Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya gargaɗi manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Arewa, da su daina faɗa tare da zama lafiya, ko kuma su fuskanci hukunci a kotu.

Gwamnan, ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya ziyarci mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikici, waɗanda yanzu ke zaune a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Arewa da ke Kangiwa.

Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga

“Na zo ne don jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a dalilin wannan rikici, amma dole ne mutane su daina ɗaukar doka a hannunsu,” in ji shi.

Gwamnan, ya ce gwamnati ta fara bincike don gano musabbabin rikicin, inda ya ƙara da cewa an riga an kama wasu, kuma kotu za ta hukunta masu laifi.

Ya kuma sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 150 ga iyalan waɗanda lamarin abin ya shafa a ƙauyukan Fulani, Zabarmawa da Arewa.

“Babu wani dalili da zai sa rikici ya shiga tsakaninsu, tun da kun shafe sama da shekaru 100 kuna rayuwa tare cikin zaman lafiya,” in ji shi.

Gwamnan, ya kuma yi alƙawarin neman taimakon Gwamnatin Tarayya domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa, tare da yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya a yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamnan Idris Makiyaya Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria

Gidauniyar Tunawa da Marigayi Sir Ahmadu Bello (ABMF) ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa sauƙin kai, tawali’u da jajircewarsa wajen ci gaban Jihar Jigawa.

Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ne ya yi wannan yabon yayin da ya jagoranci tawaga zuwa gaisuwar ban girma a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.

Ya ce salon jagoranci na Gwamna Namadi na ɗauke da ƙima da marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, ya shahara da su, musamman tsari, girmama jama’a da shugabanci na gaskiya da rikon amana.

Dr. Aliyu ya yi kira ga shugabannin Arewa su rungumi jagoranci da ke maida hankali kan al’umma, tare da fifita ilimi a matsayin tubalin cigaba.

Ya kuma sanar da cewa Jihar Jigawa ce za ta karbi bakuncin taron gidauniyar na shekarar 2026, wanda zai ƙunshi laccoci, shirye-shiryen wayar da kan jama’a da bada lambar yabo.

A jawabinsa, Gwamna Namadi ya gode wa Gidauniyar bisa wannan yabo da kuma zaɓar Jigawa don karɓar taron na 2026.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bin sawun Sardauna ta hanyar shugabanci na gaskiya, tsare-tsaren jin daɗin jama’a da kuma zuba jari a fannin ilimi.

Ya tabbatar da cikakken goyon baya wajen shirya taron 2026 cikin nasara.

Tawagar ta haɗa da Madakin Zazzau, Malam Muhammad Munir Ja’afaru, da wasu jami’an Gidauniyar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
  • Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga
  • Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata
  • Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko
  • Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma
  • Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa
  • An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi
  • Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja
  • Sama da gidaje 8,000 za su samu wutar lantarki daga hasken rana a Gombe