Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe
Published: 14th, November 2025 GMT
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta gwabza da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a wasan ƙarshe na tantance wakilin Afrika a share fagen Gasar Cin Kofin Duniya na 2026. Wasan zai ɗauki hankali zai gudana ne a ranar Lahadi a sabon filin Prince Moulay Abdellah da ke Rabat, Morocco, inda za a tantance ƙasa ta ƙarshe daga Afrika da za ta shiga matakin share fagen gasar Kofin Duniya.
Nijeriya ta samu gurbin wasan ƙarshe bayan da ta lallasa Gabon da ci 4-1 a ranar Alhamis, sakamakon da ya ƙarfafa matsayin tawagar wajen sake samun martabarta a nahiyar. A ɗaya ɓangaren, DR Congo ta samu nasarar da ta ba ta gurbin wasan ƙarshe ne bayan da ta doke Kamaru da ci 1-0, inda kyaftin Chancel Mbemba ya zura ƙwallo a mintoci na ƙarshe.
Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4A yanzu za a fafata ne tsakanin ƙasashen biyu waɗanda ke neman damar ƙarshe ta wakiltar Afrika a gasar share fagen shiga Kofin Duniya da za a yi a Mexico, Amurka da Kanada. Duk wata gazawa zata ƙare burin kowace tawaga, yayin da nasara za ta buɗe musu ƙofar shiga manyan gasannin duniya.
ADVERTISEMENTWasan na Lahadi zai kasance mai cike da zafi da taka tsantsan, domin dukkan ƙungiyoyin sun shiga Morocco da burin tabbatar da cewa su ne za su samu tagomashi a wasan share fagen, wanda zai zama matakin farko na zuwa babban gasar ta 2026.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: Kofin Duniya share fagen
এছাড়াও পড়ুন:
Nijeriya Za Ta Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Gusau
“Mun yi imani cewa ‘yan wasanmu tare da kwarewar da suke da ita, zai janyo wa Nijeriya abin alfahari, ba kawai a ranar Alhamis ba, har ma a duk tsawon wasannin share fagen da zamu buga”, hakan yasa muke da kwarin gwuiwar cewar kasarmu za ta iya samun tikitin shiga gasar cin kofin Duniya,” in ji Gusau.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA