Aminiya:
2025-11-10@21:58:35 GMT

Matar tsohon Shugaban Ƙasa Shagari ta rasu

Published: 10th, November 2025 GMT

Hajiya Sutura Shehu Shagari, matar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, GCFR, ta rasu tana da shekaru 89 a duniya.

Iyalai sun tabbatar da cewa ta rasu ne da misalin ƙarfe 3:00 na ranar Litinin, bayan fama da doguwar jinya.

Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jallo

Ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa kuma Hakimin Shagari, Kyaftin Bala Shagari (mai ritaya), shi ne ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da aka fitar daga Sakkwato.

Sanarwar ta ce: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Muna baƙin cikin sanar da rasuwar Hajiya Sutura Shehu Shagari, mata ɗaya tilo da da ta rage wa tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, GCFR, Turakin Sakkwato.”

Sanarwar ta ƙara bayyana cewa: “Ta kasance mace mai kamala, tawali’u da nutsuwa, uwa mai kulawa, kakarmu kuma jagorar gida wadda rayuwarta ta cika da mutunci da jinƙai.

“Rasuwarta babban rashi ne ga iyalan Shagari da duk wanda ya san ta. Za a sanar da cikakkun bayanai game da jana’izarta a nan gaba. Allah Ya jiƙanta da rahama.”

Shi ma a shafinsa na Facebook, ɗan marigayi shugaban ƙasa kuma jikan Hajiya Sutura, Bello Bala Shagari, ya tabbatar da rasuwar da bayyana a matsayin babban rashi.

Ya bayyana cewa “Mun yi rashi ba ƙarami ba. Ita ce mata ɗaya tilo da ta rage a cikin matan marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari. Allah Ya haɗa su a Aljannah.”

Rasuwar Hajiya Sutura ta kawo ƙarshen wani babi a tarihin gidan Shagari, gidan tsohon shugaban ƙasa na farko da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya a Jamhuriyar ta Biyu ta Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Shehu Shagari Sutura Shehu Shagari Hajiya Sutura

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Rahotonni Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mahaifiyar Minista Balarabe Lawal Abas ta rasu
  • Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
  • Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
  • Tsohon Shugaban Amurka Biden Ya Yi Dirar Mikiya Kan Trump Kan Matakinsa Na Kawo Barna
  • Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya
  • Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
  • Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta
  • Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja
  • Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC