Leadership News Hausa:
2025-11-15@15:53:37 GMT

Yadda Za Ku Gyara Kanku

Published: 15th, November 2025 GMT

Yadda Za Ku Gyara Kanku

Ki cire kwallon da ke cikin dabino, sai ki hada kwakwa da aya da dabinon, ki markada su waje daya. Bayan haka, ki kawo zuma mai kyau, mai dan yawa da kuma nonon rakumi kamar kofin shayi daya. Ki hada da kwakwar da kika markada da dabino da aya. Ki juya su waje daya sosai har sai sun hadu.

Yadda ake amfani da shi:

Ki adana hadin a wuri mai tsafta, sannan ki rika sha da safe da yamma.

Idan hadin ya kare, za ki iya sake yin wani. Kada ki yi da yawa domin kada ya lalace kafin ki gama shan sa. Ki yi hadin kamar na kwanaki bakwai kawai.

Wannan hadin na masu aurene.

Don maganin tsatsatsagewar gaba:

Ga mace da take fama da matsalar tsatsatsagewar gaba, ga abin da za ta nema:

Abubuwan da ake bukata:

Manyan kabewa, Ganyen zogale, Man kadanya, Magiji, Garin (na magani)

Yadda ake hadawa:

A hada su waje daya, a kwaba da man kadanya, sai a rika shafawa sau biyu ko uku a rana.

Kowane lokaci da aka shafa, a wanke wurin da ruwan dumi. Da iznin Allah, za a ga canji mai kyau.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ado Da Kwalliya Maganin Nankarwa (4) November 8, 2025 Ado Da Kwalliya Yadda Za A Magance Amosanin Baki October 4, 2025 Ado Da Kwalliya Hadin Tsumin Baure September 27, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

“Da zarar wanda ake zargin ya hango jami’an, ya yi amfani da wuka ya yanki daya daga cikin ’yan sa kai a kugu da hannu, wanda hakan ya jikkata shi sosai,” in ji mai magana da yawun ’yansandan.

Ya kara da cewa an garzaya da dan sa kai da ya ji rauni zuwa cibiyar lafiya mafi kusa, inda yake karbar magani a halin yanzu.

Bayan binciken jiki da aka yi wa wanda ake zargi, jami’an sun samu bindiga daya ta gida, bindiga daya, da kuma harsasai guda hudu a hannunsa.

A cikin martaninsa, kwamishinan ’yansandan jihar, CP Bello Sani, ya yaba da kwararrun ayyuka da dabarun binciken bayanan sirri da kuma hadin kai tsakanin DPO na Illo da tawagarsa tare da ’yan sa kai na yankin.

Ya ce, “Ina yabawa da yadda sashen Illo suka yi aiki cikin gaggawa da hadin kai. Wannan aikin ya nuna cewa idan hukumomin tsaro da al’umma suka hada kai, masu aikata laifi ba za su samu damar tserewa ba.”

Haka kuma, kwamishinan ya umurci a mika shari’ar zuwa sashen binciken masu laifi (SCID) na jihar da ke Birnin Kebbi domin ci gaba da bincike mai zurfi, da nufin gano cibiyar hadin gwiwar wanda ake zargi da yadda yake gudanar da ayyukansa, tare da kamo abokan aikinsa.

Ya ce, “’Yan sanda kadai ba za su iya cin nasara a wannan yaki ba. Muna bukatar ci gaba da samun goyon bayan jama’a ta hanyar bayar da bayanai cikin lokaci da kuma sahihai.”

Rundunar ta kuma tabbatar da aniyarta wajen kara kaimi a yaki da ’yan bindiga da sauran nau’o’in laifukan tashin hankali a fadin jihar, tare da tabbatar wa jama’a cewa an dauki matakan rigakafi domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

idan za a tunawa a watan Oktoba, jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da kasancewa ’yan kungiyar ’yan bindiga.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa an kama su ne yayin wata hadin gwiwar sumame da jami’an Anti-Kidnapping Skuad da na Sashen Shanono Dibision suka gudanar da misalin karfe 2 na safe, bayan samun sahihan bayanai daga mazauna kauyen Farin Ruwa a Karamar Hukumar Shanono.

Ya kara da cewa ana zargin wadanda aka kama suna hadin gwiwa da ’yan bindigar da ke kokarin shiga cikin Jihar Kano, inda ya bayyana cewa an fara bincike domin gano tsarin hadin gwiwarsu da kuma kama sauran mambobin kungiyar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Kotu Da Ɗansanda NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano November 14, 2025 Kotu Da Ɗansanda An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa November 8, 2025 Kotu Da Ɗansanda An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi November 8, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje
  • ’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi
  • Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
  • Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne
  • Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci
  • Iran da China na bunkasa alakoki da hadin gwiwa a tsakaninsu
  • Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe
  • An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea