jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar Sanata Ahmed Malam Madori...
    Rahotanni na cewa rayukan mayaƙa 200 sun salwanta a sanadiyyar wani rikicin cikin gida tsakanin ’yan ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Nijeriya. Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa rikicin ya ɓarke ne a yankin Dogon Chiku, kusa da Tafkin Chadi, a ranar Lahadi. ’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shi Bayanai sun ce wannan dai na daga cikin rigingimun da suka fi zafi tun bayan da ɓangarorin suka yi hannun riga saboda saɓanin ra’ayi a shekarar 2016. Wani ɗan sa-kai da ke taimaka wa dakarun Nijeriya wajen sa ido kan lamurran tsaro, Babakura Kolo, ya ce...
    Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana  mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.” Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira       ” Nuna wariya ta kabilanci.” Har ila yau Chiroma ya fada wa mahukuntan kasar cewa; “Al’ummar Kamaru ba su son su, kuma sun dawo rakiyarsu.” A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar, Chiroma ne ya zo na biyu bayan Paul biya a bisa kididdigar hukumar zaben kasar. An bayyana cewa Biya ya sami kaso 53.66%, yayin da Chiroma ya sami kaso 35.19%. Shi dai...
    Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon ya ambaci cewa,  Mutum daya ya kwanta dama, sadaniyyar harin wani jirgin sama maras matuki na HKI akan wata mota a garin al-yasariyyah,dake gundunar Saida, a kudancin kasar. Majiyar tsaro ta fada wa kafafen watsa labaru cewa, jirgin saman maras matuki ya harba makamai masu linzami guda 3 ne akan motar da hakan ya yi sanadiyyar konewarta baki daya. Dama dai ma’aikatar lafiya ta Lebanon din ta sanar da shahadar wasu mutane biyu sanadiyyar hare-hare biyu da Isra’ilan ta kai a kudancin kasar, a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata. Tun da aka tsagaita wutar yaki a watan Nuwamba 2024, HKI take ci gaba da keta ta, ya kai dubbai. A wani labarin daga...
    Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.   “A yau, a cikin nuna goyon baya, dubban ‘yan mazaɓarmu a garinmu na Ƙofa, Bebeji, Kano sun yi min maraba sosai. Taron ya tabbatar barinmu jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya, zuwa APC, da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a kan mulki,” in ji Jibrin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025...
      Ya ƙara da cewa, binciken yankin ya haifar da gano wasu gine-ginen ‘yan ta’adda guda 11 da kuma ceto waɗanda aka sace 86, waɗanda suka haɗa da maza, mata da yara.     A wani samame makamancin haka, sojojin da aka tura Mangada, sun kama masu samar da kayayyaki ga ‘yan ta’adda su 29 a kan hanyar Chilaria dauke da kayayyaki da dama.   Abubuwan da aka kwato daga gare su sun hada da motocin daukar kaya guda biyu da babura masu kafa uku (Keke-napep) dauke da Man fetur, kimanin lita 1,000 a cikin jarkuna, galan hudu na man injin, sabbin tayoyi biyu na motar da ake kafa bindiga, tarin kayan magunguna, da kayan abinci da kayan masarufi.  ...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, wata biyu bayan jam’iyyar NNPP ta dakatar da shi. A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar da sauya sheƙarsa tare da magoya bayansa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da goyon bayan neman wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu a zaɓen 2027. Abdulmumin Jibrin ya sanar ta shafinsa cewa sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawar al’ummar mazaɓarsa. “Na samu kyakkyawar tarba daga dubban al’ummar mazaɓata ta Kofa, Bebeji, da ke Jihar Kano. “Taron ya yi ittifaƙin ficewa daga NNPP/Kwankwasiyya, mu koma APC, tare da goyon bayan Shugaba Tinubu ya yi wa’adi na biyu. An ƙara rage kuɗin aikin Hajjin...
    An ƙara rage kuɗin kujerar aikin hajjin bana zuwa aƙalla Naira miliyan 7.5 ga maniyyata daga jihohin Arewacin Nijeriya. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai. Ya ce an rage kuɗin ne sakamakon umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na yin hakan da kuma tattaunawar da suka yi ta baya-bayan nan da kamfanonin Saudiyya. A ƙarƙashin sabon farashin yanzu jihohin da ke shiyyar Borno/Adamawa za su biya Naira 7,579,0202 maimakon Naira 8,327,125 da hukumar ta sanar a baya. Mahaifiyar Minista Balarabe Lawal Abas ta rasu NAJERIYA A YAU: Dalilan Yaɗuwar Cututtuka A Irin Wannan Lokaci Sauran jihohin Arewa kuma sabon farashinsu shi ne Naira 7,669,769 maimakon Naira 8,457,685 da aka sanar da...
    Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar. Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani. Ranar Foliyo Ta...
    Dong ta danganta raguwar farashin na PPI da aka samu a mizanin shekara-shekara bisa karuwar yawan sarrafa kaya a manyan masana’antu, da hanzarta kokarin kafa masana’antu na zamani, da kuma bude hanyoyin sayayyar kayayyaki. A watan Oktoba, ci gaban da aka samu na karuwar hada-hadar kaya da bukatarsu ya haifar da hauhawar farashi a wasu sassa kamar masana’antar hakar kwal da sarrafa shi, kamar yadda Dong ta bayyana, yana mai nuni da cewa su ma sauye-sauyen farashi a kasashen duniya sun shafi farashin wasu kayan masana’antun cikin gida. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki November 8, 2025 Daga Birnin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko November 8, 2025 Wasanni Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax November 6, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2, 2025
    Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Sama’ila Bagudo, ya kuɓuta bayan shafe fiye da mako guda a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi. Aminiya ta ruwaito cewa an sace mataimakin shugaban majalisar ne a ranar Juma’a 31 ga Oktoba, 2025, jim kaɗan bayan ya kammala sallar la’asar a masallacin garinsu na Bagudo. ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu Sakataren gwamnatin jihar, Yakubu Tafida, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Asabar. Bayanai sun tabbatar da cewa lamarin na zuwa ne daidai da lokacin da aka gudanar da addu’o’in haɗin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci domin neman zaman lafiya...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa  November 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi November 8, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne November 8, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi November 8, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne November 8, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025
    Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Taekwando na kasar Iran mai suna Abulfazl zandi ya zamo shi ne na daya a duniya a bangaren maza a ma’aunin kilograme 58, bayan yayi nasarar samun lambar yabo ta zinariya a gasar taekwando ta duniya a kasar China, Hukumar kula da wasan taekwando ta duniya ta fitar da sunayen wadanda suka yi fice a duniya a watan nuwamba, inda ta sanya gasar teakwando ta duniya da aka yi a kasar china , yan wasan kasar Iran da dama maza da mata sun samu gagarumin ci gaba a jerin fannonii daban daban na wasanni. Zandi  ya zo na daya a duniya  da maki 170.80  kuma yana mataki na 4  a bangaren Olympic, A gefe...
      Sunana Abdulhamid Ado (Danbayaro): Inna lillahi wa inna ilaihirraju’un. Na ji ba dadi na ji komai sai da ya tsaya min har tsahon lokaci, abun ba zai musaltuba, sai dai kawai mu ce Allah ya ji kan Mal. Nata’ala. Mutum ne mai barkwanci, ga zumunci na gaske, ba a yin gulma da shi, baya boye wa mutum gaskiya, kuma baya cin hakkin mutum, kuma abun hannusa baya rufe masa ido. Kuma indai ya samu abun duniya ko baka sani ba sai ya kira ka an ci da kai, harkar sa ba bakin ciki yana da hali mai kyan gaske. Wata rigar san yi da ya kawo mana ‘location’ ya raba mana dukkan ‘crew’ sai da ya bamu, ina ganin...
    Ministan harkokin wajen kasar Ukraine ne ya bayyana cewa da akwai ‘yan asalin kasashen Afirka 1,400 da suke cikin rundunonin Rasha suna tayata yaki. Ministan harkokin wajen kasar ta Ukraine, Adriy Sabiha ya ce; Moscow tana jan hankalin ‘yan Afirka akan su rattaba hannu akan wata yarjejniyar aiki, wacce take daidai da yankewa kansu hukuncin kisa. Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar na Ukraine, ya rubuta a shafinsa na X cewa; ‘yan kasashen wajen da ake dauka a cikin sojojin Rasha, ana aike su zuwa inda za a yi saurin kashe su.” Jami’an gwamnatin kasar ta Ukraine sun sha yin kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su hana ‘yan kasarsu yi wa Rasha aikin soja da hakan yake da...
    A yau Asabar ne jirgin  kasa na dakon kaya na farko daga Rasha ya iso tashar jiragen ruwa ta “Abrin” na Iran. Zuwan jigin kasan dai yana a karkashin bunkasa alakar kasuwanci ne a tsakanin Iran da Rasha.  Jirgin kasan yana dauke ne da hajar kasuwanci saboda kasuwannin Iran da kuma Iraki, yana kuma dauke da kwantena 62 masu girman kafa 40.  Shi dai wannan jirgin kasan ya taso ne daga wani yanki mai nisan kilo mita  900 daga Arewacin birnin Moscow, ya kuma ratsa ta kasashen Kazakhstan da Turkmenistan, sannan ya shigo Iran. Kwanaki 12 jirgin ya dauka akan hanya kafin a karshe ya yada zango a cikin Iran. Gabanin tashin jirgin, sai an cimma yarjeniya da kasashen da...
    “Lamarin daya kai miliyan daya na wadanda suka nemi a basu bashin karatu, lalle abin ya nuna a gaskiya matasa sun son su kyautata yadda rayuwarsu data wasu zata kasance a gaba, musamman ma yadda suka maida hankali wajen neman ilimi. Ya ci gaba da bayanin “Wannan yana nunawa a fili yadda jagorancin na Shugaban kasa Bola Tinubu ya damu da lamarin ilimi domin shi ne ginshikin ci gaban al’umma kamar yadda ya ce,”. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ilimi Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu October 18, 2025 Ilimi Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma October 18, 2025 Ilimi Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi tsokaci kan yadda bangaren shari’a na Turkiyya ya bayar da sammacin kama Netanyahu fira ministan Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yaba da fitar da sammacin neman kama jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila 37, ciki har da shugaban gwamnatin mamayar, Netanyahu mai aikata laifukan yaki, da ministocin tsaro Gallant da Katz. A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Juma’a, kungiyar ta ce wannan matakin “ya tabbatar da matsayin al’ummar Turkiyya da shugabancinsu, wadanda suka jajirce kan kyawawan dabi’un adalci da dan Adam, da kuma ‘yan uwantaka da ke tsakaninsu da al’ummar Falasdinawa da ake zalunta.” Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: “Al’ummar Falasdinawa na ci gaba da fuskantar mummunan yakin kawar da...
    A yau Juma’a ne dai masu shigar da kara a Tanzania su ka gabatar da tuhumar mutane da dama da zargin cin amanar kasa, saboda rawar da su ka taka a cikin rikicin zaben shugaban kasa.  Mutane 76 ne aka tuhuma da cewa; Sun yi kokarin kawo cikas akan zaben da aka yi a ranar 29 ga watan Oktoba da kuma tsokanar mahukunta a birnin Darussalam. Baya ga laifin cin amanar kasa,ana kuma tuhumar mutanen da cewa sun kitsa aikata laifuka. Zaben da aka yi a kasar Tanzani a karshen watan Oktoba, ya bar baya da kura saboda tashe-tashen hankulan da aka samu. Babbar jam’iyyar adawa ta Chadema ta yi zargin cewa an kashe mutane fiye da 1,000,kuma a halin...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birni Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassa Abu Turabi Fard, ya bayyana cewa; Tsayin dakar da kungiyar Hizbullah ta Lebabon da Ansurllah na kasar Yemn da kuma al’ummar Iran su ka yi wajen fada da masu girman kai na duniya, sakamako ne na koyarwar alkur’ani maigirma, Ahlul Bayt ( a.s) da kuma Ashura da jagorar matan duniya Fatima az-Zahra ( a.s). Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya ambato limamin na birnin Tehran yana kuma cewa; Makarantar gwgawarmaya tana yi wa zuriya bayan zuriya tarbiyya akan riko da gaskiya da kuma kalubalantar masu danniya. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name*...
    Tarayyar turai ta bayyana cewa ma’aikatan Agaji ba za su iya isha cikin garin Al-fahar ba,kuma birnin ya zama tamkar makabarta. Tarayyar turai din ta  bakin mai Magana da yawunta Eva Herneserova ta kuma ce; Sudan ta zama daya daga cikin kasashen da gudanar da ayyukan agaji ya tsananta a duniya,kuma har yanzu da akwai fararen hula da aka killace su adaidai lokacin da ake ci gaba da kai wa asibitoci hare-hare. Eva Herneserova ta kuma ce; Babu sauki ko kadan a kokarin shiga cikin birnin domin isar da kayan agaji. Ma Magana da yawun kungiyar tarayyar turai din ta kuma yi gagradi akan cewa bai kamata a rika amfani da yunwa da kuma kisan kiyashi a matsayin makamin yaki...
    Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano. Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale. Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar. “A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar...
    “A yayin da ake tarwatsa masu kai harin, DPO na Sassan A da B sun tura ma’aikatansu suka harba hayaki mai sa hawaye, amma wasu motoci cikin motar gwamnan sun lalace,” in ji Abiodun. Ya bayyana cewa mutane uku na farko da ake zargi sune Ali Mohammed da Adamu Hussain, dukkansu daga yankin Nasarafu, Bida, da Isah Umaru na yankin Darachita, Bida. Ya kara da cewa an kama Nagenu, mai shekaru 39, daga yankin Bello Masaba, daga baya dangane da wannan lamari, sannan ya ambaci wasu biyu, Salihu Mohammed da Abdulrahman Baba, yayin tambayoyi. “Dukkan wadanda ake zargi suna karkashin bincike kuma suna taimaka wa ‘yansanda wajen gano wasu. Ana ci gaba da kokarin kama karin mutane da ake zargi,”...
    Yau 7 ga watan Nuwamba, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Paul Biya murnar yin tazarce a wani sabon wa’adin shugabancin kasar Kamaru. Shugaba Xi ya ce, kasar Sin da Kamaru suna da daddadiyar alaka mai kyau. A cikin ‘yan shekarun nan, amincewar siyasa tsakanin kasashen biyu ta kara zurfafawa, kuma an samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban na hadin gwiwa, tare da mara wa juna goyon baya a kan batutuwan da suka shafi muradunsu da kuma batutuwa masu muhimmanci. A shekara mai zuwa ce za a cika shekaru 55 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Kamaru, matakin da ya samar musu da sabbin damammaki na ci gaban huldarsu. Xi yana dora muhimmanci sosai kan ci...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump November 7, 2025 Manyan Labarai Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari  November 7, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT November 6, 2025
    Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na shiyyar Abuja (AEDC) ya fara aikin rage ma’aikata kusan 800, a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da fama da hauhawar farashi, tsadar rayuwa, da rashin tabbas wajen samun wutar lantarki. Matakin korar wanda ta fara a ranar Laraba, ya biyo bayan watanni na sake fasalin cikin gida a kamfanin da ke ba da wutar lantarki ga Babban Birnin Tarayya Abuja da jihohin Kogi, Neja da Nasarawa. Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah Majiyoyi da dama da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa shugabannin kamfanin sun fara ne da shirin korar ma’aikata 1,800, kafin su rage...
    Muhimmin fadakarwa daga Sayyid Muqtada al-Sadr kwanaki kafin zaɓen kasar Iraki Malamin Tafarkin Shi’a na Iraki Muqtada al-Sadr ya umurci magoya bayansa a ranar Alhamis da su dakatar da duk wani zaman dirshan da zanga-zanga har zuwa lokacin zaben ‘yan majalisa dokokin kasar mai zuwa. A cikin wata sanarwa, ofishin al-Sadr ya ce ya yi nazari kan ayyukan da suka hada da tarurrukan kabilanci da na matasa da ke goyon bayan shawararsa ta kauracewa zaben kuma ya yi tsokaci, “Daga yanzu har zuwa ranar zabe, babu bukatar wani karin zanga-zanga.” Wannan shawarar ta ci gaba da tsarin al-Sadr na nisantar da kansa daga tsarin zaben tun bayan sanarwarsa a watan Yunin shekara ta 2022 na janye kansa gaba daya daga...
    Wani sabon kudiri da ke gaban Majalisar Dokokin Amurka ya nemi a hana ’yan kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah da Miyetti Allah Kautal Hore bizar shiga Amurka. Kudurin, wanda dan majalisa Christopher Smith ya gabatar a ranar Talata, ya kuma bukaci kwace kadarorin mambobin kungiyar. An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin Amurka ke ɗauka don dakile abin da ta kira take hakkin ’yancin addini ga Kiristocin Najeriya. Kudirin dai na neman hukunta mutane da ƙungiyoyi da ke da hannu ko goyon baya wajen take hakkin ’yancin addini mai, a ƙarƙashin dokar kasa da kasa ta IRFA. Christopher...
    Osimhen, wanda ya koma Galatasaray daga Napoli, ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarorin ƙungiyar ta ƙasar Turkiyya, ciki har da lashe kofin ƙalubale. A yanzu haka, shi ne ɗan wasan da ya fi ci wa Galatasaray ƙwallaye a dukkanin da ta ke bugawa a bana, ya bar sauran fitattun ’yan wasa irin su Leroy Sane da Mauro Icardi a baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2, 2025 Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025
    Li Chenggang, wakilin cinikayyar kasa da kasa na ma’aikatar kasuwanci kuma mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, ya gana da tawagar cinikayyar kayan noma ta Amurka a birnin Beijing a jiya Talata 4 ga watan Nuwamb, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, da cinikayyar kayayyakin noma, da sauran batutuwa masu alaka. Li Chenggang ya bayyana cewa kyakkyawar alaka ta tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka tana da alfanu ga kasashen biyu da kuma duniya baki daya. Tun daga watan Mayu na wannan shekarar, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na bangarorin biyu sun tattauna har sau biyar bisa jagorancin muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda...
    Ana fargabar cewa wasu yara biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan faɗawa rijiya a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dala da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu A cewarsa, tsautsayin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 8:53 na safiyar ranar Talata a ƙauyen Kashirmo da ke yankin Sarkakiya na Dawakin Tofa, inda wata yarinya mai shekara takwas mai suna Zara’u Muhammad ta faɗa wata rijiya da ke kusa da gidansu. Duk da ƙoƙarin jama’a na...
    Kungiyoyin da suka yi hadin gwiwar shigar da karar sun hada da Interfaith Partners for Peace and Development, Fityanul Islam of Nigeria, Sairul Qalbi Foundation, Tijjaniyya Youth Enlightenment Initiative, Hablullahi Mateen Foundation, Dariqa Qadiriyya of Nigeria, Kadiriyya Youth Awareness, Kadiriyya Riyadul Janna Kofar Na’isa, Ashabul Kahfi Foundation, da Majmau Ashabul Yameen.   LEADERSHIP ta ruwaito cewa, takaddamar da ta shafi Malam Lawan Triumph ta fara ne a watan Satumba bayan da wasu ƙungiyoyin addini suka ɗauki wasu wa’azozinsa a matsayin ɓatanci ga Annabi SAW, wanda ya haifar da cece-kuce da muhawara a faɗin jihar. Wannan lamari ya sa gwamnatin jihar ta shiga tsakani ta hannun Majalisar Shura ta Jiha, wadda aka ba da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen.  ...
    Kamfanin dillanacin labarun Faransa ya ambato wata majiyar shari’a tana cewa; ‘yan jaridar da aka kama su ne; Ibro Shu’aibu na gidan talbijin din Sarauniya, sai Yusuf Sariba na wani Shafin watsa labaru na  Niger Ecoh da kuma Umaru Kano na jaridar “Errison.” Dukkanin ‘yan jaridar uku an kai su kurkukun Kolo wanda yake da nisan kilo mita 50 daga babban birnin kasar Yamai. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai aka kama wadannan ‘yan jaridar da kuma wasu abokan aikinsu. Ana tuhumar ‘yan jaridar da fallasa bayanan gwamnati da shi ne bukatar samarwa da gwamnatin taimakon kudi daga ‘yan kasa. Bayan watsa labarin da aka zargi tashar talabijin din Sarauniya da yi, labarin ya watsu a cikin...
    China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar da Amurka ta yi na janye tallafi da kuma daukar matakin soja kan kasar da ke Yammacin Afirka saboda zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci. A kwanan nan ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar “barazana” a Najeriya, yana mai gargadin cewa Amurka za ta iya tura sojoji idan gwamnatin Najeriya ta gaza dakatar da abin da ya bayyana a matsayin ta’addacin masu kaifin kishin islama. Ya kuma sanar da cewa za a saka Najeriya cikin jerin “kasashen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.” ke sa wa ido. Hukumomin Najeriya dai sun yi watsi da wadannan zarge-zargen, suna bayyana su a matsayin marasa tushe a...
    Zohran Mamdani ya lashe zaben Magajin Garin birni mafi girma a Amurka wato New York, kuma zai zama Musulmi na farko a tarihi da ya taɓa shugabantar birnin. Mamdani, mai shekara 34 kuma dan jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya samu nasara bayan ya motsa masu ra’ayin sauyi a cikin birnin da ma fadin ƙasar, duk da suka daga Shugaba Donald Trump da ‘yan Republican, da wasu ‘yan Democrat masu matsakaicin ra’ayi. Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150 An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump A jawabin nasararsa bayan doke tsohon Gwamna Andrew Cuomo, Mamdani ya ce yana da cikakken goyon baya daga jama’a, kuma ya bayyana...
    Dakta Bukar ya bayyana wannan hadin gwiwar a matsayin abu mai muhimmanci wanda yazo a kan gaba wajen karfafa wayar da kan jama’a game da rawar da sahihan bayanai suke takawa wajen tsara ci gaba da samar da manufofi masu tushe , da dorewar cigaban kasa.   Dakta Bukar, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa da kafafen yada labarai wajen isar da bayanan Hukumar ga al’umma.   A cikin jawabinsa, Kwamishinan yada labarai Malam Ahmed Maiyaki, ya yaba da wannan shiri tare da tabbatar da cikakken goyon bayan Ma’aikatarsa ga manufofin Hukumar.   Yace samar da sahihan da kafa gwamnati mai wacce da dogara da adalci yana daga cikin manifofi da kudirorin gwamnatin jihar Kaduna wanda hakan zai taiama wajen kawo...
    Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka gabata yana fafatawa a gasar World Endurance Championship (WEC) tare da ƙungiyar Jota. Tsohon gwarzon Formula 1 ɗin ya taɓa lashe Gasar Duniya ta Formula 1 a shekarar 2009 tare da ƙungiyar Brawn, kafin ya yi ritaya daga F1 a 2016 — bayan fafatawa a wasanni 306 cikin shekaru 18 na aikinsa, inda ya lashe Grand Prix sau 15.
    Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka gabata yana fafatawa a gasar World Endurance Championship (WEC) tare da ƙungiyar Jota. Tsohon gwarzon Formula 1 ɗin ya taɓa lashe Gasar Duniya ta Formula 1 a shekarar 2009 tare da ƙungiyar Brawn, kafin ya yi ritaya daga F1 a 2016 — bayan fafatawa a wasanni 306 cikin shekaru 18 na aikinsa, inda ya lashe Grand Prix sau 15.
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin nan ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin kasashen da kasarsa ke kara mayar da hankali a kansu, bisa zargin barazanar da ya ce mabiya addinin Kirista na fuskanta a kasar. Trump ya kara da cewa, idan har gwamnatin Najeriyar ta gaza shawo kan kisan Kiristoci, to Amurka za ta hanzarta dakatar da dukkanin tallafin da take baiwa kasar, kana...
    Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon ya bayyana cewa; Gwagwarmaya ta tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila rashin girke sojojinta a kan iyakar da ke tsakanin Isra’ila da Lebanon Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Nabih Berri ya tabbatar da cewa: “Gwagwarmaya ta yi cikakken biyayya ga sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma sojojin Lebanon sun tura sojoji da jami’ai sama da 9,000 a yankin da ke kudancin Kogin Litani.” Ya ƙara da cewa “sojojin suna da ikon tura sojoji a kan iyakokin da ƙasashen duniya suka amince da su tsakanin Labanon da Isra’ila, amma abin da ke kawo cikas ga wannan shi ne ci gaba da mamaye yanki mai girma na kudancin Lebanon da sojojin mamayar Isra’ila suka yi, kamar yadda Rundunar UNIFIL da rahotanninta na...
    Ana ci gaba da tattara gawarwakin mutane da mayakan kungiyar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai DaukinGaggawa suka kashe a jihar Arewacin Kordofan na kasar Sudan. Kungiyar Likitoci na Kasar Sudan ya ruwaito cewa: Ana ci gaba da tattara gawawwakin mutane a Arewacin Kordofan, bayan da mayakan Rappid Support Forces suka farma yankunan a kokarin da suke yi na kwace iko da jihar baki daya. Kungiyar Likitoci ta Sudan ta bayyana cewa, tana bin diddigin manyan laifukan da Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces suke aikatawa kan fararen hula marasa makamai a birnin Bara da ke jihar Arewacin Kordofan. Kungiyar ta tabbatar da cewa: Gawawwaki da dama sun taru a cikin gidaje a cikin birnin, kuma mayakan Rapid...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Dick Cheney, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya. Cheney shi ne mataimakin shugaban ƙasa na 46, wanda ya yi aiki tare da tsohon shugaban ƙasa, George W. Bush a wa’adin mulki biyu daga shekarar 2001 zuwa 2009. An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri A cewar iyalansa, marigayin ya rasu bayan doguwar jinyar da ya yi fama da ita sakamakon ciwon huhu da na zuciya da jijiyoyin jini. Dick Cheney, wanda aka san shi da tsananin ra’ayin mazan jiya, yana daga cikin mataimakan shugabanni mafi tasiri a tarihin Amurka. Ya taka muhimmiyar rawa wajen...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin Tehran da Washington ya samo asali ne daga muradun jama’a, yana mai gargadin cewa duk wani hadin gwiwa da Amurka za a iya cimma shi ne kawai idan ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa Isra’ila, ta kuma janye dukkan sansanonin sojinta daga yankin, sannan ta daina tsoma baki a harkokin Iran. Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya bayyana hakan yayin ganawa da wani rukunin dalibai na kasar a jajibirin Ranar Dalibai ta Kasa wacce kuma ta yi daidai da ranar kasa ta yaki da girman kai na duniya. Jagoran ya bayyana ranar a matsayin “ta tarihi” kuma wani muhimmin bangare...
    Natasha ta bayyana dakatar da ita a matsayin mataki wanda ba na doka ba, tana mai cewa hakan ya nuna yadda tsoro da barazanar siyasa ke rinjayar halayen jami’an gwamnati. An dakatar da Sanata Natasha a watan Maris saboda zargin da ya shafi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, amma ta koma kujerarta a watan Satumba bayan kammala wa’adin dakatarwar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump November 3, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna November 1, 2025 Siyasa Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar October 31, 2025
    Bayan shafe lokaci, wani jami’in hukumar shige da fice ya dawo mata da fasfo ɗinta. Duk da haka, Natasha ta ci gaba da nuna ɓacin ranta. “Da ban yi bidiyon kai-tsaye ba, da ba za su dawo da min fasfo ba.” A halin da ake ciki, ofishin Akpabio da Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ba su fitar da wata sanarwa ba game da lamarin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025 Manyan Labarai Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump  November 4, 2025 Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025
    Ya jaddada cewa gwamnati tana tabbatar da tsaron kowa ba tare da bambanci ba. Kalaman Trump sun haifar da ruɗani da cece-ku-ce a tsakanin ‘yan Nijeriya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025 Manyan Labarai Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi November 3, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025
    Ko da yake ƙungiyar ta yaba da sakin biliyan ₦10.6 ga asusun gidauniyar likitoci masu neman ƙwarewa (Medical Residency Training Fund) (MRTF) na 2025, ta ce biyan ya kamata ya zama na yau da kullum, a buɗe, kuma ya dace da hauhawar farashi. NARD ta kuma yi tir da dawo da wasu daga cikin likitocin da aka kora a Asibitin Koyarwa na Lokoja (FTH Lokoja), tana mai cewa dole ne a dawo da dukkan su ba tare da sharaɗi ba. Sauran matsalolin da ta jero sun haɗa da bashin albashi da ba a biya ba a BSUTH, da FMC Owo, da OAUTHC Ile-Ife, rashin aiwatar da tsarin one-for-one replacement, da kuma matsalar amfani da likitoci ƴan kwangila a asibitoci da...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar a yau Litinin cewa; Jirgin sama maras matuki na HKI ta kai wa wata mota hari a kusa da garin “Sharqiyya”. Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon kuwa ya sanar da cewa; Jirgin sama maras matuki na HKI ya jefa bom a kusa da wata motar Buldoza a garin Khayyam, sai dai babu wanda ya jikkata. Haka nan kuma kamfanin dillancin labarun ya ce; Jirgin saman maras matuki ya jefa wasu bama-baman guda uku akan hanyar Zafta. A cikin kwanakin bayan na HKI tana kara tsananta kai hare-hare a kudancin Lebanon, lamarin da yake nuni da kokarin sake dawowar yaki gadan-daban. Tun bayan tsagaita wutar yaki a Lebanon shekarar da ta gabata HKI...
    An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.” Baƙin da aka gayyata...
    An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.” Baƙin da aka gayyata...
    Sojojin haɗin gwuiwa ta Operation MESA ƙarƙashin Birgediya ta 3 sun kashe ƴan bindiga 19 a ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano, bayan wata musayar wuta mai tsanani da ta faru a yankunan Unguwan Tudu, Unguwan Tsamiya, da Goron Dutse da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Asabar. Wannan sumame ya biyo bayan sahihan bayanan leƙen asiri kan motsin wasu ƴan ta’adda da suka shiga yankin daga maƙwabtan dazuka. A cewar sanarwar Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan hulɗa da Jama’a na Birgediya ta 3, Sojojin tare da jami’an tsaro sun fatattaki ƴan ta’addan bayan musayar wuta, inda aka kashe ƴan bindiga 19, yayin da wasu suka gudu da raunin harbi. Ya ce an ƙwato babura da dama da kuma wayoyi...
    Ofishin Yada Labarai na Gwamnatin Gaza Ismail al-Thawabteh y ace Rundunar sojin Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. al-Thawabteh, darektan ofishin, ya shaida wa kamfanin dinalancin labarai na Anadolu cewa laifukan sun hada da hare-haren da Isra’ila ta kai hana shigar da kayayyakin lafiya, magunguna, tantuna. Jami’in na Hamas ya ce sojojin Isra’ila sun sha ketare “layin da aka shata musu”, suna aika motoci zuwa wuraren zama, suna kai hare-hare ta sama da rusa gidaje, wanda ya haifar da mutuwar fararen hula da raunuka. A cewar ofishin yada labarai, daga ranar 10 ga Oktoba zuwa karshen watan, manyan motoci 3,203 ne kawai suka shiga...
    Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan, Salma Ishaq, ta bayyana cewa Mayakan (RSF) sun kashe mata kusan 300 tare da yi wa 25 fyade a El Fasher, babban birnin Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, a matsayin wani bangare na ayyukan kisan kiyashin da suke aikatawa a yankin. A ranar 26 ga Oktoba, dakarun RSF sun kwace iko da El Fasher kuma sun yi kisan gilla ga fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa. A cikin sanarwar da ta fitar Salma Ishaq, Ishaq ta ce abin da ya faru a El Fasher “ya yi kama da abin da ya faru a El Jeneina a shekarar 2023, amma ba a bankado da kuma yada laifukan...
      Shugaba Xi ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, duniya na fuskantar sauye-sauye irin wadanda ba a taba gani ba kuma cikin sauri. Don haka, kamata ya yi kasashen biyu masu dadaddun wayewar kai su zurfafa koyi da juna, da shigar da sabon kuzari cikin gina cikakken salon hadin kai, bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, kana su tattaro karfin wayewar kai don gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil’adama.   A wani ci gaban kuma, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping wato ministan raya al’adu da yawon bude ido na kasar Sun Yeli, ya halarci bikin bude babban gidan adana kayan tarihin na GEM bisa gayyatar gwamnatin Masar. Kafin bikin, shugaba al-Sisi ya...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025 Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025
      Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu November 2, 2025 Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da...
    Qatar ta bayar da tallafin gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Sudan Gwamnatin Qatar ta aika da agajin gaggawa da tallafin jin kai zuwa birnin Ad-Dabba da ke Jihar Arewacin Sudan domin rage wa dubban mutanen da suka rasa matsuguninsu da ke tserewa daga El Fasher, babban birnin Jihar Arewacin Darfur. Ma’aikatar Harkokin Waje ta Qatar ta bayyana cewa: “Wannan tallafin ya zo ne a cikin tsarin jajircewar Qatar na tallafawa ‘yan uwantaka na Sudan, musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin halin jin kai da fararen hula ke ciki, ciki har da karancin abinci mai tsanani da kuma karuwar bukatar matsugunai da kayan masarufi.” Sanarwar ta kara da cewa wannan tallafin wani bangare ne na kokarin da...
    Shi ma wasan da ta yi nasara a kan kungiyar Sifaniya a daf da za a tashi ta ci kwallon a gasar Zakarun Turai da na Newcastle United a Premier League. Tun daga nan alamomi suka fara bayyana cewar akwai tarin matsaloli a Liberpool, wadda kowanne wasa kwallo ke shiga ragarta in ban da wanda ta yi nasara a kan Arsenal 1-0 a Premier League cikin Agusta da wanda ta ci Burnley 1-0 a cikin watan Satumba a Premier League. Sababbnin ‘Yanwasan da Liberpool ta saya a kakar banamages Giorgi Mamardashbili daga Balencia Jeremie Frimpong daga Bayern Leberkusen, Florian Wirtz daga Bayern Leberkusen, Milos Kerkez daga Bournemouth, Hugo Ekitike daga Eintracht Frankfurt, Aledander Isak daga Newcastle United, Armin Pecsi daga...
    Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya musanta zargin da y ace karce ce ” da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta yi cewa Hamas ta sace wata babbar mota dauke da kayan agaji. “Mun tabbatar da cewa wannan zargin karya ne, kuma wani bangare ne na manufar kafofin watsa labarai da nufin bata sunan rundunar ‘yan sandan Falasdinu, wadanda ke aikinsu na kasa da na jin kai na neman taimako da kare ayarin motocin agaji,” in ji Ismail Al-Thawabta, darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza. Yakara da cewa ba a fayyace ainihin rana, lokaci, da wurin da lamarin ya faru ba, Al-Thawabta ya bayyana bidiyon a matsayin “yunkuri bayyananne na yada bayanai marasa tushe.” Sanarwar ta karyata ikirarin...
    An gudanar da taron tattaunawa na duniya kan kirkire-kirkire da bude kofa da ci gaba na bai daya, jiya Juma’a a birnin Lagos na Nijeriya. Yayin taron wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos suka shirya, ministan kula da harkokin matasa na Nijeriya Ayodele Olawande da shugaban CMG Shen Haixiong, sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo. A cewar ministan na Nijeriya, cikin shekaru 5 da suka gabata, dubban matasan kasar sun ci gajiyar tallafin karatu da shirye-shiryen horo da na musaya da Sin ta samar, kuma wannan hadin gwiwa da ake yi a aikace ya kara fahimta da aminci tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, a shirye ma’aikatarsa...
      Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik.   Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang) ShareTweetSendShare...
    Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar nuna goyan baya ga wani kudiri da ya jaddada cewa shirin da Morocco ta gabatar kan Yammacin Sahara shi ne mafita ‘’mafi dacewa” ga yankin da ake takaddama a kai.   Kudirin ya nuna goyan bayan kasashe mambobin kwammitin ga shirin na Morocco, tare da bayyana cewa ikon masarautar kan yankin zai iya kasancewa mafita mafi dacewa. Kan hakan ne kwamitin yaya kira ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da wakilinsa na musamman kan wannan batu, Staffan de Mistura, da su gudanar da tattaunawa “bisa ga” wannan shirin don cimma yarjejeniya da kowa zai aminta da ita. Aljeriya wacce ta ke kaddama da Morocco kan yankin ta kaurace kada...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u    Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi  ritaya a matakin jiha da  kananan hukumomi. A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati. A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi. Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne...