Aminiya:
2025-11-09@11:26:07 GMT

Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga

Published: 9th, November 2025 GMT

Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Sama’ila Bagudo, ya kuɓuta bayan shafe fiye da mako guda a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi.

Aminiya ta ruwaito cewa an sace mataimakin shugaban majalisar ne a ranar Juma’a 31 ga Oktoba, 2025, jim kaɗan bayan ya kammala sallar la’asar a masallacin garinsu na Bagudo.

’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu

Sakataren gwamnatin jihar, Yakubu Tafida, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Asabar.

Bayanai sun tabbatar da cewa lamarin na zuwa ne daidai da lokacin da aka gudanar da addu’o’in haɗin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci domin neman zaman lafiya a jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da cewa an saki mataimakin shugaban majalisar.

CSP Abubakar ya bayyana cewa yanzu haka yana tare da iyalansa bayan mahukunta sun tabbatar da ƙoshin lafiyarsa a wani asibiti.

“An sace shi a ranar 31 ga Oktoba, amma an sako shi jiya [Asabar] kuma yanzu yana cikin ƙoshin lafiya kamar yadda mahukunta suka tabbatar,” in ji kakakin rundunar.

Ya ƙara da cewa rundunar ta yaba da jajircewar jami’an tsaro da suka shiga aikin ceto tare da goyon bayan al’umma, inda ya ce bayanan da jama’a suka bayar sun taka muhimmiyar rawa wajen ceto wanda aka sace lafiya.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da kai hare-hare kan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a faɗin jihar, tare da kira ga jama’a su kasance masu lura da duk wani motsi da ake zargi su kuma rika sanar da hukumomin tsaro cikin gaggawa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Kebbi tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.

Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya saboda zargin ana zaluntar Kiristoci.

Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock

Barau ya ce maganar da Trump ya yi ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba za ta yadda a ci zarafinta ko a tsangwame ta ba.

“Shugaban Amurka ya fito ya ce, ‘Najeriya wulaƙantaciyyar ƙasa ce, za mu kai muku hari,’ wannan bai dace ba.

“Ya kamata ya janye wannan maganar ya kuma nemi afuwar Najeriya,” in ji Barau.

Ya ƙara da cewa maganganun Trump sun karya dokokin diflomasiyya da na ƙasa da ƙasa.

“Idan kuna da ƙorafi a kan ƙasarmu, ku bi hanyoyin shari’a. Ku je Majalisar Ɗinkin Duniya, ku nemi izini, sannan ku aiwatar da shi yadda ya dace. Tsallake wannan hanya ba abin da ya dace ba ne,” in ji shi.

Barau, ya jaddada cewa kalaman Trump ba za su firgita Najeriya ba, kuma ya kamata shugaban Amurka ya girmama ƙasa mai cin gashin kanta.

“Ba za mu ji tsoron faɗin gaskiya ba. Da Trump yana nan, da na faɗa masa kai-tsaye cewa abin da yake yi ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa kuma ba daidai ba ne,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra
  • Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
  • Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura
  • Minista Goronyo ya Duba Ci Gaban Aikin Titin Abuja Zuwa Kano
  • Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata
  • Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya
  • Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta