Mazauna Millennium City Sun Zargi Kaduna Electric Da Tilasta Sanya Masu Mita
Published: 10th, November 2025 GMT
Mazauna Millennium City a Jihar Kaduna sun zargi kamfanin wutar lantarki na Kaduna Electric da tilasta musu sanya mita da kuma ƙara farashin wuta ba tare da tuntuba ba.
Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da MPH Estate, TUC Estate, Urban Shelter Estate, Yardan Allah Estate, Highfield Estate, Rahusa Estate, Danbushiya, Sabon Gari, Keke da Doka.
Mazauna sun bayyana cewa an katse musu wuta na makonni saboda ƙin karɓar mitocin da kamfanin ya kawo.
Sun ce matakin Kaduna Electric ya saba da umarnin Hukumar Kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC), wadda ta tanadi cewa dole a tattauna da al’umma kafin a yi canjin mita ko a sauya tsarin biyan kuɗin wuta.
Mazauna sun kuma yi ƙorafi cewa kamfanin ya saka su cikin Band A — wanda aka fi warewa ga masana’antu da wuraren da ake amfani da wuta sosai — duk da cewa unguwanninsu wuraren zama ne na jama’a. Sun kuma bayyana cewa duk da ƙarin farashin, ba sa samun isasshen wuta da ya dace da tsarin Band A.
Wani daga cikin mazauna ya koka da cewa rashin tabbataccen wuta yana janyo musu asara, yana mai cewa: “Kayayyakinmu na lalacewa a cikin firiji, suna cewa muna kan Band A, amma a mafi yawan lokuta ba mu wuce awanni 15 da wuta a rana ba.”
Sai dai kamfanin Kaduna Electric ta bakin Mataimakin Daraktan Kamfanin, Abubakar Sadiq Mohammed, ya kare matakin da suka ɗauka, yana mai cewa ya yi daidai da ƙa’idojin hukumar NERC. Ya ce dokar ta tanadi cewa aƙalla kashi 40 cikin 100 na wutar da ake samu za ta tafi ga Band A, kuma ba abokin ciniki ke zaɓar irin band ɗinsa ba.
Ya ƙara da cewa shirin sanya mitocin kyauta yana cikin wani shiri ne da Bankin Duniya ke tallafawa domin kawar da tsarin ƙiyasta biyan kuɗin wuta da kuma samar da gaskiya a amfani da lantarki.
Lamarin ya ci gaba da jawo martani daga al’ummomin da abin ya shafa, inda ƙungiyoyin mazauna ke kira ga hukumomin da suka dace da su shiga tsakani domin tabbatar da adalci wajen tsarin mita da farashin wuta.
PR: Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Darfur: Babu zaman lafiya da masu yi wa al’ummar Sudan kisan gilla
Gwamnan yankin Darfur na Sudan, Bahreldin Adam Karamah, ya bayyana cewa shugabannin mayakan RSF sun aikata laifuka a El Fasher, yana mai jaddada cewa “ba za su iya ɓoye su ba.”
A cikin wata sanarwa da ya fitar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Sudan (SUNA), Karamah ya fayyace cewa shawarar da Majalisar Tsaro ta Sudan ta yanke, wacce shugabanninta suka goyi bayanta baki daya, ta tabbatar da cewa “babu wani sulhu da masu kisan gillar al’ummar Sudan.” Ya kara da cewa, “Ba za mu yi sulhu a kan wannan kasa ba, kuma ba za mu bari a sauke tutarta ko a lullube ta a cikin laka tare da ta wulakanta ta ba.”
Gwamnan Darfur ya nuna cewa rikicin da ake yi a yanzu “yakin son rai ne da gwagwarmayar domin fayyace makoma” da mutanen da “suka rubuta alkawari na girmamawa da biyayya ga kasa da jininsu.” Ya tabbatar da cewa Sudan “ba za ta ci amanar shahidanta ba kuma za ta mika tutar kasar ga al’ummomi masu zuwa a cikin nasara.”
A wani yanayi makamancin haka, Shugaban Majalisar Mulkin Soja ta Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ziyarci matsugunan mutanen da suka rasa matsuguninsu daga El Fasher a birnin Al-Dabba na Jihar Arewa a ranar Asabar. Ya duba yanayinsu da kuma irin taimakon da suke bukata.
A cewar Kamfanin dillancin labaran SUNA, al-Burhan ya jaddada ruhin hadin kan al’umma, yana mai nuni da “jajircewar kasar wajen magance matsalolin mutanen da suka rasa matsuguninsu da kuma ba su damar rayuwa mai daraja.” Ya umurci dukkan hukumomin gwamnati da abin ya shafa da su samar da muhimman abubuwan bukata ga wadanda suka rasa matsugunin da kuma yin aiki kan kawar da duk wani abin da zai iya kawo cikas ga rayuwarsu ta yau da kullum.
A ranar 26 ga Oktoba, dakarun (RSF) suka sanar da kwace iko da El Fasher bayan fadace-fadace masu tsanani da sojojin Sudan. Duk da haka, al-Burhan ya tabbatar da cewa janyewar sojojin daga birnin don gujewa asarar rayukan fararen hula ne.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araghchi : Iran na yunkurin warware rikicin Pakistan da Afghanistan November 9, 2025 Kasashen (AES) za su hanzarta kafa rundunar hadin gwiwa ta tsaro November 9, 2025 Najeriya: An yi zanga-zangar tir da barazanar Trump November 9, 2025 Sudan : MDD ta yi Allah wadai da ta’addancin El-Fasher November 9, 2025 Lebanon: Akalla mutane uku sun mutu a hare-haren Isra’ila November 9, 2025 An Kafa Mutum-mutumin Tarihi Na Sarkin Daular Roma Da Ya Durkusa A Gaban Sarkin Iran November 9, 2025 Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati November 9, 2025 Wasu Kasashe Takwas Sun Bukaci Ganin An kama Benjamine Netanyahu November 9, 2025 WFP: Ana Fama Da Matsananciyar Yunwa A Gabashin DRC November 9, 2025 Iran da Pakistan sun habaka cinikayyar kan iyaka don karfafa kasuwanci da tsaro November 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci