An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano
Published: 12th, November 2025 GMT
’Yan sanda a Jihar Kano sun gano wata mota ƙirar Toyota Hilux mallakar ofishin mataimakin gwamnan jihar, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, wadda aka sace kwanan nan a harabar gidan gwamnati.
Majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano sun ce an sace motar ce cikin dare, lamarin da ya kai ga tsare direban da motar ke hannunsa, Shafiu Sharp-Sharp a matsayin ɗaya daga cikin ababen zargi.
Sai dai wata sanarwa da ofishin mataimakin gwamnan ya fitar, ta ce jami’an tsaro sun gano motar da safiyar wannan Larabar bayan wani aikin haɗin gwiwa na gaggawa da aka gudanar.
Sanarwar ta ce an kama wanda ake zargi da satar motar, Ya’u Gezawa, wanda yanzu haka yana taimaka wa jami’an tsaro wajen bincike.
Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya bayyana lamarin a matsayin cin amanar aiki, tare da jinjinawa ’yan sanda bisa gaggawar da suka yi wajen gano motar da kama wanda ake zargi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aminu Abdussalam Gwarzo Fadar Gwamnatin Kano
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa
Ya bayyana cewa mutanen sun fita da sassafe don wani aiki, amma ‘yan bindigar suka tare su suka kashe su tare da tserews da babur ɗinsu .
Mista Ajeh, ya roƙi hukumomin tsaro da su gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Haka kuma, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta jiha da su ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a Jihar Nasarawa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA