Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro
Published: 12th, November 2025 GMT
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tare da shugabannin Rundunonin Sojin Najeriya, za su ci gaba da kare duk wani jami’i da ke gudanar da aikinsa bisa doka.
Badaru, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a taron da aka shirya domin bikin tunawa da Sojojin Najeriya na shekarar 2026 a Abuja.
Wannan na zuwa ne bayan ce-ce-ku-cen da ya faru ranar Talata tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wani jami’in rundunar sojan ruwa, Laftanar A. M. Yerima.
An yi taƙaddama ne kan wani fili da ke Abuja da ake zargin mallakar wani tsohon Shugaban Rundunar Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo (mai ritaya) ne.
“A Ma’aikatar Tsaro, da kuma rundunonin sojoji, za mu ci gaba da kare jami’anmu masu aiki bisa doka,” in ji Badaru.
“Muna binciken al’amarin da ya faru, kuma muna tabbatar da cewa duk wani jami’i da yake aikinsa yadda doka ta tanada za a kare shi. Ba za mu bari wani abu ya same shi ba matuƙar yana yin aikinsa da kyau.”
Ministan, ya kuma sanar da sabon shirin gwamnati na haɗa tsofaffin sojoji cikin aikin tsaron al’umma da ci gaban yankuna ta hanyar shirin “Reclaiming the Ungoverned Space for Economic Benefits Programme (RUSEB-P)”.
Ya ce manufar shirin ita ce amfani da ƙwarewar tsofaffin jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankunan da ake samun rikice-rikice.
Badaru, ya bayyana cewa shirin RUSEB-P zai taimaka wajen rage aukuwar ta’addanci da kuma bunƙasa harkokin noma, hakar ma’adinai, da sauran ayyukan tattalin arziƙi.
Ya ƙara da cewa an kafa kwamiti da ke aiki kan yadda za a aiwatar da shirin.
Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnati na shirin sake duba ‘Nigerian Legion Act’ domin kafa Ƙungiyar Tsofaffin Sojojin Najeriya (Veterans Federation of Nigeria – VFN), wacce za ta ƙarfafa tsarin kariya da tallafa wa walwalar tsofaffin jami’an tsaro.
Ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da za su inganta tsaron ƙasa, inganta walwalar sojoji, da kuma girmama sadaukarwar tsofaffin jami’an tsaro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Badaru Ministan tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Jakadun Kasashen Waje: Shirin Raya Kasa Na 15 Na Sin Na Dauke Da Kyakkyawan Sako
Manyan jami’an diplomasiyya daga kasashe sama da 160, ciki har da jakadu 90 dake kasar Sin da manyan jami’an ofisoshin jakadancin kasashen ne suka halarci taron, wanda sashen kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS ya shirya. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA