Gabon: An Daure Mata Da ‘Dan Tsohon Shugaban Kasa Bongo Shekaru 20 A Gidan Yari
Published: 12th, November 2025 GMT
Matar tsohon shugaban kasar Gaba, Sylvia Bongo da kuma dansa Nuruddin Bongo za su yi zaman kaso na tsawon shekaru 20 saboda samunsu da laifin almubazzaranci da kudin kasa.
Kotun da ta yi shari’ar ta yanke hukunci ne akan iyalan tsohon shugaban kasar Ali Bongo ba tare da suna gabanta ba. Kotun dai an kafa ne domin yin binciken laifuka da suke da alaka da barnata dukiyar kasa.
Kotun ta sami mai dakin tsohon shugaba Bongo, Sylvia Bongo Ondimba da laifin almundahana da dukiyar kasa da kuma yin takardu na jabu.
Shi kuwa Nuruddin Bongo an same shi ne da laifukan da su ka hada da runton bai wa kai mukamai,wanke kudaden haram da mayar da su halaliya, sannan da shirya makarkashiya domin aikata laifuka.
Kowane daya daga cikinsu an kuma ci tararsu da kudin da sun kai saifa miliyan 100.
Dan shugaban kasar ta Gabon Nuruddin Bongo ya kore cewa ya yi almundahanar kudin kasar, kuma ya yi alkawalin ci gaba da kare hakkinsa har bayyanar gaskiya.
Mai shigar da kara na gwamnati ya bukaci ganin kotun ta musamman ta yanke wa Sylvia da Nuruddin hukuncin zaman kurkuku na shekaru 20, saboda daukar duniyar al’umma da mayar da ita ta kashin kai.
A 2023 ne dai aka yi juyin Mulki a kasar ta Gabon wanda ya kawo karshen mulkin iyalan Bongo na tsawon shekaru 55.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tanzania: MDD Ta Yi Kira Da A Yi Bincike Akan Daruruwan Mutanen Da Aka Kashe Sanadiyyar Rikcin Zabe November 12, 2025 Iran Ta Zama Memba A Kungiyar Tattara Bayanai Na Ilimomi Da Kere-kere Ta Duniya ( ISKO) November 12, 2025 Iran: Ta’addanci barazana ce ga dukkan yankin November 12, 2025 Araghchi: Matsalar Yammacin duniya ita ce ci gaban kimiyyar Iran ba makaman nukiliya ba November 12, 2025 Sheikh Qassem: Kawar Da Hizbullah Ne Babban Burin Isra’ila A Lebanon November 12, 2025 Masar Da Sudan Sun Jaddada Wajabcin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin November 12, 2025 Venezuela: Maduro Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tsaron Kasa Mai Cikakkiyar Kariya November 12, 2025 UNICEF: Isra’ila ta hana allurar rigakafin yara masu mahimmanci shiga Gaza November 12, 2025 Ministocin harkokin wajen kasashen yamma sun yi Allah wadai da ta’asar RSF a El Fasher Darfur November 11, 2025 Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya November 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya ce duk da kalubale masu yawa da ake fama dasu a fadin, kasar tana samun “ci gaba, kuma tana kokari,” ta hanyar juriya, da kuma tabbatar da adalci ga mutanenta.
“Mmatsaloli a fadin kasar suna da yawa, amma al’umma, kowace rana, da juriya, kuma bisa yardar Allah kasar tana ci gaba, tana kokari,” in ji shi.
Jagoran ya bayyana hakan ne yau Alhamis yayin da yake jawabi ga dubban jama’a a bikin tunawa da ranar haihuwar Sayyada Fatima Zahra (SA) a Tehran.
Ayatollah Khamenei ya tabo wani bangare game da yakin farfaganda bayan harin watan Yuni da Isra’ila da Amurka suka kai wa Iran, wanda ya tilasta wa makiya su tsagaita wuta.
“A yau, bayan yakin da muka gani, muna tsakiyar yakin farfaganda da kafofin watsa labarai na makiya,” in ji shi.
Ya soki wadanda ke ikirarin sake barkewar yaki, yana mai cewa “Wasu suna ta kara nuna yiwuwar sake gwabza yaki, wasu kuma suna kara ruruta hakan da gangan don sanya mutane cikin rashin tabbas da damuwa, amma da yardar Allah, ba za su yi nasara ba.”
Ayatollah Khamenei ya ce ‘’burin makiyi” shi ne share tasiri, manufofi, da ra’ayoyin juyin juya halin Musulunci.
“Tsawon shekaru, azalumai na duniya sun yi kokarin canza asalin addini, tarihi, da al’adu na kasar Iran, amma juyin juya halin Musulunci ya sa duk wannan kokarin bai yi amfani.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannun kan yarjeniyoyi da dama a tsakaninsu December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Hamas: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza December 11, 2025 Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan December 11, 2025 Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka December 11, 2025 Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan December 11, 2025 ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci