MURIC ta buƙaci Tinubu ya sauke Amupitan daga shugabancin INEC
Published: 13th, November 2025 GMT
Kungiyar Kare Muradun Musulmai (MURIC) ta bukaci a gaggauta tsige Farfesa Joash Amupitan daga shugabancin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), saboda matsayinsa kan batun rashin tsaro a Najeriya.
Aminiya ta rawaito cewa, a cikin wani rubutu a baya, Amupitan wanda a lokacin malami ne a Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya ce “abu ne sananne cewa ana aikata laifuka a ƙarƙashin dokokin kasa da kasa a Najeriya, musamman laifukan da suka shafi cin zarafin bil’adama, laifukan yaki da kuma kisan kare dangi.
Ya kara da cewa: “Kalma guda da hukumomin Najeriya da masu bincike na kasa da kasa da masu bayar da rahoto ba su ambata ba (ko kuma suka ki ambata) dangane da dogon rikicin da ake fama da shi a Najeriya ita ce ‘kisan kare dangi.’ Shin wannan mantuwa ce ta gangan ko kuskure ne?
“Zargin shiga tsakanin gwamnati da kungiyoyin da ba na gwamnati ba wajen aikata laifukan kasa da kasa a Najeriya ya kara dagula lamarin da tuni ya yi tsauri.
“Kungiyar Boko Haram tana da burin sauya Najeriya zuwa tsarin Musulunci. ’Yan bindigar kabilar Fulani, a nasu bangaren, sun shiga irin wannan rikicin na adawa da Kiristoci kamar yadda Boko Haram ke yi,” kamar yadda ya rubuta a lokacin.
Haka kuma ya kira Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, hukumomin majalisar da manyan kasashen duniya da su shawarci kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kisan kare dangi su kai Najeriya kotun kasa da kasa (ICJ) saboda gazawar ta wajen hana da hukunta kisan kare dangi kamar yadda aka tanada a cikin saɗarori na 8 da 9 na yarjejeniyar; sannan su yi la’akari da shigar dakarun Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ko na ECOWAS a matsayin mataki na karshe, bisa ga saɗara ta 42 a Kundin Majalisar Dinkin Duniya.
To sai dai a cikin wata sanarwa da shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar, MURIC ta gargadi cewa duk wanda ya shafi irin wannan rubutu mai cike da cece-kuce ba za a iya amincewa da shi wajen jagorantar harkokin zabe ba a Najeriya.
“Mutumin da ya rubuta wasikar kiyayya ga Shugaba Donald Trump kan Musulmai a Arewacin Najeriya ba za a iya tsammanin adalci daga gare shi wajen gudanar da zabe a Najeriya ba,” in ji shi.
MURIC ta ce rawar da ake zargin shugaban INEC ya taka a cikin rahoton ta lalata amincewar da jama’a suka yi masa a baya kuma tana haifar da “barazana ga Musulmai ’yan takara a Arewa ta Tsakiya da sauran sassan kasar.”
“Tun daga lokacin da wannan bayani ya fito, Amupitan ya zama wanda Musulmai ba sa son ganin ya taka rawa a harkokin zabe. Muna bayyana cikakkiyar rashin amincewa da shi a matsayin shugaban INEC,” in ji kungiyar.
Kungiyar ta kuma bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tsige shugaban INEC daga muƙaminsa tare da nada wanda zai samu karɓuwa a fadin kasa.
“Muna ba da shawarar cewa a zabi wani wanda ya cancanta, da zai samu karbuwa a fadin kasa, wanda zai fi dacewa ya kasance mai addini daya da Amupitan amma daga wani yanki daban na siyasa,” in ji Akintola.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zargin kisan Kiristoci kisan kare dangi
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar.
A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko wasu ‘yan kaɗan ke da ɗaruruwan masu tsaro a gefensu.
Ko yaya tasirin tura ‘yan sanda tsaron wasu daidaikun mutane maimakon tsaron alummar kasa gaba daya?
Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan