Nijeriya ta doke Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya
Published: 13th, November 2025 GMT
Tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles ta doke tawagar ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026 da suka fafata a yammacin wannan Alhamis.
Wasan wanda aka soma da ƙarfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat a Morocco, ya bai wa Super Eagles damar lallasa The Panthers har ci 4-1.
Wannan sakamakon ya bai wa Nijeriya nasarar kaiwa zagayen ƙarshe a wasan cike gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026.
Akor Adams ne ya fara ci wa Super Eagles ƙwallo a minti na 78, amma daga baya Gabon ta farke ta hannun Mario Lemina daf a tashi daga fafatawar.
A haka dai aka tashi 1-1 bayan minti 90 da suka buga, lamarin da ya sa aka yi ƙarin minti 30 saboda dole sai an samu wanda zai yi nasara.
Bayan an dawo daga hutun ƙarin lokacin ne aka ci gaba da fafatawar har ta kai ga Super Eagles ta ƙara na biyu ta hannun Chidera Ejuke, sannan Victor Osimhen ya ƙara na uku na hudu.
A ɗaya wasan daf da ƙarshen kuma, Kamaru ce za ta fafata da Jamhuriyar Congo a ranar Alhamis, inda duk wanda ya yi nasara a ciki, zai fuskanci tawagar ta Nijeriya a ranar Lahadi mai zuwa.
Wasan na yau dai shi ne na farko tsakanin ƙasashen tun bayan shekarar 2005, lokacin da Nijeriya ta doke Gabon da ci 2-0.
An barje gumin ne ƙasa da awanni 24 bayan tawagar Super Eagles da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) sun warware matsalolin da suka shafi kuɗaɗe tsakanin ‘yan wasa da hukumomin ƙwallon ƙafa.
Kyaftin William Troost-Ekong ya tabbatar da cewa an biya dukkan haƙƙoƙin da suke bi, inda ya ce tawagar ta koma fili cikin karsashi da ƙwarin gwiwar neman nasara a wasan yau.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
BUA ya tallafa wa ɗaliban Sakkwato 200 da miliyan 40
Kamfanin samar da siminti na BUA ya bayar da tallafin karatu Naira miliyan 40 ga ɗalibai 200 da ke manyan makarantu a jihohin tsohuwar Jihar Sakkwato.
An bayar da tallafin domin ganin sun cimma burinsu a fannin ilmi.
An kai hari gidan jami’in ɗan sanda a Yobe Ɗaliban Jami’ar Unijos 8 sun mutu a hatsarin motaƊaliban da suka ci gajiyar sun haɗa da matasa 50 daga Sakkwato, 50 daga Kebbi da 50 daga Zamfara, sai 50 a Wamakko inda cibiyar kamfanin simintin yake.
Kowane ɗalibi zai karɓi Naira dubu 200, an samu ninkin ɗaliban kuɗin ma an samu ƙari da kashi 100 bisa ga shekarun baya.
Shugaba kuma Daraktan kamfanin, Injiniya Yusuf Binji ya ce sun ninka yawan ɗalibai daga 100 zuwa 200 haka kuɗin daga dubu 100 zuwa 200.
Injiniya Binji ya bayyana tallafin karatun matsayin saka jari ne da zai samar da al’ummar mai ɗorawa a gaba.
Ya yi kira ga waɗanda suka ci gajiyar su yi abin da ya dace kuma kamfani zai bibiyi karatunsu.
Shugaban Kamfanin na BUA ya gode wa gwamnatin jiha kan samar musu filin kasuwanci ba tsangwama.
Mai baiwa Gwamanan Sakkwato shawara, Honarabul Usman Arzika Fako ya ce tallafin zai bunƙasa ilmi da samar da aikin yi ga matasa.
Ya yaba wa kamfanin ga wannan hoɓɓasar, akwai buƙatar a duba wasu ɓangarori suma a yi abin da ya kamata.
Balkisu Bello Muhammad, ɗaliba daga Kebbi ta bayyana BUA ginshiƙi ne na samar da cigaba ta gode wa kamfanin kan wannan saka jarin da suka yi da za su ci gajiyarsa a gaba.
Umar Bello ɗalibi daga Zamfara ya nuna farin cikinsa ga kamfanin yadda ya ɗaga karatunsa zai samu nasara a gaba.