Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci
Published: 14th, November 2025 GMT
Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici.
Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta bari wasu kasashe su raba kawunansu, ya kuma bayar da tabbacin cewa; duk da kalubalen da ake fuskanta, Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa mai girma da kuma ci gaba da samun hadin kai.
Har ila yau, Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Abubakar Danbazau, a jawabinsa ya bayar da shawarar cewa; dole ne a magance matsalar rashin tsaro, matsalolin fatara, sauyin yanayi, rashin aikin yi da kuma amfani da kudaden tarayya da aka kayyade.
A cewarsa, kwararar masu tsattsauran ra’ayin addini cikin kasar, ya taimaka wajen tabarbarewar tsaro da ke bukatar daukar matakin yaki da su ko kuma korar su daga kasar baki-daya.
Kazalika, ya kuma bukaci Gwamnonin Arewa da su yi amfani da kudaden asusun tarayya, ta hanyar samar da guraben ayyukan yi da samar da karin masana’antu, domin samun ci gaban tattalin arziki.
A cewar tasa, alkaluma sun nuna cewa; sakamakon ayyukan ‘yan fashi da makami, ya hana kimanin yara miliyan 10 shiga makarantun firamare da sakandare a Arewacin Najeriya.
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, a wani faifan bidiyo da ya gabatar a wurin taron, ya yaba wa wadanda suka shirya taron, musamman ganin cewa; an riga an tattauna batun rashin tsaro a taron Kungiyar Gwamnonin Arewa.
“An yi matukar samun nasarori a wannan taro, kana kuma an tura jami’an tsaro ko’ina a Arewacin kasar nan,” in ji shi.
Gwamna Uzodimma Ya Bukaci Sarakunan Gargajiya Su Jagoranci Yi Wa Kasa Adduo’I’n Zaman Lafiya
Biyo bayan matsin lamba da ake yi wa Nijeriya, kan kashe-kashen da rashin tsaro ke haifarwa, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Cif Hope Uzodimma, ya yi kira ga Sarakunan gargajiya da su rika yin addu’o’i, domin samun saukin matsalar tsaro.
Uzodimma, wanda shi ne Gwamnan Jihar Imo, ya jagoranci sauran gwamnonin wajen kai wa Gwamna Mohammed Umar Bago na Jihar Neja ziyara, domin jajanta masa kan asarar rayuka da dama da aka yi a Jihar, a kwanakin baya.
Gwamnan ya kara da cewa, duk da kokarin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, na karfafa tsarin tsaron kasar, ya kamata Sarakunan Gargajiya su yi amfani da nasu hanyoyin da za su kawo karshen rashin tsaro.
“Ina kira ga Sarakunan Gargajiya, da su hada kan al’ummar kasar nan, domin kare al’umma, shugaban kasa, ya himmatu wajen samar da ayyuka, kuma mu a kananan hukumomi; mun dukufa wajen aiwatar da dukkanin manufofinsa, kana kuma; nuna shugabanci na gari shi ne abin da muka sanya gaba,” in ji shi.
Dangane da dalilin ziyarar Gwamna Bago, ya ce; sun je jihar ne, domin jajanta wa gwamnati da jama’a, dangane da haduran jiragen ruwa da na tankar mai da rashin tsaro da suka yi sanadiyyar salwantar rayuka da dama tare da raba mutane da dama da gidajensu.
Ya ce, “Mun zo ne, domin mu yi wa dan’uwanmu ta’aziyya tare da karfafa masa gwiwa, mu kuma bayar da gudunmawar kudi da addu’o’i, da kuma bai wa iyalan wadanda iftila’in ya afka hakuri tare yi musu ta’aziyyar rashin da suka yi”.
“Gwamna Bago, na daya daga cikin mafi kyawun cikinmu, mafi haske, mai kuzari kuma wanda ya san makamar aiki” in ji shi.
Gwamnan Jihar Neja, Bago da Etsu Nupe da Shugaban Masu Rike da Sarautun Gargajiya na Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, duk sun yaba da ziyarar da gwamnonin masu ci suka kawo musu jihar.
Bago ya yi tir da kalubalen tsaro da dimbin bala’o’i da suka addabi jihar, ya kuma ce; gwamnati ta dukufa wajen ganin an samu zaman lafiya.
Gwamnonin da suka ziyarci Minna, sun hada da na Jihohin Delta, Kogi, Ebonyi, Imo da kuma Legas, yayin da Mataimakan Gwamnonin Jihohin Jigawa, Kebbi da Sokoto, suka wakilci nasu gwamnonin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: Sarakunan Gargajiya rashin tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe
Gwamnatin Jihar Gombe ta dakatar da wani Hakimi da Dagaci a ƙaramar hukumar Funakaye bayan barkewar rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin.
Rahotanni sun ce rikicin dai ya yi sanadin mutuwar ɗan sanda ɗaya tare da jikkatar wasu jami’an tsaro da dama.
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal Yadda na yi asarar N120m a gobarar Singa — Ɗan Kasuwar KanoKwamishinan Shari’a na jihar, Barista Zubairu Muhammad, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai bayan zaman kwamitin tsaro da aka gudanar ranar Laraba.
Ya ce an dauki matakin dakatarwar ne domin tabbatar da doka da oda, tare da aika sakon gargaɗi ga sauran masu rike da sarautun gargajiya cewa ba za a lamunci sakaci wajen dakile rikice-rikice ba.
“Majalisar ta yi nazari mai zurfi kan lamarin kuma ta nuna damuwa. Gwamnati ba za ta lamunci kai hari ga jami’an tsaro ko hana su gudanar da ayyukansu bisa doka ba. Duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani,” in ji shi.
Barista Muhammad ya tabbatar da cewa an kama wasu da ake zargi da hannu a harin da aka kai wa jami’an tsaron, kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.
Kwamishinan ya ce kodayake ɗaya daga cikin shugabannin da aka dakatar ya rasa ɗansa a cikin lamarin, hakan bai hana gwamnati ɗaukar mataki ba saboda gazawarsa wajen hana rikicin ya ƙara kamari.
“Rahotanni game da halayen mamacin sun tayar da hankali. Da mahaifinsa, wanda shi ne shugaba a yankin, da ya ɗauki mataki tun da wuri, da ba a kai ga tashin hankali ba. Jagoranci na nufin jarumta da adalci,” in ji shi.
Kwamishinan ya sake jaddada goyon bayan gwamnati ga jami’an tsaro, inda ya yaba da jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya wanda ya sa jihar ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da suka fi kwanciyar hankali a ƙasar.
“Gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro don su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa. Duk wani yunƙurin tsoratar da su ko hana su aiki ba za a lamunce shi ba,” in ji shi.
Barista Muhammad ya kuma ambaci rahoton kwamiti ƙarƙashin tsohon Mataimakin Sufeton ’yan sanda na kasa, AIG Zubairu Muazu (mai ritaya), wanda ya binciki tushen rikicin na manoma da makiyaya a jihar.
Kwamishinan ya ce kwamitin ya gano toshe burtalolin kiwo na asali ta hanyar gonaki da gine-gine a matsayin babban abin da ke haddasa rikice-rikicen da ake ta fama da su.
Gwamnatin jihar ta kuma jaddada aniyarta ta kare zaman lafiya tare da yin gargaɗin cewa babu wanda za a rufa wa asiri idan aka same shi da laifin kawo barazana ga tsaro ko hana shari’a gudanar da aikinta yadda ya kamata.