AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro
Published: 15th, November 2025 GMT
Kungiyar tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya sun karfafa kawancensu kan dabarun tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaba don magance kalubalen duniya da na yanki yanki.
“Hadin gwiwa tsakanin kungiyoyinmu bai taba kasancewa mafi karfi da muhimmanci fiye da yadda yake a yau ba,” in ji Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres.
Wannan sanarwar ta zo ne a karshen taron hadin gwiwa na shekara-shekara na 9 na Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka gudanar a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York a ranar Alhamis, wanda Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahamoud Ali Youssouf, da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres suka jagoranta.
Guterres ya jaddada cewa duniya a halin yanzu tana fuskantar “rikici, tashin hankali, karuwar rashin daidaito, wadannan tasirinsu ake ganinshu sosai a nahiyar Afirka.”
Jami’an biyu sun jaddada cewa hadin gwiwa tsakanin AU da Majalisar Dinkin Duniya muhimmin ginshiki ne na kokarin kasa da kasa na inganta zaman lafiya da kare hakkin dan adam.
Sun nuna damuwa game da yaduwar rikice-rikicen jin kai da ke shafar yankuna da dama.
Babban Sakataren ya bayyana “damuwarsa mai zurfi” game da rahotannin baya-bayan nan na “kisan kiyashi da keta hakkokin dan adam” a Al-Fashir da kuma karuwar tashin hankali a yankin Kordofan na Sudan, tare da gargadi game da karuwar rashin tsaro a yankin Sahel ciki har da Mali, Sudan ta Kudu, Somaliya, Libya, da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta bukaci duniya ta gaggauta daukar mataki a Sudan November 15, 2025 EU ta bukaci Isra’ila ta dauki mataki don kawo karshen tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan November 15, 2025 Amurka Ta Sanar Da Fara Kai Farmakin Soja Mai Sunan ” Mashin Kudu” Akan Yankin Latin November 14, 2025 Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire November 14, 2025 Unrwa: Fiye Da Gidaje 282,000 “Isra’ila” Ta Rusa A Gaza November 14, 2025 Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya November 14, 2025 Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya November 14, 2025 Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza November 14, 2025 Kwamitin Tsaro ya tsawaita wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya November 14, 2025 Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin November 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Masu Alaka
Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Fara Karbar Harajin Man Fetur
Hukumar kula da harkokin man fetur a Najeriya ta ce ta dakatar da shirin fara karbar harajin kashi 15 cikin 100 kan albarkatun man fetur ɗin da ake shigowa da su kasar daga ƙasashen waje.
Mai magana da yawun hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), George Ene-Ita, ya faɗa cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa ya kamata ‘yan Najeriya su daina fargaba.
A ranar 29 ga watan Oktoba ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da saka harajin kan man fetur da dizel, wanda zai kara farashin man da ake saukewa a defo-defo, kuma daya daga cikin manufarta shi ne karfafa matatun mai na cikin gida.
Gwamnatin Najeriya ta tsara fara aiki da harajin daga ranar 21 ga watan Nuwamban nan, kafin matakin da NMDPRA ta sanar.
Duk da manufar karfafa matatun mai na cikin gida da harajin zai yi, zai kuma iya jawo hauhawar farashin a gidajen mai kasancewar har yanzu Najeriya na shigo da fetur mai yawa daga kasashen waje.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da china Za su Yi Bikcin Cika Shekaru 55 Da Huldar Diplomasiya Tsakaninsu November 13, 2025 Faransa: An Fara Shari’ar Shugaban ‘Yan Tawayen DRC Bisa Laifuna Akan Bil’adama November 13, 2025 Almayadin Ta Sami Rahoton Hukumar Makamashin Ta Duniya ( IEA) Aka Cewa Iran Tana Aiki Da Dukkanin Ka’idoji November 13, 2025 Janar Ali Fadwi: Muna Aiki Tukuru Domin Sabunta Nisan Makamanmu Masu Linzami November 13, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Iran da Rasha sun Tattauna Gabanin Taron Gwamnonin IAEA November 13, 2025 Iraki: An Fara Sanar Da Sakamakon Farko Na Babban Zaben Da Aka Gudanar November 13, 2025 Kenya: An gano tarin zinari a karkashin kasa da darajarsa ta haura Dala biliyan 5 November 13, 2025 Gaza: Hamas Ta Nemi Kawo Karshen Kisan Kiyashi Da Lamunce Shigar Da Taimako November 13, 2025 MDD ta yi gargadi game da hadarin yunwa a wasu sassa na duniya November 13, 2025 Amurka Na Shirye-Shiryen Aikewa Da Sojoji Guda 1000 A Iyakar Isra’ila Da Yankin Gaza November 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci