Wani mutum ya rasu a gidan karuwai bayan ziyartar ’yan mata
Published: 11th, November 2025 GMT
Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a tabbatar da abin da ya jawo mutuwarsa ba.
Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ta ce an miƙa batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.
Wasu majiyoyi daga cikin gidan karuwan sun bayyana cewa wani ma’aikacin otal ɗin da ke kula da wurin ya yi faɗa da mamacin kafin daga bisani ya yanke jiki ya faɗi ya mutu.
Matar tsohon Shugaban Ƙasa Shagari ta rasu EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jalloMajiyar ta ƙara da cewa an garzaya da mutumin asibiti domin ba shi agajin gaggawa, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Rahotanni sun ce an kama wani mutum daga cikin gidan matan da ake zargi da hannu a lamarin, kuma rundunar ’yan sanda ta jihar ta ta fara bincike a kai.
SP Grace Iringe-Koko ta kuma tabbatar da cewa an kama mutum ɗaya da ake zargi, kuma sashen ’yan sanda na Azikiwe ya miƙa shari’ar zuwa SCID domin gudanar da bincike mai zurfi.
Sai dai bayan faruwar lamarin, an lura dukkan ’yan mata masu zaman kansu da ke yawo a cikin da wajen gidan karuwan sun yi layar zana.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fatakwal jarirai ya mutu a tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: A bayyane yake cewa Amurka tana da hannu dumu-dumu wajen wuce gona da iri kan kasar Iran
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya mayar da martani ga amincewar da shugaban Amurka ya yi na daukar alhakin harin da sojojin Sahayoniyya suka kai wa Iran, yana mai cewa: “Tun daga farko a bayyane yake cewa Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran.”
Baqa’i ya rubuta a shafinsa na X-Platform: “Shin kuna tuna cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya sanar a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025 cewa: Amurka ba ta da hannu a harin da ‘yan Sahayoniyya suka kai wa Iran, kuma ya jaddada cewa wannan ‘aikin hadin gwiwa ne’ da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi kuma ‘ba su da hannu a hare-haren da aka kai wa Iran’?”
Ya ci gaba da cewa: “Wannan ikirarin karya ce karara, domin tun daga farko ya bayyana cewa: Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran. Yanzu shugaban Amurka ya yarda cewa shi ne ke da alhakin hakan, yana fallasa karyar sakataren harkokin wajensa kuma a zahiri ya yarda cewa Amurka ce ke da alhakin gudanar da wannan aikin tun daga farko.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Mexico Sun Karyata Zarge-Zargen Da Aka Yi Kan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran November 8, 2025 Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila November 8, 2025 Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta November 8, 2025 Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe November 7, 2025 Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma November 7, 2025 Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan November 7, 2025 Tarayyar Turai: Ana Fuskantar Matsananciyar Wahalar Isar Da Kayan Agaji Zuwa Al-Fashar Na Sudan November 7, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon November 7, 2025 Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza November 7, 2025 Falasdinawa Miliyan 1.5 Ne Ke Cikin Mawuyacin Hali November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci