Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta
Published: 16th, November 2025 GMT
Gwamnatin Beirut ta ce za ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban Majalisar Dinikin Duniya game da gida katangar siminti a kan iyakar Kudancin Lebanon.
A cikin wata sanarwa data fitar fadar shugaban Lebanon ta sanar da cewa Beirut za ta shigar da kara a Majalisar Dinkin Duniya game da gina katangar.
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya umarci Ministan Harkokin Wajen kasar Youssef Radji da ya umurci tawagar Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ta shigar da karar gaggawa a kwamitin Tsaro kan gwamnatin Isra’ila saboda gina katangar siminti a kan iyakar kudancin Lebanon, wadda ta wuce ‘’Layi Shuɗi’’ da aka zana bayan janyewar Isra’ila a shekarar 2000.
Hukumomin Lebanon sun ce katangar simintin da sojojin Isra’ila suka gina ta hana mazauna kudancin Lebanon shiga wani yanki mai fadin murabba’in mita 4,000 na yankin Lebanon.
Wani bincike da Rundunar Wucin Gadi ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ta gudanar a watan Oktoba ya nuna cewa katangar da sojojin Isra’ila suka gina ta ratsa Layin Shuɗi, kamar yadda Stéphane Dujarric, kakakin Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ya sanar a ranar Juma’a.
An kuma gina wani sashe na biyu na wata katangar a kudu maso gabashin kauyen Yaroun na Lebanon, kuma ita ma ta ratsa Layin Shuɗi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran : kasantuwar sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ce ga zaman lafiyar duniya November 16, 2025 AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025 An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba November 15, 2025 Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a Majalisar Dinkin Duniya ta shigar da
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa: An Fara Shari’ar Shugaban ‘Yan Tawayen DRC Bisa Laifuna Akan Bil’adama
A jiya Laraba ne aka bude shari’ar tsohon madugun ‘yan tawayen kasar DRC Roger Lombala a kasar Faransa bisa tuhumar da ake yi masa da aikata laifuka akan bil’adama a yayin yakin DRC na biyu. Ana kuma tsammanin cewa wannan shari’ar za ta dauki wata daya ana yinta.
A yayin zaman shari’ar za a gabatar da shaidu daga wadanda su ka cutu sanadiyyar ayyukan kungiyar ‘yan tawayen wacce Lombala ya jagoranta.
Wannan shi ne karon farko da za a yi wa dan kasar DRC shari’a a kasar Faransa bisa ka’idar hurumin shari’a na duniya.
Ofishin Fada Da Laifuka Aka Bil’adama ( OCLCH) ya kama Lombala ne a ranar 29 ga watan Disamba 2020 a birnin Paris. An kuma gabatar da shi a gaban kotu a ranar 2 ga watan Janairu 2021 inda aka tuhume shi da; “Kitsa makirci da zummar aikata manyan laifuka akan bil’adama” da kuma ” Makarkashiyar aikata laifuka akan bil’adama.”
A cikin watan Nuwamba na 2023 aka tuhumi madugun ‘yan tawayen a karkashin wani tsari da doka da yake bai wa wata kasa yin shari’a akan laifuka masu hatsari da aka tafka, ba tare da la’akari da inda inda aka yi laifukan ba.
Ana zargin Lombala da kungiyarsa da cewa ya aikata laufukan a tsakanin watan Oktoba na 2002 zuwa watan janairu na 2003 a karkashin kungiyarsa ta “Gamayyar ‘yan Demokradiyya da Masu Kishin Congo” wacce kasar Uganda take taimakawa. A wancan tsakanin kungiyar ta yi kokarin shimfida ikonta a yankin Bini wanda yake cike da ma’adanai a gundumar Itori ta gabas. Daga cikin laifukan nasu da akwai kisa da kuma fyade da wawason dukiyar al’umma.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Almayadin Ta Sami Rahoton Hukumar Makamashin Ta Duniya ( IEA) Aka Cewa Iran Tana Aiki Da Dukkanin Ka’idoji November 13, 2025 Janar Ali Fadwi: Muna Aiki Tukuru Domin Sabunta Nisan Makamanmu Masu Linzami November 13, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Iran da Rasha sun Tattauna Gabanin Taron Gwamnonin IAEA November 13, 2025 Iraki: An Fara Sanar Da Sakamakon Farko Na Babban Zaben Da Aka Gudanar November 13, 2025 Kenya: An gano tarin zinari a karkashin kasa da darajarsa ta haura Dala biliyan 5 November 13, 2025 Gaza: Hamas Ta Nemi Kawo Karshen Kisan Kiyashi Da Lamunce Shigar Da Taimako November 13, 2025 MDD ta yi gargadi game da hadarin yunwa a wasu sassa na duniya November 13, 2025 Amurka Na Shirye-Shiryen Aikewa Da Sojoji Guda 1000 A Iyakar Isra’ila Da Yankin Gaza November 12, 2025 Shugaban Iran Ya Aike Da Wasika Ta Musamman Zuwa Ga Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya November 12, 2025 Gwamntin Nijeriya tace Za ta Kare Sojojinta Da Ke Bakin Aiki November 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci