Jihar Jigawa Za ta Kashe Sama da Naira Biliyan Daya Domin Inganta Ayyukan Wutar Lantarki
Published: 12th, November 2025 GMT
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse.
A cewarsa, wannan mataki na daga cikin jajircewar gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma bunkasa ci gaban al’umma musamman a yankunan karkara.
A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, aikin na nuna kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da karin samun wutar lantarki, kara habakar tattalin arziki, da inganta rayuwar jama’a a birane da karkara.
Ya bayyana cewa, aikin zai kunshi samarwa da girka sabbin na’urorin bada wuta (transformers), hada garuruwa ta hanyar layin wuta na 33KV, da kuma maye gurbin turakun wuta da suka lalace a sassa daban-daban na jihar.
Sanarwar ta kara da cewa, garuruwan da za su amfana sun hada da Madaka a Gagarawa, Bosuwa a Maigatari, Mai Tsamiya da Unguwar Gawo a Sule-Tankarkar, Yandamo a Gumel, Farin a Dutse, Giginya a Gwaram, Kwanar Dindu zuwa Bulangu a Kafin Hausa, Kanya Babba a Babura da kuma Garki a Karamar Hukumar Garki.
Ya ce wannan aikin da aka yi na nuna jajircewar gwamnatin Namadi wajen samar da ci gaba mai dorewa da tabbatar da cewa kowace al’umma ta amfana da romon dimokuradiyya.
Alhaji Sagir ya kara da cewa, gwamnatin Namadi ta kuma amince da bayar da kwangilar gina rijiyoyin samar da ruwa da ke aiki da hasken rana domin sabbin gidaje na Danmodi Housing Estates.
Wadannan gidaje sun hada da na Birnin Kudu, Kafin Hausa, Kazaure, Ringim da kuma hanyar Nguru–Hadejia.
Kwamishinan ya bayyana cewa, kwangilar da ta kai fiye da Naira miliyan 378 tana nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen samar da muhimman abubuwan more rayuwa da ke kara ingancin zama da dorewar sabbin gidaje a fadin jihar.
Ya ce amincewar wannan aiki na nuna yadda gwamnatin Namadi ke aiwatar da tsare-tsaren ci gaba cikin tsari guda, wanda ya hada da gidaje, ruwa, da makamashi mai sabuntawa domin inganta rayuwar al’umma baki daya.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Wutar Lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ba da tabbacin isasshen tsaro a zaɓen ƙananan hukumomin Borno
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Borno ta yi kira ga mazauna da su fito cikin kwanciyar hankali domin kada kuri’arsu a zaɓen ƙananan hukumomin da ake gudanarwa a yau Asabar.
Tundunar ta tabbatar da cewa za a samar da isasshen tsaro a lokacin zaɓen da kuma bayan kammalawarsa.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya yi wannan kira ne a yayin wani taron tsaro mai muhimmanci da aka gudanar tare da ƙungiyoyi, kwamandojin tsaro, shugabannin sassa, da dukkan DPOs a faɗin jihar, kafin zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a yau Asabar, 13 ga Disamba, 2025.
“Rundunar tana kira ga jama’a da su fito ba tare da wani shakka ba domin aiwatar da nauyin da ke kansu cikin lumana,” in ji sanarwar, wadda kakakin Rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a Maiduguri
Ya kuma gargadi mazauna jihar da su kasance cikin taka tsantsan, tare da kauce wa labaran ƙarya da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a.
Rundunar ta bayyana cewa an riga an fara amfani da dabarun tura jami’an tsaro da sanya idanu a fadin jihar domin tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.