’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato
Published: 11th, November 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin.
“Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su yi garkuwa da su. A wasu lokuta ma suna ɗora wa al’umma haraji, idan ba a biya cikin wa’adin da suka bayar ba, sai su kawo hari,” in ji shi.
Wata majiya ta bayyana cewa akwai wasu mutum biyu da suka jikkata sakamakon harbin bindiga da ke karɓar magani a wani asibiti da ke kusa da yankin.
Shugaban al’umma a yankin ya roƙi gwamnati ta kafa ofishin jami’an tsaro a yankin domin daƙile barazanar maharan, yana mai cewa yanzu babu ko ɗaya a yankin.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce bai samu rahoton lamarin ba tukuna, amma zai bincika.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, bai waiwayi Aminiya da wani ƙarin bayani ba.
Ƙauyen Alkalije na cikin gundumar Kilgori da ke iyaka da Ƙaramar Hukumar Silame da wasu ƙauyuka na Jihar Kebbi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jihar Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Isra’ila” A Yankin Saida
Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon ya ambaci cewa, Mutum daya ya kwanta dama, sadaniyyar harin wani jirgin sama maras matuki na HKI akan wata mota a garin al-yasariyyah,dake gundunar Saida, a kudancin kasar.
Majiyar tsaro ta fada wa kafafen watsa labaru cewa, jirgin saman maras matuki ya harba makamai masu linzami guda 3 ne akan motar da hakan ya yi sanadiyyar konewarta baki daya.
Dama dai ma’aikatar lafiya ta Lebanon din ta sanar da shahadar wasu mutane biyu sanadiyyar hare-hare biyu da Isra’ilan ta kai a kudancin kasar, a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata.
Tun da aka tsagaita wutar yaki a watan Nuwamba 2024, HKI take ci gaba da keta ta, ya kai dubbai.
A wani labarin daga Lebanon an bayyana cewa mutane 28 ne su ka yi shahada daga watan da ya gabata.
Ministan Lafiya na Lebanon Rakan Nasser Eddine ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon, musamman a kudancin kasar, sunakara tsananta, yana mai jaddada cewa rikicin ba wai kawai ya takaita ga wani yanki ɗaya ba ne, lamari ne da ya shafi kowace gida a Lebanon.”
A lokacin ziyararsa a birnin Hermel da ke arewa maso gabashin Lebanon, Nasser Eddine ya bayyana cewa adadin waɗanda suka yi shahada ya karu daga 23 zuwa 28 a cikin watan da ya gabata, yana mai jaddada cewa waɗannan shahidai suna da iyalai da dangi da ‘yan uwa, kuma dole ne ƙasa ta tsaya musu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tarayyar Afirka (AU) Ta Yi Gargadi Akan Tabarbarewar Harkokin Rayuwa A Kasar Mali November 10, 2025 An Fara Gasar Karatun Alqur’ani Mai Tsarki ta Sheikha Hind Bint Maktoum November 10, 2025 Zaben Iraki: Gwaji don ‘yancin siyasa da kawo karshen tsoma bakin Amurka November 10, 2025 Iran da Rasha sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa November 10, 2025 Iran ta nuna damuwa kan zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan November 10, 2025 Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa November 10, 2025 Maduro ya kirayi taron CELAC da ya yi tir da ayyukan tsokana na Amurka a yankin Caribbean November 10, 2025 Lebanon: Mutane 28 ne suka yi shahada a hare-haren Isra’ila tun daga watan da ya gabata November 10, 2025 Gwamnan Darfur: Babu zaman lafiya da masu yi wa al’ummar Sudan kisan gilla November 10, 2025 Araghchi : Iran na yunkurin warware rikicin Pakistan da Afghanistan November 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci