Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci
Published: 15th, November 2025 GMT
A gobe Lahadi ne za a wallafa makalar babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, game da ingiza gina sabbin ginshikan samar da ci gaban kasa masu inganci, daidai da yanayin da kasar ta Sin ke ciki.
Za a wallafa makalar ta Xi Jinping, wanda shi ne shugaban kasar Sin, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar ne a mujallar Qiushi fitowa ta 22 a bana, muhimmiyar mujallar kwamitin kolin JKS.
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand
Da safiyar yau Juma’a 14 ga watan Nuwamba, a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sarkin Thailand Maha Vajiralongkorn wanda yake ziyarar aiki a nan kasar Sin.
Yayin ganawar tasu shugaba Xi ya ce, sarkin ya sanya kasar Sin a matsayin babbar kasa ta farko da ya kai ziyara. Hakan ya tabbatar da kasancewarsa sarkin Thailand na farko da ya taba ziyartar kasar Sin, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Thailand, wanda hakan ya shaida muhimmancin dangantaka tsakanin kasashen biyu, da kuma dankon zumuncin dake akwai tsakanin Sin da Thailand.
A nasa tsokacin kuwa, sarkin ya ce Thailand na fatan koyon darussa daga kwarewar ci gaban Sin, da fadada hadin gwiwa a fannoni daban-daban da Sin, da kuma habaka huldar al’adu, don kara karfafa abota tsakanin Thailand da Sin. (Amina Xu)
ADVERTISEMENTShareTweetSendShare MASU ALAKA