Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Comoros Azali Assoumani, sun aika wa juna sakon taya murnar cika shekaru 50 da kulla alakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

A cikin sakonsa, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, yana mayar da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Comoros, kuma yana son hada hannu da shugaba Azali, da amfani da cikar alakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu shekaru 50, a matsayin wata dama ta ciyar da dangantakarsu ta gargajiya gaba, da ma inganta tabbatar da nasarorin da aka cimma a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), da bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Comoros bisa manyan tsare-tsare, da kuma kara taka rawar gani wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta Sin da Afirka ta ko wane lokaci a sabon zamani.

A nasa bangaren, shugaba Azali ya bayyana cewa, bisa yanayin da duniya ke ciki na fuskantar sauye-sauye da rikice-rikice, ra’ayin da shugaba Xi Jinping ya gabatar na girmama ikon mulkin kai da rashin tsoma baki cikin harkokin gidan kasa da kasa tare kuma da cimma nasara tare ta hanyar hadin kai, ya kara wa kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, ciki har da kasar Comoros. Ya ce kasarsa na son yin kokari tare da kasar Sin bisa ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam, don karfafa samun dauwamamman ci gaba irin na hakuri da juna, da ba da gudummawa ga inganta hadin kai da ma samun wadata tare a tsakanin Afirka da Sin. (Bilkisu Xin)

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe November 13, 2025 Daga Birnin Sin An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea November 13, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa November 12, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

Wannan shi ne baje koli na farko bayan taron kwamitin kolin JKS da ya amince da shirin raya kasa na shekaru 5-5 karo na 15, wanda ya jaddada kudurin Sin na fadada bude kofarta. Halartar kamfanoni da adadinsu ya kai 4,108, daga manya da matsakaita da kananan kasashe ya tabbatar da cewa, kofar Sin a bude take ga kasa da kasa su shigo, su yi cudanya da hadin gwiwa domin samun ci gaba na bai daya. Karuwar adadin mahalarta tamkar kira ne cewa, duniya ta amince kuma tana goyon bayan manufofi da tsare-tsaren kasar Sin. Haka kuma, goyon baya ne ga kiran kasar Sin na dunkule tattalin arzikin duniya da bunkasa cudanyar bangarori daban-daban domin samun ci gaba tare. Bugu da kari ya nuna cewa, bude kofa hanya ce ta samun habakar tattalin arziki da karin gogewa, da takara mai tsafta cikin ’yanci da samun damarmaki, maimakon kariyar ciniki da yakin haraji da dakile ci gaban wasu domin samun riba. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jakadun Kasashen Waje: Shirin Raya Kasa Na 15 Na Sin Na Dauke Da Kyakkyawan Sako November 11, 2025 Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Babbar Hanyar Mota Da Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa A Namibia November 11, 2025 Daga Birnin Sin An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin  November 10, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Ya Bukaci Matasa Masanan Harkokin Sin Su Kasance Gada Tsakanin Sin Da Duniya
  • Iran da china Za su Yi Bikcin Cika Shekaru 55 Da Huldar Diplomasiya Tsakaninsu
  • An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea
  • Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing
  • An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba
  • Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?
  • Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170
  • ’Yan ta’adda na kafa doka da karɓar haraji a Arewa — Dambazau
  • Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin